Matakai 5 da Bola Tinubu Ya Dauka bayan Sace Dalibai a Kebbi da Neja

Matakai 5 da Bola Tinubu Ya Dauka bayan Sace Dalibai a Kebbi da Neja

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dauki wasu matakai masu muhimmanci na niyyar inganta tsaro bayan sace dalibai a jihohin Kebbi da Neja.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A makon da ya wuce wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane suka sace dalibai mata a GGCSS Maga a Kebbi da wasu a makarantar coci a jihar Neja.

Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da sace daliban tare da yin alkawarin ceto su daga hannun 'yan ta'addan.

Bola Tinubu da hafsoshin tsaro
Shugaba Bola Tinubu yayin karbar rahoto game da tsaro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun kawo muku jerin matakan da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dauka bayan faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Tinubu ya fasa tafiya kasashen waje

A ranar 19, Nuwamba, 2025, shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya dage tafiyar da ya shirya yi zuwa Johannesburg a Afirka ta Kudu domin halartar taron shugabannin G20.

Kara karanta wannan

Matawalle ya yi bayani bayan gano wurin da aka boye 'daliban da aka sace a Kebbi

A sakon da Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook, da farko an tsara cewa daga Afrika ta Kudu Tinubu zai cewa zuwa Luanda a Angola domin taron AU-EU kafin soke tafiyar.

Taron G20 da aka yi a Afrika ta Kudu
Wajen taron G20 da Tinubu ya tura Shettima a Afrika ta Kudu. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Fadar shugaban kasa ta ce shugaban ya dage tafiyar ne saboda taka tsantsan da kuma tabbatar da cewa an dauki matakan da suka dace.

2. An tura Shettima jaje jihar Kebbi

Bayan soke tafiyar, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima zuwa jihar Kebbi.

Kashim Shettima ya ziyarci jihar Kebbi domin yi wa jama'ar jihar jaje da kuma gana wa da shugabanni domin tattauna hanyoyin karfafa tsaro.

Kashim Shettima a jihar Kebbi
Shettima yayin ganawa da shugabannin jihar Kebbi. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook cewa shugaban kasar zai saurari rahoton halin da ake ciki domin daukar wasu matakai daga Shettima.

3. Bello Matawalle ya tare a jihar Kebbi

Jaridar Punch ta rahoto cewa shugaban kasa ya umarci karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya tare a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Shugaban DSS ya fadi halin tsaron da kasa ke ciki yayin ganawa da Tinubu

Shugaban kasar ya tura ministan ne domin zama a jihar ya jagoranci shirye-shiryen dakarun Najeriya domin tabbatar da ceto daliban.

Ministan tsaro da gwamnan Kebbi
Ministan tsaro da gwamnan Kebbi bayan isa Birnin Kebbi. Hoto: Dr Bello Matawalle
Source: Facebook

Tuni da Bello Matawalle ya ce sun fara kokarin ceto daliban bayan gano wajen da aka boye matan da aka sace.

4. Tinubu ya tura ministan tsaro Neja

Bayan sace dalibai a wata makaranta a jihar Neja, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura ministan tsaro, Badaru Abubakar jihar.

Karaminin ministan tsaro, Bello Matawalle ne ya bayyana haka yayin wata tattauna wa da BBC Hausa da ya yi.

Ministan tsaro, Badaru Abubakar
Ministan tsaro, Badaru Abubakar yayin ganawa da 'yan jarida. Hoto: Mati Ali
Source: Facebook

Ministan ya ce:

''Shi ma Badaru zai je Neja kamar yadda aka turo ni Kebbi, domin ƙoƙarin gwamnati na kuɓutar da ɗaliban da aka sace.''

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai

5. An janye 'yan sanda ga manyan kasa

A daren Lahadi, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a janye ‘yan sandan da ke ba manyan mutane tsaro a ƙasar nan.

A cewarsa, daga yanzu, rundunar ‘yan sanda za ta tura jami'ai ne domin maida hankali kan aikinsu na asali na kare rayuka da dukiyoyi.

Wannan umarni na shugaban kasa ya fito ne a taron tsaro da ya jagoranta tare da shugabannin rundunar ‘yan sanda, rundunar sojin sama, rundunar sojin ƙasa da shugaban DSS a Abuja.

Shugaban kasa tare da sufeton yan sanda
Shugaba Tinubu yayin zama da jami'an tsaron Najeriya a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A bisa wannan sabon umarni, duk wani babban mutum da yake buƙatar tsaro, zai nemi jami’an hukumar NSCDC.

Ya ce yankuna da dama na Nigeria, musamman ƙauyuka masu nisa, suna fama da ƙarancin ‘yan sanda a ofisoshin su, lamarin da ke kawo cikas wajen kare al’umma yadda ya kamata.

Shugaban DSS ya gana da Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban hukumar DSS na kasa, Tosin Ajayi ya gana da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Bayan fasa zuwa kasashen waje, ADC ta gayawa Tinubu abin da ya kamata ya yi

Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa Tosin Ajayi ya bayyana wa shugaba Bola Tinubu halin da kasa ke ciki ne kan tsaro yayin zaman.

Ana ganin hakan na cikin matakan da shugaban kasar ke dauka na ganin ya mayar da hankali kan ceto daliban da aka sace a jihohin Kebbi da Kwara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng