Sanata Kalu: "Mun Gano Dalilan da Suka sa Aka Dawo da Satar Dalibai"
- Sanata Orji Kalu ya ce akwai hannun ƴa siyasa a cikin kashe-kashe da sace mutane da ake gani a sassan Najeriya
- Bayanin tsohon gwamnan na zuwa ne bayan ƴan ta'adda sun kai hare-hare tare da sace dalibai a jihohin Kebbi da Neja
- Sanatan ya danganta hare-haren da matsin lamba na zaben 2027 da kuma maganganun Donald Trump a kan Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja– Tsohon gwamnan Jihar Abia kuma sanata, Orji Uzor Kalu, ya bayyana dalilan ƙaruwar ayyukan ƴan ta'adda da sace-sacen dalibai.
Sanata Kalu ya ce yawaitar kashe-kashe da garkuwa da mutane a Najeriya na da alaka ta kai tsaye da siyasa da zaben 2027.

Source: Facebook
Channels TV ta wallafa cewa tsohon gwamnan Abia ya ce wasu ‘yan siyasa na daukar nauyin ‘yan bindiga domin tada tarzoma da tada hankalin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka, Trump ya kara daukar zafi, ya kira Najeriya da kalma mara dadin ji
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Kalu ya magantu kan rashin tsaro
Daily Post ta wallafa cewa Sanata Kalu ya ce abin da ke faruwa yanzu ba sabon abu ba ne, domin irin wannan ya faru lokacin shugabancin Goodluck Jonathan.
Ya akwai ‘yan Najeriya da wasu daga kasashen waje da ke aiki kafaɗa-da-kafaɗa wajen lalata zaman lafiya da tayar da hankulan ƴan Najeriya.
Ya ƙara da cewa:
"Idan lokacin zabe ya kusanto, mutane kan yi amfani da matsin lamba don tada hatsaniya. Kuma wadanda ke goyon bayan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga don su tayar da hankalin gwamnati.”
Sai dai bai fadi sunayen mutanen da yake zargi ba da hannu a tashe-tashen hankulan da suka jawo rufe makarantun wasu jihohi a Arewa ba.
Kalu ya kuma ce duk da haka Tinubu ya nuna cewa yana da dabarar shawo kan matsalar a cikin natsuwa da kwanciyar hankali
Ya ce ana iya ganin ƙoƙarin Tinubu musamman bayan shugaban ya soke dukkanin wasu shirye-shiryensa don mai da hankali kan tsaro.

Kara karanta wannan
"Babu wurin zaman ƴan ta'adda a Kebbi": Gwamnati ta fadi yadda aka kai hari makaranta
Abin da gwamnati ke yi game da tsaro
Tsohon gwamnan Abia, Orji Kalu ya bayyana cewa gwamnati na aiki tukuru domin ceto duk wadanda aka sace, daga ciki har da daliban da aka yi garkuwa da su a kwanakin nan.

Source: Twitter
Sanatan ya danganta karin matsalolin tsaro da kalaman Shugaba Donald Trump na Amurka, wanda ya ce ana kashe Kiristocin Najeriya a salo a ƙare dangi.
Kalu ya bayyana cewa irin wadannan maganganu na iya karawa rikice-rikice zafi, musamman ganin yadda ‘yan siyasa ke tunkarar batun zaben 2027.
Ya ce hukumomin leken asiri sun san wadanda ke daukar nauyin hare-haren, yana mai jaddada cewa kuɗi aka zuba a harkar lalata tsaron Najeriya.
Kalu ya kuma yaba wa matakin Shugaba Tinubu na janye ‘yan sandan da ke gadin manyan mutane, yana mai cewa hakan zai kara karfin jami’an tsaro a fagen aiki.
Ya yi kira ga gwamnatin Amurka, yana mai cewa:
“Muna bukatar mu yi aiki tare da Amurka, domin wannan hadin kan zai taimaka.”

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai
Gwamnati ta rufe makarantu saboda tsaro
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Jihar Bauchi ta bada umarnin a rufe dukkannin makarantu — na firamare, sakandare da na jami’a saboda tsaro.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta jihar ta fitar, ta ce an dauki matakin bayan dogon nazari da tuntubar hukumomin tsaro domin tabbatar da kare dalibai.
Ma’aikatar ta roki iyaye, masu makarantu da sauran jama’a su bayar da hadin kai tare da gaggawar mika bayanan tsaro idan sun lura da abin da ya saɓa hankali.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng