Tura Ta Kai Bango: Gwamnoni 6 Sun Kafa Asusun Tsaro, Za Su Yaki 'Yan Ta'adda

Tura Ta Kai Bango: Gwamnoni 6 Sun Kafa Asusun Tsaro, Za Su Yaki 'Yan Ta'adda

  • Gwamnonin Kudu maso Yamma sun ce lokaci ya yi da za a kafa 'yan sanda jihohi saboda tabarbarewar tsaro a yankin
  • Sun amince da kafa Asusun Tsaron Yankin Kudu maso Yamma da kuma dandalin musayar bayanan sirri na zamani
  • Gwamnonin sun nuna damuwa kan karuwar 'yan ta'adda a dazuzzuka da kuma shigar mutane jihohinsu ba bisa ka'ida ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Yayin da matsalolin tsaro ke ƙaruwa a jihohin Kudu maso Yamma, kungiyar gwamnonin yankin sun yi wani zama na musamman a Ibadan, birnin jihar Oyo.

A yayin zaman gwamnonin, sun bayyana cewa lokaci ya yi da za a kafa ’yan sandan jihohi, kuma a gaggauta yin hakan ba tare da jan kafa ba.

Gwamnonin Kudu maso Yamma sun kafa asusun tsaro domin yaki da 'yan ta'adda.
Gwamnonin Kudu maso Gabas suna jawabi jim kadan bayan kammala taronsu. Hoto: @jidesanwoolu
Source: Twitter

Gwamnonin Kudu maso Yamma sun yi zama

Gwamnonin sun yanke wannan hukunci ne a babban taron da suka gudanar a ofishin Gwamna Seyi Makinde a ranar Litinin, in ji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bukaci N150m kudin fansar babban Sarki da suka sace

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wajen taron, an tattauna kan batutuwan tsaro, ci gaban tattalin arziki, aikin gona, da kuma haɗin gwiwa a tabbatar da dorewar martabar al’adu.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas, wanda shi ne shugaban ƙungiyar, ya karanta sanarwar bayan taron.

Gwamnonin da suka halarta sun haɗa da: Dapo Abiodun (Ogun), Biodun Oyebanji (Ekiti), Lucky Aiyedatiwa (Ondo), Babajide Sanwo-Olu (Legas), wakilin gwamnan jihar Osun Prince Kola Adewusi, da kuma mai masaukin baki, Seyi Makinde (Oyo).

Gwamnoni 6 sun kafa asusun tsaro

Gwamnonin sun gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa matakan gaggawa da aka ɗauka a Kebbi, Neja da Kwara sakamakon hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane.

A matakin yankin kuma, sun amince da kafa asusun tsaro na Kudu maso Yamma (SWSF) karkashin hukumar DAWN.

Gwamnonin sun amince cewa za a gudanar da wannan asusun ne ta hannun mashawartan tsaro na jihohin shidda, kuma za su rika ganawa kowane wata.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace mai martaba sarki a jihar Kwara

Gwamnonin sun amince da wani sabon tsarin fasahar rarraba bayanan sirri wanda zai bada damar rarraba bayanai kai tsaye idan an samu barazana, ko wani abu ya faru da kuma yadda za a ɗauki matakin gaggawa tsakanin jihohin yankin.

Gwamonin sun nemi a inganta tsaron dazuzzuka

Sun kuma koka da yadda 'yan ta'adda ke samun mafaka a cikin dazuzzuka, inda suka bukaci gwamnatin tarayya ta ƙara kula da tsaron dazuzzuka da kuma tallafawa aikin dakarun tsaron dazuzzuka.

Kungiyar gwamnonin Kudu maso Yamma sun ce dole ne a kwato dazuzzuka daga hannun ’yan ta’adda da masu aikata laifuffuka, in ji rahoton Channels TV.

Gwamnonin sun nuna damuwa kan yadda mutane ke shiga jihohin yankin ba tare da tsari ba, lamarin da zai iya baiwa miyagu damar ɓuya ko kai hari.

Sannan sun ce hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ta zama barazana ga tsaro da muhalli don haka dole su dauki matakai a kan hakan.

Gwamnoni
Gwamnonin shiyyar Arewa maso Yamma suna gudanar da taro. Hoto: @jidesanwoolu
Source: Twitter

“Lokacin kafa ’yan sandan jihohi ya yi”

Gwamnonin sun jaddada bukatar kafa ’yan sandan Jihohi, inda suka ce: “Lokaci ya yi yanzu, kuma ba za mu ci gaba da jira ba.”

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon gwamna ya riga mu gidan gaskiya a Najeriya, an yi jana'iza

A fannin noma, sun yaba da cigaban da aka samu a yankin da kuma kokarin gwamnatin tarayya wajen tabbatar da wadatar abinci.

Haka kuma sun yaba da kafa hukumar ci gaban Kudu maso Yama, sannan suka nuna gamsuwa da aikin hukumar DAWN wajen haɗa kai da bunkasa tsaro.

Matasan Arewa sun ba gwamnoninsu shawara

Legit Hausa ta tattauna da wasu matasan Arewa da ke fadar albarkacin bakunansu game da halin tsaro a kasar nan, inda suka bukaci gwamnonin Arewa su tashi tsaye kamar na Kudu.

Nura Haruna Mai Karfe ya ce:

"Wannan mataki na gwamnonin Kudu-maso-Yamma na kafa asusun tsaro da kuma tsarin raba bayanan sirri ya cancanci a kwaikwayi shi a Arewa.
"Akwai bukatar gwamnonin Arewa su dauki irin wannan matakin mai tsauri don magance matsalolin tsaron da suka addabi yankin nan. Rufe makarantu kawai ba zai magance matsalar ba."

Shi kuwa Bala Bawaji daga jihar Bauchi ya ce:

"Tabbas, Arewa ce ta fi fama da hare-hare kama daga 'yan ta'adda, masu garkuwa da mutane da 'yan fashi, don haka ana buƙatar matakai na gaggawa kuma masu tsaru.

Kara karanta wannan

"Mun san su": Sanata Maidoki ya ba gwamnati zabi 2 kan kawo karshen 'yan bindiga

"Dakatar da karatun ɗalibai na da muhimmanci a irin wannan lokaci, duk da zai cutar da ilimi, amma hakan ya nuna raunin tsarin tsaron yankin. Muna buƙatar wani tsarin tsaro na musamman da zai hafar da ɗa mai ido..
"Ya kamata gwamnonin su zauna su tsara wani tsarin raba bayanan sirri na zamani a tsakanin jihohi don yaƙar masu laifi. Irin wannan tsarin zai taimaka wajen ganowa da hana hare-hare kafin su faru a Arewacin Najeriya."

Bamai Dabuwa ya ce:

"Abin da gwamnonin Kudu-maso-Yamma suka yi wani abu ne da ya nuna tsantsar himma wajen kare mutanensu.
"Gwamnonin Arewa suna buƙatar tashi tsaye wajen inganta fannin tsaro a yanzu. Kuɗi da fasaha sune manyan abubuwan da za su iya dakile ayyukan ‘yan ta’adda a Arewa."

Shi kuwa Sada Bn Sulaiman cewa ya yi:

"Ya kamata gwamnonin Arewa su haɗa kai su samar da hanyar magance matsalolin tsaro a dukkan jihohin shiyyar.
"Wannan yana buƙatar sadaukarwa ta kuɗi da kuma amfani da sabbin fasahohin zamani wajen tattara bayanai da kuma aiwatar da su."

Matsayar gwamnonin Arewa kan 'yan sandan jihohi

A wani labari, mun ruwaito cewa, kungiyar gwamnonin Arewa ta gudanar da taro kan matsalolin da suka addabi yankin a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Shawarar da Gwamna Nasir ya ba daliban da 'yan bindiga suka saki a Kebbi

Daga abin da gwamnonin guda 19 na jihohin Arewa suka cimmawa har da amincewa da kafa rundunar ƴan sandan jihohi da ake kokarin yi.

Gwamnonin sun kuma yabawa shugaban ƙasa bisa yadda ya jajirce wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi yankin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com