An Kama 'Dan Bindigan da Ya Gudu Bauchi daga Zamfara da Makamai da Kudi

An Kama 'Dan Bindigan da Ya Gudu Bauchi daga Zamfara da Makamai da Kudi

  • Jami’an DSS sun gudanar da samame a kauyen Bojinji, inda suka kama wani ɗan bindiga tare da kwato makamai da miliyoyin Naira
  • Bincike ya nuna cewa wanda ake zargi ya koma Bauchi daga Jihar Zamfara yana ikirarin tserewa rikici tare da neman mafaka
  • Biyo bayan kama shi, hukumomi sun yi kira ga jama’a su rika kai rahoton mutanen da ba a yarda da halayensu ba, musamman baki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Jami’an hukumar DSS sun samu nasarar kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga a kauyen Bojinji da ke bayan garin Bauchi.

Rahotanni sun nuna cewa an kama dan bindigar ne yayin wani samamen gaggawa da aka gudanar a yankin.

Taswirar jihar Bauchi
Taswirar jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas. Hoto: Legit
Source: Original

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa an kuma gano makamai da alburusai masu yawa tare da makudan kuɗi a hannunsa.

Kara karanta wannan

Ba a gama da jihohin Kebbi da Neja ba, an sace mata a jihar Borno

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ake zargin ya baro Jihar Zamfara ne, yana ikirarin cewa yana gudun hijira, sannan ya zauna cikin al’umma tare da iyalinsa.

Yadda aka gano dan bindiga a Bauchi

Wani jami’in tsaro ya shaida cewa DSS ta dade tana sa ido kan wanda ake zargin, tana bibiyar yadda yake samun kudin da yake kashewa da kuma alakar da yake yi da wasu mutane

A cewar majiyar, an tabbatar da cewa ya kasance mutum ne mai yawan kashe kuɗi ba tare da wata hanya ta halal ta neman kudi da aka san shi da ita ba.

Halayensa da suka jawo hankalin hukuma

Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya shahara da nuna takama, inda yake yin kwanaki yana shan giya a Unguwar Yelwan Angas, tare da sayawa wasu mutane kayan barasa.

Duk da wannan almubazzaranci, ba wanda ya yi masa zargin aikata wani laifi sai bayan shigar jami'an DSS cikin al’amuransa.

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi
Gwamna Bala Mohammed a wani taro da jami'an tsaro. Hoto: Lawan Muazu Bauchi
Source: Facebook

Wannan ya sa jami’an tsaro suka jaddada cewa irin waɗannan halaye na iya zama alamar aikata laifi.

Kiraye-kirayen hukumomi ga jama’a

Jami’an tsaro sun yi kira ga mazauna kauyuka da birane su rika ba hukumomi rahoto kan duk wani mutum da yake rayuwa ta hanyar da ba ta dace ba.

Sun bayyana cewa taka-tsantsan din jama’a yana da matukar muhimmanci wajen dakile miyagun ayyuka da kuma gano hanyoyin da ’yan ta’adda ko ’yan fashi ke bi wajen buya a cikin al’umma.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa bincike yana ci gaba domin gano dabarun da ake zargin ɗan bindigar ke yi, tare da gano ko yana da abokan hulɗa a cikin jihar Bauchi.

Tsohon gwamnan Bauchi, Abu Ali ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan soja na jihar Bauchi, Birgediya Janar Abu Ali (Mai ritaya) ya rasu.

Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ne ya sanar da rasuwar Abu Ali a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Karfin hali: 'Yan bindiga sun nemi kudin fansa har Naira biliyan 3 a Kwara

Tsohon gwamnan ya jagoranci kafa kungiyar kwallon kafa ta jihar Bauchi da wasu muhimman ayyuka a lokacin mulkinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng