Gwamnatin Bauchi Ta Sanar da Rufe Makarantu saboda Tsoron Ƴan Ta'adda
- Gwamnatin jihar Bauchi ta bi sahun wasu daga cikin jihohin Najeriya da suka bayar da umarnin rufe makarantu
- Lamarin ya biyo bayan tsaurin idon ƴan ta'adda na kai hari makarantu tare da kwashe dalibai da malamsu
- Gwamnatin Bauchi ta ce ta dauki matakin rufe makarantun bayan ganawa da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi – Gwamnatin Bauchi ta sanar da rufe dukkannin makarantun da ke sassan jihar saboda fargabar matsalar tsaro.
Gwamnati ta ce umarnin ya shafi makarantun firamare, sakandare da manyan makarantu masu zaman kansu da na gwamnati.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa sanarwar ta kuma shafi makarantun gwamnatin tarayya da ke aiki a cikin jihar, sakamakon ƙarin fargabar tsaro da ya taso a kwanakin nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Bauchi ta rufe makarantu
Radio Nigeria ta ruwaito sanarwar rufe makarantun ta fito ne daga ofishin yada labarai da hulɗa da jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar.
Kakakin ma'aikatar, Jalaludeen Usman, ya ce an dauki matakin ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a kan lamarin.
A cewar sanarwar, rufe makarantun ya zama dole domin kare ɗalibai, malamai da sauran al’ummomi daga barazanar tsaro da ta karu a yankuna.
Gwamnati ta ce tana fahimtar cewa wannan mataki zai iya jefa iyaye da makarantu cikin ɗan takura, amma ta jaddada cewa tsaron yara shi ne muhimmin abin da muka fi bai wa muhimmanci.
Kiran gwamnatin Bauchi ga iyaye
Gwamnatin ta yi kira ga iyaye, masu kula da yara da kuma masu makarantu da su ba wa hukumomi haɗin kai yayin da ake aiki tukuru wajen dawo da zaman lafiya.
Haka kuma gwamnatin ta nemi jama’a su kasance masu lura, su kuma rika kai rahoton duk wani abu da suke zargin yana da alaka da rashin tsaro.

Source: Original
Ta ce su yi gaggawar samar da jami'an tsaro da ke kusa da su domin ɗaukar matakin gaggaw na kare duk wata barazana.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar Bauchi na aiki kai tsaye tare da hukumomin tsaro domin magance matsalolin da suka taso.
Ta ce za a rika fitar da sababbin bayanai a kan yadda al’amura ke tafiya, yayin da za a buɗe makarantu ne kawai idan an tabbatar da cewa yanayi ya inganta.
Gwamnatin ta bukaci al’umma da su ci gaba da addu’a, da kuma kasancewa cikin shiri, tare da nanata cewa za a dawo makarantu kawai idan al'amura sun daidaita.
An fara kwashe dalibai daga makarantu
A baya, kun ji cewa iyaye sun fara kwashe ’ya’yansu daga makarantar FGGC Bwari da ke Abuja a ranar Asabar, bayan karuwar matsalolin tsaro a yankin.
Iyayen yaran sun hallara a makarantar ne bayan umarnin gwamnatin tarayya na rufe makarantun Unity sama da 40 a faɗin Najeriya biyo bayan satar ɗalibai da aka fara.
Najeriya na fuskantar sabon salo na yawaitar hare-haren ’yan bindiga a kan makarantu, inda aka sace dalibai a Kebbi, Neja da masu bauta a Kwara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


