Neja: Wasu Dalibai da Aka Sace Sun Yi Dabara, Sun Gudo daga Hannun 'Yan Bindiga
- Dalibai 50 da aka sace a makarantar St. Mary’s Papiri a jihar Neja sun samu nasarar kubutowa daga hannun 'yan bindiga
- Kungiyar CAN ta bayyana cewa har yanzu dalibai 236 da wasu ma’aikata 12 da daliban sakandare 14 na hannun ’yan bindiga
- An saki sunayen daliban 50 da suka gudo yayin da jami'an tsaro ke kara kaimi wajen ganin an ceto sauran wadanda aka sace
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - An samu babban cigaba a Neja bayan da yara 50 daga makarantar St. Mary da ke Papiri, suka kubuta daga hannun ’yan bindiga.
Harin, wanda ya faru a daren Juma’a, ya rikita al’ummar karamar hukumar Agwara, inda maharan suka kutsa makarantar, suka yi harbe-harbe.

Source: UGC
Dalibai 50 sun gudo daga hannun 'yan bindiga
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa 'yan bindigar sun harbe wani mai gadi sannan suka yi awon gaba da daruruwan dalibai tare da malamai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton farko ya nuna cewa ma'aikata 12 da dalibai 215 aka sace amma bayan sake duba lamarin da kuma kirga dalibai, aka gano cewa har yanzu akwai wasu 88 da ba a san inda suke ba.
A cikin sabuwar sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi ta hannun hadimin shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) na jihar, Daniel Atori, an tabbatar da cewa dalibai 50 sun tsere daga hannun maharan kuma sun koma gidajensu lafiya.
Sanarwar ta ce:
"Muna sanar da ku cewa a ranar Lahadi, 23 ga Nuwamba, 2025, mun samu rahoto mai faranta rai, cewa dalibai 50 sun kubuto daga hannun 'yan bindiga, kuma sun hadu da iyayensu."
Saura daliai 236 a hannun 'yan bindiga
Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna, wanda shi ne shugaban makarantar, ya bayyana cewa makarantar tana da tsarin kwana da jeka-ka-dawo a makarantar, kuma sashen firamare na da dalibai 430, daga cikinsu 377 'yan makarantar kwana ne, 53 kuma ’yan jeka-ka-dawo ne.
Ya ce har yanzu akwai dalibai 236 a hannun masu garkuwar, sannan akwai yara uku na masu aiki da aka kama, da kuma daliban sakandare 14.
Ma’aikata 12 na makarantar su ma suna tsare. Wannan ya nuna cewa daruruwan mutane – yara kanana, matasa da manya – har yanzu suna cikin hadari a dazuzzukan da ke tsakanin Niger, Kebbi da Sakkwato.

Source: Original
Sunayen dalibai 50 da suka kubuto
Rabaran Yohanna ya roki al'umma da su ci gaba da addu'a domin kubutar sauran dalibai da ma'aikatan da aka sace.
Daliban da aka sace su ne:
1. Samson Bitrus
2. Emmanuel Francis
3. Amos Mathew
4. Timothy Peter
5. Ayuba Victor
6. Bulus Emmanuel
7. Bulus Samaila
8. Caleb Hosea
9. Catherine Emmanuel
10. Christopher Ezekiel
11. Dominic Daniel
12. Dominic Elisha
13. Elisha Harunna
14. Elisha Yakubu
15. Ezekiel Emmanuel
16. Ezekiel Joel
17. Ezekiel Pius
18. Ezra James
19. Friday Joel
20. Gloria Jeremiah
21. Godiya Mathew
22. Iliya Philip
23. Ishaya David
24. Joseph Sunday
25. Julius Paul
26. Justina Adamu
27. Keziah Musa
28. Lawrence James
29. Lawrence Yohanna
30. Marcus Bulus
31. Mariam Joshua
32. Mathew Dauda
33. Micah Luka
34. Michael Jacob
35. Musa Timothy
36. Naomi Bulus
37. Nicodemus Ibrahim
38. Peter Jonathan
39. Pricillia Peter
40. Emmanuel Godwin
41. Samaila Dauda
42. Stephen Anthony
43. Sunday Shedrack
44. Veronica Iliya
45. Victoria Ishaku
46. Vincent Emmanuel
47. Wisdom Fabian
48. Yakubu Saminu
49. Yunusa Musa
50. Yusuf Sunday
Dalibai da malamai 277 ne aka sace a Neja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar CAN ta tattara adadin dalibai da malaman da 'yan bindiga suka sace a makarantar Katolika da ke Neja.
Wannan hari da yan bindiga suka kai makarantar da tsakar dare ya tada hankulan mutane daga sassa daban-daban na kasar nan.
Gwamnati da hukumomin tsaro sun sha alwashin cewa ba za su runtsa ba har sai sun tabbatar da ceto wadanda aka sace cikin koshin lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng



