"Ya Sha gaban Shugabannin Najeriya": Sanatan Kaduna Ya Yi Magana kan Salon Mulkin Tinubu

"Ya Sha gaban Shugabannin Najeriya": Sanatan Kaduna Ya Yi Magana kan Salon Mulkin Tinubu

  • Sanata Sunday Marshall Katung ya bayyana bambancin salon mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da na wadanda suka shude
  • Ya ce tun da fari, salon mulkin Shugaban da yadda ya ke zuba ayyuka a yankin Kuduncin Kaduna da ya ke wakilta ya sanya shi sauya sheka
  • Sanata Katung ya ce ko da bai bar PDP ba, da zai yi aiki dari bisa dari don ganin Tinubu ya sake samun nasara a zaben 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Sanata Sunday Marshall Katung, dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kudancin Kaduna, ya kare matakinsa na komawa jam’iyyar APC daga PDP.

Ya ce ya yanke shawarar ne saboda nuna godiya ga abin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa yankinsa a cikin shekaru biyu na mulkinsa,

Kara karanta wannan

Bayan fasa zuwa kasashen waje, ADC ta gayawa Tinubu abin da ya kamata ya yi

Sanata Katung ya jinjina wa mulkin Tinubu
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Ajuri Ngelale
Source: Facebook

Nigerian Tribune ta ruwaito Sanata Katung ya bayyana haka ne a yayin ganawa da manema labarai da ya yi a karshen mako.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata ya fadi alherin Bola Tinubu

Thisday ta ruwaito cewa ko da bai bar jam’iyyar PDP ba, zai yi aiki dari bisa dari domin ganin Tinubu ya sake cin zabe a 2027.

Ya ce:

“Na yanke shawarar sauya sheka ne domin na nuna godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ko da na ci gaba da zama a PDP, zan yi masa aiki. Babu wani shugaban kasa—mai rai ko wanda ya rasu—da ya taba yi wa mutanena irin abin da ya yi musu.”
Sanata Katung ya ce zai yi aiki don Tinubu ya kara wa'adi na biyu
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sanatan ya jaddada abin da ya kira gagarumin ci gaba da yankinsu ya samu cikin kasa da watanni 18 na mulkin Bola Tinubu.

A kalamansa:

“A wannan 'dan lokacin, ya kafa Jami’ar Tarayya a mazabata, tare da Kwalejin koyon aikin lafiya, da kuma Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya. Wadannan muhimman gina-gine ne da za su dade ana mora."

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an ji abin da ya hana Shugaba Tinubu zuwa Amurka ya gana da Trump

Sanatan Kaduna ya goyi bayan Tinubu

Ya ce bayan shawarwari da dama da ya yi da al’ummarsa, sun gane cewa marawa Bola Tinubu baya shi ne mafi alheri a gare su.

Sanata Katung ya ce a yanzu burinsa ba neman wa’adin biyu ba ne, sai dai a bar masa tarihin ayyuka da al’umma za su tuna.

A kalamansa:

“Na damu matuka kan yadda Kauru da Sanga suka kasance cikin manyan yankuna da aka fi mantawa da su a Najeriya. Babu hanyoyi, tafiyar mintuna 15 na iya zama ta awanni uku. Akwai kauyuka da jami’an gwamnati ba su taba ziyarta ba saboda tsananin wahalar hanyar shiga.”

Ya kara da cewa:

“Lokacin da na ketare wani rafi da dalibai suka rasu a yayin tsallakawa, na tausaya sosai. Mutane ne kamar ni. Shi ya sa ya kamata a ba aikin gine-ginen hanya, asibitoci da wutar lantarki fifiko.”

Sanata Kalu ya ce Tinubu na kokari

A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Jihar Abia, kuma sanata a majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na kokarin magance matsalolin Najeriya.

Kara karanta wannan

PDP ta fara adawa mai zafi, ta ragargaji Tinubu kan sace dalibai a Kebbi

Ya bayyana cewa hare-hare, tashin hankali, garkuwa da mutane da kuma sace-sacen dalibai da ake kara fuskanta a Najeriya na da alaƙa kai tsaye da siyasar zaben 2027 mai zuwa.

A cewar Sanata Kalu, wasu ‘yan siyasa ne ke ɗaukar nauyin ‘yan bindiga domin tada tarzoma da kuma tada hankalin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kafin zaben.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng