Amurka Ta Sake Fusata, Ta Gabatar da Wasu Bukatu ga Najeriya bayan Sace Dalibai

Amurka Ta Sake Fusata, Ta Gabatar da Wasu Bukatu ga Najeriya bayan Sace Dalibai

  • Amurka ta yi kakkausar suka kan garkuwa da ɗalibai a Niger da Kebbi, inda ta bukaci gwamnatin Najeriya ta kama masu laifin
  • Gwamnatin Amurka ta ce dole Najeriya ta inganta tsaro tare da kare Kiristoci daga hare-haren da za su hana su yin ibada
  • An shiga tashin hankali a Arewa bayan sace dalibai fiye da 300 a Niger da 25 a Kebbi, da kuma wasu masu ibada a jihar Kwara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Gwamnatin Amurka ta yi kakkausar suka kan sace ɗaruruwan ɗalibai, malamai, da sauran ma’aikatan makarantu a jihohin Niger da Kebbi.

Amurka ta bayyana wadannan sace-sace da cewa mummunan ta’addanci ne da “bai kamata a barsa haka ba tare da an hukunta masu laifin ba.”

Amurka ta yi martani da aka sace dalibai a makarantun Najeriya
Shugaban Amurka, Donald Trump ya na jawabi a wani taro a Washington DC lokacin yakin neman zabensa. Hoto: @realDonaldTrump
Source: Getty Images

Amurka ta yi tir da sace daliban Najeriya

Kara karanta wannan

Ana tsaka da hare hare, ƴan sanda sun yi karin haske kan zargin hari a cocin Gombe

A cikin wata sanarwa da hukumar BAA ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin, Amurka ta ce dole ne waɗanda suka aikata wannan laifi su fuskanci hukunci cikin gaggawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

“Amurka tana tir da sace ɗalibai sama da 300 da malamai daga makarantar Katolika ta St. Mary da ke Papiri, jihar Niger, da kuma sace ɗalibai 25 a Maga, jihar Kebbi.
“Ya zama wajibi a kama masu laifin nan da gaggawa. Gwamnatin Najeriya ta dauki mataki mai ƙarfi, ta kuma kare al’ummar Kirista da sauran ‘yan ƙasa domin su iya rayuwa da yin ibada cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoro ba.”

Rahoton hare-hare a makarantun Arewa

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a ranar 17 ga Nuwamba, 2025 ‘yan bindiga suka kutsa makarantar GGCSS Maga, jihar Kebbi inda suka kashe mataimakin shugaban makarantar, Hassan Makuku, tare da sace akalla dalibai mata 25.

Bayan kwana huɗu, a ranar 21 ga Nuwamba, 2025 wasu miyagun suka sake kai hari a makarantar St. Mary’s Catholic da ke Papiri a karamar hukumar Agwara, jihar Niger, inda suka yi awon gaba da dalibai 303 da malamai 12.

Kara karanta wannan

"Babu wurin zaman ƴan ta'adda a Kebbi": Gwamnati ta fadi yadda aka kai hari makaranta

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta tabbatar da adadin ne bayan tattara bayanan iyaye da ‘yan uwa kan wadanda ba a samu ganinsu ba bayan harin.

Sai dai daga baya, dalibai 50 sun tsere daga hannun masu garkuwar suka koma gida cikin aminci, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Yayin da gwamnatin Najeriya ta dauki matakai bayan sace dalibai, Amurka ta nemi a kare Kiristoci.
Shugaban Amurka, Donald Trump, da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: @realDonaldTrump, @officialABAT
Source: Getty Images

Matakin da Tinubu ya dauka da martanin Amurka

A matsayin martani, Shugaba Bola Tinubu ya umarci karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, da ya koma Kebbi domin jagorantar aikin ceto daliban da aka sace.

Haka kuma, jihohin Niger, Katsina, Plateau, Bauchi, Kwara da wasu na Arewa sun rufe makarantu domin hana maharan sake samun damar sace dalibai.

Amurka dai ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kara tsaro musamman a yankunan da al’ummomin Kirista da sauran masu rauni ke rayuwa.

A cewar Amurka, dole ne Najeriya ta samar da kariya ga yara 'yan makaranta da malamai domin kaucewa sake afkuwar irin wannan bala’i nan gaba.

Trump na gallazawa wasu Kiristoci a Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu ’yan Iran da suka koma addinin Kiristanci sun ce an tursasa musu komawa gida duk da cewa sun nemi kariya daga Amurka.

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

Rahotanni sun ce akwai rashin daidaito a yadda hukumomin Amurka ke tantance hatsarin da ke fuskantar wadanda suka nemi mafaka daga Iran.

Hakan na zuwa ne yayin da shugaban Amurka ke cewa zai kai hari Najeriya domin kare mabiya addinin Kirista da ya ce ana yi wa kisan kare dangi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com