Sojoji Sun Dauki Mataki kan Dakaru da Ake Zargi Sun Janye kafin Sace Daliban Kebbi

Sojoji Sun Dauki Mataki kan Dakaru da Ake Zargi Sun Janye kafin Sace Daliban Kebbi

  • Ministan tsaro Bello Matawalle ya bayyana matakin da rundunar sojoji ke shirin dauka kan dakaru da ake zargin sun tsere a harin Kebbi
  • Matawalle ya ce sojojin da suka janye kafin sace daliban Maga suna fuskantar tuhuma kuma za su fuskanci hukunci idan aka same su da laifi
  • Gwamna Nasir Idris ya kira janyewar sojoji da abin takaici a Kebbi, yana mai cewa an janye jami’an tsaro mintuna 45 kafin harin ’yan bindiga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi magana game da matakin da za a dauka kan wasu sojoji da ake zargin sun tsere a harin Kebbi.

Matawalle ya bayyana cewa rundunar sojoji ta kama dakarun da ake zargi sun janye daga bakin aiki kafin sace dalibai 25 a makarantar sakandare.

Kara karanta wannan

Matawalle ya yi bayani bayan gano wurin da aka boye 'daliban da aka sace a Kebbi

Matawalle ya ce an kama sojoji a Kebbi
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle tare da sojoji. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Source: Twitter

Alkawarin da Bello Matawalle ya yi a Kebbi

Matawalle ya ce rundunar soji ba ta bayar da umarnin janyewar ba, kuma ana gudanar da bincike sosai kan lamarin, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace yan mata a makaranta da ke Maga, cikin karamar hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi.

Ministan ya isa Birnin Kebbi ne bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu domin jagorantar kokarin ceto daliban da aka sace.

Ya tabbatar da cewa sojojin da suka janye suna tsare, kuma idan an tabbatar sun yi kuskure, kotun soja za ta dauki mataki a kansu.

Gwamnan Kebbi ya zargi dakarun sojoji

Tun da farko, Gwamna Nasir Idris ya nemi kwakkwaran bayani daga rundunar soji kan janyewar jami’an tsaro daga makarantar.

Ya ce an samu bayanan sirri tun da farko, gwamnati ta kira taron tsaro, kuma an tabbatar masa cewa jami’an tsaro za su kasance a makarantar.

Kara karanta wannan

Ta ya haka ta kasance: Gwamnatin Kebbi ta gano matsalar da ta auku kafin sace dalibai

Duk da haka, sojoji sun janye da karfe 3:00 na asuba, kuma da karfe 3:45 ’yan bindiga suka afka, suka dauke dalibai.

Gwamnan ya tabbatar da cewa suna bincike kan wanda ya bayar da umarnin janyewar a lokacin da ake bukatar tsaro sosai.

An kama sojojin da ake zargin sun tsere a harin Kebbi
Tsohon gwamnan Zamfara kuma karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Source: Original

Zargin da ake yi wa sojoji

A cewar wani malamin makarantar da ya tsira, jami’an tsaro sun kwana a makarantar, suka dauki hotuna da dalibai, amma sun tashi kafin wayewar gari, sannan ’yan bindigar suka afka bayan kusan rabin sa’a da barinsu.

Gwamna Idris ya kafa kwamitin bincike karkashin jagorancin Daraktan DSS na Jihar Kebbi domin gano musabbabin kuskuren tsaro da kuma jagorantar kokarin ceto dalibai.

Ya ce gwamnatin tarayya da ta jiha na aiki tare domin ganin an kubutar da daliban cikin gaggawa, cewar Punch.

Gwamnan ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa turo Matawalle da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, zuwa jihar.

Gwamnatin Kebbi ta fadi yadda aka sace dalibai

Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Kebbi ta ce tana aiki kafada da kafada da jami’an tsaro domin tabbatar da ganin an ceto daliban Maga.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ce ana shirin aikin da zai dagula kokarin ceto daliban Kebbi

Mai ba gwamna Nasir Idris shawara ne ya bayar da tabbacin, har ya ce gwamna na cikin takaici matuƙa.

Gwamnatin ta bayyana harin da kuma kwashe ɗaliban a matsayin ƙaddara, la'akari da ƙoƙarin da gwamnati ke yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.