Sojoji Sun Ci Karo da Maɓoyar Ƴan Ta'adda a Laluben Ɗaliban da Aka Sace

Sojoji Sun Ci Karo da Maɓoyar Ƴan Ta'adda a Laluben Ɗaliban da Aka Sace

  • Rundunar Sojan Najeriya ta ce ta kara kaimi wajen aikin nema da ceto daliban da aka sace a jihohin Neja, Kebbi da Zamfara
  • Dakarun ta bayyana cewa a cikin awanni 24, sojoji sun kashe ’yan ta’adda, bayan sun yi kicibis da sansaninsu hanyar neman dalibai
  • Sojojin sun kara da cewa za su ci gaba da aikin har sai an ceto duk daliban da aka sace, tare da ragargaza masu tada karyar bayan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Rundunar Sojan Najeriya ta bayyana cewa dakarun da ke karkashin Operation Fansan Yamma' sun dukufa domin aikin ceto daliban kasar nan da aka sace.

Ta bayyana cewa yanzu haka akwai tarin dakaru da suka bazama domin neman tare da ceto yaran a jihohin Neja, Kebbi da Zamfara.

Kara karanta wannan

Tsohon minista: 'Abin da ya sa 'yan bindiga ke garkuwa da yara 'yan makaranta'

Sojoji sun bazama nemo daliban Kebbi da Neja
H-D: Dakarun sojojin Najeriya, jirgin saman yankin Najeriya na shawagi Hoto: HQ Nigerian Army/Nigerian AirForce HQ
Source: Facebook

Nigerian Tribune ta wallafa cewa a cikin awanni 24 da suka gabata, sojoji sun kashe ’yan ta’adda, sun rushe maboyarsu a yankin Arewa ta Tsakiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun fara fatattakar 'yan ta'adda

Rahoton ya kara da cewa sojojin suna fatattakar 'yan ta'adda a Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma – daga Magaman Daji zuwa gandun dazuzzukan Gando da Sunke.

A Neja, dakarun sun mayar da martani cikin gaggawa bayan sace daliban Makarantar St Mary’s, Papiri a karamar hukumar Agwara.

Sojoji sun shiga dazuka a Neja, Zamfara da Kebbi
Hoton sojojin Najeriya yayin fareti Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

An tura jiragen ISR domin sintiri daga sama, yayin da tawagar kasa ke bin hanyar da ’yan ta’adda suka bi.

Haka kuma an fadada aikin bincike zuwa Audu Fari a karamar hukumar Borgu, inda ake zargin ’yan ta’adda sun bi domin tserewa.

A karamar hukumar Mariga, sojoji daga FOB Gulbin Boka sun yi wa ’yan ta’adda kwanton-bauna yayin da suke kokarin haduwa da wasu abokansu a kusa da Magaman Daji.

Kara karanta wannan

Ana neman daliban Kebbi, 'yan sanda sun ceto mata 25 da aka yi garkuwa da su

Sojoji sun rushe sansanonin 'yan ta'adda

A Kebbi kuwa, dakarun soji sun kara kaimi wajen aikin ceto daliban da aka sace daga GGSS Maga a ranar 17 ga Nuwamba.

An gudanar da babban samame a yankin dajin Gando/Sunke na Kebbi da kuma Talata Mafara a Zamfara.

A cewar wata majiya:

“An rusa sansanonin ’yan ta’adda guda uku, lamarin da ya tilasta masu guduwa suna barin kayan aikinsu.”

Majiyar ta kara da cewa rundunar soji za ta ci gaba da aiki ba kama kafar yaro, har sai an ceto dukkannin daliban da aka sace.

Sojoji suna aikin ceto dalibai

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da cewa sojoji sun fara aiki tukuru domin kwato daliban makarantar sakandaren mata ta Maga cikin koshin lafiya.

Yahaya Sarki, mashawarcin gwamna a kan kafafen yada labarai ya tabbatar da cewa sojojin na samun nasara wajen ceto daliban, tare da ba wa iyayen yara tabbacin dawo masu da yaransu.

Kara karanta wannan

Matawalle ya yi bayani bayan gano wurin da aka boye 'daliban da aka sace a Kebbi

Ya fadi haka ne bayan karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya sauka a jihar Kebbi, tare da bayar da tabbacin cewa aiki ya yi nisa wajen bincike dazukan Neja da Zamfara don gano 'yan matan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng