Gwamnati Ta Bankado yadda Aka yi Aringizon N61bn a Kamfanin NNPCL
- Ofishin Mai Binciken Asusun Gwamnati ya gano badakalar kudi iri 28 da suka shafi kamfanin samar da mai na kasa, NNPCL,
- Daga cikin badakalolin akwai wanda suka N30.1bn, $51.6m, £14.3m da €5.17m da ake zargin ko dai an biya wasu kudi ba dalili ko an kashe babu hujja
- Jimillar kudin da ake zargin NNPCL da rassanta sun yi badakalarsu sun kai kimanin N61.1bn, kamar yadda wani rahoto ya bayyana
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ofishin Mai Binciken Asusun Gwamnati ya bankado gagarumar badaka a cikin harkokin kudin kamfanin mai na kasa (NNPCL).
Binciken ofishin ga gano wadansu badakaloli da hanyar biyan kudin da babu dalili, kashe kudi ba tare da takardun shaida ba, da kuma wuce iyaka a kasafin kudi.

Kara karanta wannan
Hukumar gwamnatin Kano ta toshe kafar zurarewar kudi, an fara tara N750m duk wata

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wani rahoto na shekarar 2022 da ya bayyana ma’amalolin da NNPCL da rassanta suka yi a shekarar 2021.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano badakaloli a kamfanin NNPCL
The Cable ta wallafa cewa rahoton da aka aika ga majalisar dokoki ta nuna cewa raunin tsarin cikin gida, da kwangilolin da aka bayar ba bisa ka'ida ba da wasu dalilai na jawo wa gwamnati asara.
Rahoton ya tunatar da binciken baya da suka zargi kamfanin da karkatar da N2.68tn da $19.77m tsakanin 2017–2021, abin da ke nuna dogon lokaci na rashin gaskiya da rashin bin tsari a NNPCL.

Source: Getty Images
Daya daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali shi ne gano cewa ofishin NNPCL na Landan ya kashe £14,322,426.59 ba tare da takardu ba.
Dokar 2009 dai ta bukaci duk masu kula da kudi su samar da isassun takardu, ciki har da bayanai kan farashi, kwangila, da izinin kashe kudi—amma ba a samu wadannan bayanai ba.
Yadda NNPCL ya kashe kudi
Rahoton ya bayyana cewa NNPCL ya kahse £5.94m wajen biyan albashi da kudin ma’aikata, an kashe £1.43m wajen biyan kudin kwangila sai kuma £6.94m da aka kashe da sunan sauran kudin aiki.
Duk da wannan yawan kudi, masu bincike sun ce ba su ga takarda daya ba da ta tabbatar da yadda aka kashe kudin ba.
Rahoton ya kara gano €5.16m da aka biya dan kwangila ba tare da wata shaida ta aiki ba, $22.84m na biyan DSDP ba tare da dalili ba da $12.44m na sayen janareto a Mosimi
Haka kuma an gani cewa an kashe $1.80m wajen biyan kwangila da aka tsawaita ba bisa ka’ida ba, sai jimillar kudin da aka saba kashe wa da ya kai $51.67m.
Majalisar tarayya ta fara binciken
A baya, kun ji cewa Majalisar wakilan tarayya ta dauki matakin bincikar $18bn da gwamnati ta kashe cikin shekaru 20 wajen gyara matatun mai mallakin gwamnati a sassan kasar nan.
Majalisa ta fara wannan yunkuri ne bayan gabatar da kudiri a zauren majalisa ta hannun Hon. Sesi Oluwaseun Whingan, domin gano ta hanyar da kudin suka zurare.
Whingan ya nuna takaicinsa kan yadda wadannan muhimman matatun – wanda sune ginshikin tsarin makamashi da tattalin arzikin Najeriya – suka zama tamkar kayayyakin tarihi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

