'Tinubu ne Ya Tsara Komai': Yadda Aka Ceto Kiristoci 38 da Aka Sace a Kwara

'Tinubu ne Ya Tsara Komai': Yadda Aka Ceto Kiristoci 38 da Aka Sace a Kwara

  • Majiyoyi sun ce Shugaba Bola Tinubu ne da kansa ya tsara yadda DSS, sojoji suka ceto Kiristoci da aka sace a Kwara
  • An tabbatar da cewa jami’an tsaro sun samu cikakkiyar nasarar ceto mutum 38, ciki har da yara kanana ba tare ko rauni ba
  • Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ya gode wa Tinubu, inda ya ce gwamnatinsa za ta kara tallafa wa jami'an tsaro a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda aka samu nasarar ceto dukkan mutane 38 da ’yan bindiga suka sace daga Cocin Christ Apostolic, Eruku, a jihar Kwara.

Bayanai daga manyan jami’an tsaro sun tabbatar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne da kansa ya dauki nauyin jagorantar dukkan tsare-tsaren ceto mutanen.

An ji yadda Tinubu ya jagoranci ceto masu ibada 38 da aka sace a cocin Kwara
Shugaba Bola Tinubu na ganawa da hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa Abuja. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu ya jagoranci ceto Kiristocin da aka sace

Kara karanta wannan

Tinubu ya umarci janye ƴan sanda da ke rakiyar manya, za a dauki dubban jami'ai

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Tinubu ya shirya komai a Abuja, sannan ya ci gaba da karɓar rahotanni dare da rana domin ganin ba a cutar da ko daya daga cikin wadanda aka sace ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin dai ya auku ne a daren Laraba lokacin da 'yan bindigar dauke da manyan bindigogi suka shiga cocin yayin ibada, suka kashe mutane biyu, suka jikkata wasu, sannan suka yi awon gaba da mutum 38

Majiyoyi sun ce tun bayan samun rahoto, Shugaba Tinubu ya shiga tattaunawa kai tsaye da NSA, DSS, sojojin sama da kasa, domin ba da dabaru masu inganci a aikin ceto mutanen.

Wannan matakin nasa ya haifar da tura manyan kwararrun DSS da jami’an rundunar sojojin sama domin gudanar da leken asiri tare da nazarin taswirar dazuzzukan yankin.

Rahotanni sun nuna cewa a yankin Oreke–Okeigbo ne ake zargin ’yan bindigan suka boye wadanda aka sace, lamarin da ya jawo kara tsaurara bincike a wurin.

Kwara: Yadda aka ceto masu ibada 38

A ranar Lahadi, 23 ga Nuwamba, 2025, da misalin 3:20 na rana, aka kai babban samamen da ya kawo karshen aikin ceton, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.

Kara karanta wannan

Neja: Wasu dalibai da aka sace sun yi dabara, sun gudo daga hannun 'yan bindiga

Ba a bayyana ko an yi musayar wuta da ’yan bindigar ba, ko kuwa sun tsere kafin zuwan jami’an tsaro, amma an tabbatar cewa an kubutar da mutanen 38 cikin koshin lafiya.

Cikakkun bayanai sun nuna cewa daga cikin wadanda aka ceto akwai mata 26 da maza 12. Haka nan akwai yara masu shekaru 6, 9 da 10, in ji rahoton TVC.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya godewa Shugaba Tinubu bayan ceto masu ibada 38 da aka sace a Kwara.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq. Hoto: @followKWSG
Source: Twitter

Gwana AbdulRazaq da al’ummar Eruku sun yi godiya

Al’ummar Eruku sun rungumi juna suna kuka da farin ciki bayan jin labarin an ceto 'yan uwansu, inda suka ce sun kwashe kwanaki cikin tsoro da fargaba.

Wani dattijo ya ce jin cewa Shugaba Tinubu ya sa hannu kai tsaye ya basu kwarin guiwa sosai, kuma suka dora yakini kan dawowar 'yan uwansu.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya gode wa shugaban kasa bisa kulawarsa ta musamman, yana mai cewa jihar ta kuduri aniyar kara tallafa wa jami’an tsaro domin ganin yankunan karkara sun samu kariya daga hare-haren da ke faruwa akai-akai.

'Yan bindiga sun sake kai hari Kwara

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai sabon hari kayen Bokungi, karamar hukumar Edu ta jihar Kwara, inda suka sace manoma.

Kara karanta wannan

Ana neman daliban Kebbi, 'yan sanda sun ceto mata 25 da aka yi garkuwa da su

Wannan harin ya biyo bayan na garin Eruku a cikin kasa da awanni 24, inda 'yan bindiga suka kashe masu ibada, suka kuma tafi da akalla 38.

Wani jami'in rundunar ƴan sanda ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa ana kokarin ceto mutanen da aka sace a wasu dazuzzukan Bokungi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com