'Idan ba Za Ka Iya ba Ka Sauka,' PDP Ta Taso Tinubu a gaba bayan Rufe Makarantu

'Idan ba Za Ka Iya ba Ka Sauka,' PDP Ta Taso Tinubu a gaba bayan Rufe Makarantu

  • PDP ta ce rufe makarantu saboda tsaro na iya taimaka wa ’yan ta’adda, domin dama wannan ne burinsu kan Arewacin Najeriya
  • Jam’iyyar ta bukaci a aiwatar da tsarin kare makarantu na kasa, tana mai cewa rufe makarantu ba zai magance matsalar ba
  • PDP ta kuma zargi gwamnati da nuna halin ko in kula, inda ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus idan ba zai iya ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, PDP ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus.

Jam'iyyar ta gabatar da bukatar ne yayin da take magana kan makarantun da gwamnatin tarayya da jihohi suka rufe saboda hare-haren 'yan bindiga.

PDP ta bukaci Tinubu ya yi murabus idan ya san ba zai iya magance matsalolin tsaro ba.
Hoton shugaba Bola Tinubu a lokacin taron Japan. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Kakakin jam’iyyar na kasa, Comrade Ini Ememobong, ya ce rufe makarantu na iya zama daidai da taimaka wa ’yan ta’adda cimma manufarsu ta tsoratar da jama’a da durkusar da ilimi, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Mai Mala Buni: Gwamna ya hango hadari, ya rufe dukkan makarantun kwana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Rufe makarantu ba mafita ba ce” — PDP

PDP ta ce idan gwamnati ta rufe makarantu a duk lokacin da aka samu hari, to hakan yana nuni cewa ’yan bindiga sun fi karfinta, kuma gwamnati ta kasa kare 'yan kasar.

Ememobong ya yi nuni da bukatar gwamnatin tarayya ta dawo da aiwatar da tsarin NPSSVFS, watau tsarin kare makarantu na kasa.

Ya ce wannan tsarin ya dogara ne kan bayanan sirri daga al’umma, hanzarta kai dauki, da dabarun dakile hari tun kafin ya faru.

A cewarsa, a halin da ake ciki, rashin tsaro ya zama babban cikas ga ci gaban ilimi, inda alkaluman UNICEF ke nuna cewa sama da yara miliyan 18 ne ba sa zuwa makaranta, kuma yawancinsu daga Arewa ne.

Ya ce:

“Idan aka ci gaba da rufe makarantu, Arewa za ta kara fadawa cikin duhun jahilci kuma wannan shi ne abin da ’yan ta’adda ke so.”

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

PDP ta soki martanin gwamnati kan sace dalibai

Jam’iyyar PDP ta ce martanin gwamnati kan hare-haren da suka yi kamari a makonni biyun da suka gabata bai nuna tsantseni ko tausayi ba.

Ta ce abin takaici ne cewa Shugaba Bola Tinubu bai ziyarci Kebbi da Neja ba, inda aka sace daruruwan dalibai, sai dai kawai ya tura karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Sanarwar Ememobong ta bayyana cewa gwamnatin APC ta nuna halin ko-in-kula, tana mai cewa:

“Yawan wakilan da aka tura Amurka da G-20 idan aka kwatanta da wanda ake tura wa wuraren da aka yi sace-sacen, ya nuna rashin kulawar gwamnati kan al’amarin.”
PDP ta bukaci Tinubu ya yi murabus bayan rufe makarantu saboda matsalar tsaro
Sabon mai magana da yawun jam'iyyar PDP na kasa, Ini Ememobong. Hoto: @IEmemobong
Source: Twitter

“Idan ba za ka iya ba ka sauka” — PDP ga Tinubu

PDP ta jaddada cewa babban aikin gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyi. Jam’iyyar ta ce idan gwamnati ta gaza, ya kamata ta nemi taimakon kasa da kasa ko ta sauka daga mulki cikin mutunci.

Sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai

“Mun sake tunatar da shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu cewa kare rayuka shi ne ginshikin aikin gwamnati.
"Idan gwamnatinsa ba za ta iya ba, to ta nemi taimako daga kasashen da za su iya, idan hakan ba zai yiwu ba, to shugaban kasa ya yi murabus kawai."

Jam’iyyar ta kammala da cewa rufe makarantu ba zai warware matsalar tsaro ba, kuma gwamnati ta daina daukar matakan da ba sa inganta makomar dalibai.

Sace dalibai: Malami ya bukaci Tinubu ya sauka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, malamin Kiristoci ya fusata game da yawan sace al'umma da ake yi inda ya roki Shugaba Bola Tinubu ya sauka.

Fasto Elijah Ayodele ya soki Tinubu saboda karuwar sace-sace da kashe-kashe inda ya bukaci ya magance matsalolin.

Fitaccen malamin Kiristocin ya ce kashe-kashen da aka danganta bai da alaka Kiristoci kaɗai, ya hada da Musulmi da sauran ‘yan Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com