Matawalle Ya Yi Bayani bayan Gano Wurin da Aka Boye Daliban da Aka Sace a Kebbi
- Bello Matawalle ya bayyana cewa an samu ci gaba matuka a kokarin ceto daliban makarantar Maga da 'yan bindiga suka sace a Neja
- Karamin ministan tsaron ya ce an tura dakarun sojoji zuwa iyakoki da hanyoyin da 'yan bindiga ke bi a tsakanin Kebbi, Zamfara da Neja
- Dalibai mata kusan 25 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su, amma daga bisani daya daga ciki ta gudo kuma ta koma gida
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi, Nigeria - Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya tabbatar da cewa an samu ci gaba a kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na ceto daliban da aka sace a Kebbi.
Matawalle ya ce an tura dakarun tsaro zuwa iyakokin Kebbi da Zamfara da wasu wurare masu muhimmanci domin tabbatar da 'yan matan sun dawo gida cikin koshin lafiya.

Source: Original
An gano wurin da daliban Kebbi suke
A rahoton da Premium Times ta wallafa, Bello Matawalle, ya bayyana cewa dakarun tsaro sun gano inda ’yan mata daliban makarantar Maga da aka sace a jihar Kebbi suke.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Litinin ne ’yan bindiga suka sace dalibai 25 daga makarantar sakandiren 'yan mata ta gwamnati da ke garin Maga, a karamar hukumar Danko-Wasagu.
Hukumar makarantar ta tabbatar da cewa daya daga cikin daliban ta tsere daga hannun 'yan bindigar, ta dawo gida, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.
Matawalle ya fadi matakan da ake dauka
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Birnin Kebbi ranar Asabar, Matawalle ya ce an samu ci gaban da ya kai ga matakin karshe tun bayan tura jami’an tsaro domin kubutar da daliban.
“Batun tsaro abu ne mai sosa rai, amma zuwa yanzu bayanan sirri da muke da su sun nuna cewa muna dab da inda yaran suke,” in ji Matawalle.

Kara karanta wannan
Sojoji sun dauki mataki kan dakaru da ake zargi sun janye kafin sace daliban Kebbi
Ya ce an tura jami’an tsaro da dama, tare da kulle mafi yawan hanyoyin da ’yan bindiga kan bi tsakanin jihohin Kebbi, Zamfara, da Neja.
Matawalle ya bukaci al'umma su bai wa jami'an tsaro hadin kai domin ganin an samu nasara a kokarin dawo da 'yan matan gida.
Yadda Tinubu ya tura Matawalle Kebbi
Tun a ranar Alhamis, Shugaba Bola Tinubu ya umurci Matawalle da ya koma Kebbi domin jagoranta da kuma sa ido kan aikin ceto daliban.
Matawalle, wanda tsohon gwamnan Zamfara ne, shi ne ya shugabanci jihar lokacin da ’yan bindiga suka sace dalibai 279 daga makarantar sakandiren mata ta gwamnati da ke Jangebe a 2021.

Source: Facebook
Wani jami'in tsaro na rundunar CJTF ya ce fallasa bayanan sirri a harkar tsaro na daya daga cikin abubuwan da ke kawo koma baya a yaki da ta'addanci.
Da yake hira da Legit Hausa bisa sharadin boye bayanansa, jami'in ya ce bai kamata a rika fitar da irin wadannan bayanai ba.
Ya ce:
"Mai girma minista da shugabanninmu suna kokari, amma sanya siyasa a harkar tsaro ita ke kara lalata abun, bai kamata irin wadannan bayanan su rika fita ba har sai an cimma nasara.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai
"Wani lokacin yadda mutane ke sukar lamarin shi ke tilasta wa shugabannin siyasa magana, har su fadi sirrin da bai kamata ba, muna fatan Allah kawo mana zaman lafiya.'
Gwamnatin Kebbi ta fadi halin da ake ciki
A baya, kun ji labarin cewa gwamnatin jihar Kebbi ta bayar da tabbacin cewa za a ceto ƴan matan da ƴan ta'adda suka sace a garin Maga.
Mai taimaka wa gwamnan Kebbi kan harkokin yada labarai, Yahaya Sarki, ya bayyana cewa jami'an tsaro suna aiki ba dare ba rana domin dawo da matan gida.
Hadimin gwamnan ya ƙara cewa an ɗauki matakan da za su tabbatar da cewa an kuɓuto da yaran daga hannun miyagun mutanen da suka yi garkuwa da su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
