"Ba za a Jima ba": Gwamnatin Kebbi Ta Yi Magana kan Ceto Ƴan Matan Maga
- Gwamnatin jihar Kebbi ta ce za a ceto dukkanin ɗaliban makarantar sakandaren mata ta Maga da aka sace
- Mashawarcin gwamna Nasir Idris Kan yaɗa labarai, Yahaya Sarki ya shaida wa Legit cewa ana ɗaukar matakai
- Tabbacin na zuwa ne kwanaki shida da ƴan ta'adda suka kutsa makarantar Maga tare da kaɗa ɗalibai da dama zuwa daji
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kebbi –Gwamnatin Nasir Idris ta jihar Kebbi ta bayar da tabbacin cewa za a ceto ƴan matan da ƴan ta'adda suka sace a garin Maga da ke ƙaramar hukumar Danko Wasagu.
Wannan tabbaci na zuwa kusan kwanaki shida bayan miyagun mutanen sun kwashe ƴan matan daga makarantarsu.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa ƴan ta'addan sun kashe mutum ɗaya lokacin da suka kai harin, kafin su yi awon gaba da matan da suka kusa kai 25.

Kara karanta wannan
"Babu wurin zaman ƴan ta'adda a Kebbi": Gwamnati ta fadi yadda aka kai hari makaranta
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bi sawun ɓarayin daliban Kebbi
A ganawarsa da Legit, Yahaya Sarki, hadimin gwamna Nasir Idris a kan yaɗa labarai ya bayyana cewa jami'an tsaro suna aiki ba dare ba rana.
Ya ƙara cewa an ɗauki matakan da za su tabbatar da cewa an kuɓuto da yaran daga hannun miyagun mutanen da suka yi garkuwa da su. A kalamansa:
"Gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya – akwai matakai da dama da aka ɗauka wanda ya danganci harkar tsaro."
"Ba komai ne za mu iya fitowa mu bayyana ba, saboda yadda lamarin tsaro yake, kada ya gurgunta irin ayyukan da jami'an tsaro ke yi na ƙoƙarin kubutar da waɗannan ƴan mata na makarantar Sakandaren Maga."
"Mun ga kyakkyawan haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Kebbi karkashin gwamnanmu, Kwamred Nasiru Idris Kauran Gwandu, wanda tun farkon hawan shi mulki yake bada gagarumar kulawa dangane da harkar tsaro. Za a ceto daliban Kebbi

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai
– Gwamnati
Za a ceto ɗaliban Kebbi – Gwamnati
Gwamnatin Kebbi ta ce tana da yakinin za a ceto yaran da aka kwashe daga makarantarsu lafiya.
Ta ce yanzu haka akwai jami'an tsaro da ke aiki tukuru a Kebbi, Zamfara da duk hanyar da aka san cewa ƴan ta'addan na amfani da ita domin ƙwato yaran.

Source: Facebook
Hadimin gwamnan, Yahaya Sarki, ya shaida wa Legit cewa:
"Mun ga yadda sojoji ke kai da komowa, muna da labarin yunƙurin da suka yi na shiga dazuka domin ganin cewa an samu nasarar kubutar da waɗannan mata.Ya bayyana cewa suna da tabbacin aikin da jami'an tsaro ke yi zai haifar da ɗa mai ido, kuma za a dawo da daliban ga iyayensu cikin koshin lafiya.
Ya ce:
"In sha Allah sojoji sun bazama domin ganin cewa an ci nasara."
"Gaskiya, yadda muke ganin abubuwa na tafiya, In Sha Allahu ba da daɗewa ba, waɗannan yaran za a kubutar da su In Sha Allahu."
PDP ta fusata game da sace ɗaliban Kebbi
A wani labarin, mun wallafa cewa jam'iyyar PDP ta soki Shugaba Tinubu kan zamansa a Abuja duk da yawaitar hare-haren da ake yi a jihohin Arewa.
Sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, Ini Ememobong, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar bayan sace daliban Maga da ke jihar Kebbi.
Ememobong ya ce sace dalibai 25 a makarantar Sakandaren Maga da kuma karuwar tashin hankali a Arewa ya nuna Tinubu ya gaza magance matsalar tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
