Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Abin da Tawagarta karkashin Ribadu Ke Yi a Amurka

Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Abin da Tawagarta karkashin Ribadu Ke Yi a Amurka

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta yi karin haske kan abin da ya kai tawagarta karkashin Nuhu Ribadu Amurka yayin da ake kallon kallo a tsakani
  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana cewa tawagar gwamnati a Amurka na kokarin gyara labaran karya da ke zargin wariyar addini
  • Ya ce sun mika hujjoji ga hukumomin Amurka, suna bayani kan tsaro da yadda gwamnati ke kare ‘yan Najeriya ba tare da bambancin addini ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi magana game da dalilin tura tawaga ta musamman kasar Amurka ana tsaka da zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ce tawagar gwamnatin tarayya da ke Amurka, karkashin jagorancin Nuhu Ribadu, na kokarin warware labaran bogi na wariyar addini a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya sanya ranar fara azumi, addu'o'i, ya shawarci Musulmi, Kirista

Gwamnatin Tinubu ta fadi dalilin tura tawagar Ribadu Amurka
Malam Nuhu Ribadu da Shugaba Bola Tinubu a Najeriya. Hoto: Nuhu Riadu, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da ma'aikatar yada labarai da wayar da kan jama'a ta wallafa a X a daren yau Asabar 22 ga watan Nuwambar 2025 wanda Legit Hausa ta ci karo da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da tawagar gwamnati ke tattaunawa a Amurka

A cikin sanarwar, Idris ya bayyana cewa tawagar tana gabatar da hujjoji da bayanai domin tabbatar da babu wata gwamnatin da ke zaluntar addini.

Ministan ya ce sun gana da ministan tsaro na Amurka, ‘yan majalisa da ma’aikatar harkokin waje, suna bayani kan tsaro da kokarin kare kowane dan kasa.

Ya ce wadannan tattaunawa na da muhimmanci domin gyara fahimtar da wasu kungiyoyi suka yada a majalisar dokokin Amurka kan zargin kisan kiyashi.

Abubuwan da tawagar Najeriya ke tattaunawa da Amurka
Nuhu Ribadu da ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth Hoto: @nuhuribadu.
Source: Twitter

Yadda gwamnati ke ganin barazanar Trump

Idris ya bayyana cewa gwamnati na daukar lamarin da muhimmanci, inda Tinubu ya karfafa tsarin tsaro tare da fadada hadin kai a fannin yaki da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Amurka ta fara canza tunani kan shirin kawo farmaki Najeriya bayan ganawa da Ribadu

Ya kara da cewa wannan aiki na Amurka yana tabbatar da jajircewar gwamnati wajen kare martabar Najeriya da tabbatar da cewa kasashen waje na dogara ga sahihan bayanai.

Idris ya ce:

“Manufarmu a bayyane take, muna nuna wa abokan hulɗarmu cikakken yanayin matsalar tsaro, matakan da gwamnati ke dauka, da gaskiyar cewa ‘yan ta’adda sun kashe Kirista da Musulmi baki ɗaya.
"Wadannan labaran kisan kiyashi ba karairayi kadai ba za a ce, suna da matuƙar haɗari.”

Idris ya ce dangantakar Najeriya da Amurka na nan daram, kuma tattaunawa na nuna budaddiyar zuciya da gwamnatin Tinubu ke da shi da gaskiya, hadin kai da nuna karamci.

Ya bukaci ‘yan kasa su kwantar da hankali, yana tabbatar musu cewa gwamnati za ta ci gaba da yaki da rashin tsaro tare da kare martabar Najeriya a duniya.

Trump: Dabarun da gwamnatin Tinubu ke dauka

Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da daukar matakan kauce wa barazanar shugaban Amurka, Donald Trump ta kai hari Najeriya.

Wata kungiya ta yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Malam Nuhu Ribadu bisa yadda suka bullo wa lamarin cikin hikima.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa har yanzu ba a hukunta 'masu' daukar nauyin ta'addanci ba': Minista

Kungiyar ta jaddada manufarta na hada kan yan kasa domin bunkasa zaman lafiya da kare martabar Najeriya a idon duniya duba da halin da ake ciki a yanzu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.