Ana Wata ga Wata: Amurka Ta Yi Magana kan Sace Dalibai a Kebbi da Neja

Ana Wata ga Wata: Amurka Ta Yi Magana kan Sace Dalibai a Kebbi da Neja

  • Ana ci gaba da jimamin sace dalibai da malaman da 'yan bindiga suka yi a jihohin Kebbi da Neja na Arewacin Najeriya
  • Gwamnatin Amurka ta shiga cikin sahun masu yin Allah wadai da hare-haren da 'yan bindiga suka kai a makarantun guda biyu
  • Ta bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta karfafa matakan tsaro tare da kare yankunan da ke fama da barazana

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Amurka - Gwamnatin Amurka ta yi Allah-wadai da sace dalibai da malaman da 'yan bindiga suka yi a jihar Neja.

Gwamnatin Amurka ta kuma yi tir da sace yara mata ’yan makaranta a jihar Kebbi a kwanaki kadan da suka gabata.

Amurka ta yi magana kan hare-hare a Najeriya
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Shugaba Donald Trump Hoto: @DOlusegun, @RealDonaldTrump
Source: Getty Images

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin kasashen Afrika ta Amurka ta fitar a shafinta na X ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Amurka ta sake fusata, ta gabatar da wasu bukatu ga Najeriya bayan sace dalibai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun sace dalibai a Najeriya

A ranar 17 ga Nuwamba, ’yan bindiga sun mamaye GGCSS Maga, inda suka kashe mataimakin shugaban makarantar, Hassan Makuku, sannan suka sace akalla dalibai mata 25.

Sai kuma a ranar 21 ga Nuwamba, wasu ’yan bindiga suka kai hari St. Mary’s Catholic Primary and Secondary School, Papiri, a karamar hukumar Agwara, jihar Neja, inda suka sace dalibai 303 da malamai 12.

Da farko rahotanni sun yi karo da juna, amma daga baya CAN ta tabbatar da adadin bayan tantancewa da kididdigar wadanda suka bace.

Daga baya kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bayyana cewa dalibai 50 kuwa sun tsere, inda suka koma koma gida sannan aka haɗa su da iyalansu.

Me Amurka ta ce kan sace dalibai?

Amurka ta bayyana hare-haren a matsayin laifuffukan da dole a hukunta su, tare da kira ga gwamnatin tarayya ta kamo wadanda suka aikata wa jama’a wannan danyen aiki.

Kara karanta wannan

Neja: Wasu dalibai da aka sace sun yi dabara, sun gudo daga hannun 'yan bindiga

Sanarwar ta kuma bukaci gwamnati ta karfafa matakan tsaro, musamman a yankunan da ke fama da barazana, ciki har da al’ummomin Kirista.

Amurka ta yi Allah wadai da sace dalibai a Neja
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sanarwar na cewa:

“Amurka na Allah-wadai da sace sama da dalibai 300 da malamai daga makarantar St. Mary’s Catholic School a Papiri, kihar Neja, da kuma sace dalibai 25 daga Government Girls Comprehensive Secondary School, Maga, jihar Kebbi, 'yan kwanaki kafin haka."
“Dole a kamo wadanda suka aikata wadannan laifuffuka cikin gaggawa a hukunta su."
"Dole ne gwamnatin Najeriya ta dauki mataki cikin gaggawa kuma ta kara kare Kiristoci da tabbatar da 'yan Najeriya suna rayuwa, karatu da gudanar da addininsu cikin ‘yanci ba tare da tsoro ko tashin hankali ba.”

Trump ya dauki zafi kan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi kakkausar suka kan kashe-kashen da ake yi a Najeriya.

Shugaba Donald Trump ya sake jaddada cewa ana kashe dubban Kiristoci ba gaira babu dalili kuma gwamnatin Najeriya ta gaza daukar matakin da ya dace.

Hakazalika, shugaban kasar na Amurka wanda ya nuna damuwa kan kashe-kashen, ya yi barazanar dakatar da tallafin da kasarsa ke bayarwa ga Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng