Mutane Sun Ga Abin da ba Su Taba Gani ba bayan Maida Nnamdi Kanu gidan Yarin Sakkwato
- An tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen gidan yarin Sakkwato bayan labari ya bulla cewa an kai shugaban IPOB, Nnamdi Kanu
- Wannan na zuwa ne bayan babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yanke wa jagoran 'yan aware hukuncin daurin rai da rai
- Mazauna Sakkwato sun bayyana cewa sun ga shigowar dakarun sojojin Najeriya da yawa, lamarin da suka ce ba su taba gani ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Mutanen gari sun ga sauyi a matakan tsaro bayan maida shugaban kungiyar 'yan Biafra watau IPOB, Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato.
Rahoto ya nuna cewa an ƙara tsaurara matakan tsaro a gidan gyaran halin aka kai Kanu a jihar Sakkwato bayan babbar kotun tarayya ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Source: Twitter
Tashar Channels ta ruwaito cewa an yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai ne ranar Alhamis a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bayan an same shi da laifuka masu alaƙa da ta'addanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A hukuncin, Mai Shari'a James Omotosho ya umurci a mayar da Kanu zuwa “gidan yari mai talsaro," yana mai cewa Gidan Gyaran Hali na Kuje da ke Abuja ba shi da aminci.
Idan ba ku manta ba gidan yarin Kuje, wanda galibi aka fi tura manyan mutane na fama da matsaloli ciki har da hare-haren fashin magarkama daga 'yan ta'adda.
An maida Nnamdi Kanu Sakkwato
A ranar Juma’a, lauyansa, Alloy Ejimakor, ya shaida wa jaridar Punch cewa an mayar da Kanu gidan yarin Sakkwato.
Ya bayyana matukar damuwa kan wannan mataki saboda a cewarsa hakan ya nesanta jagoran IPOB daga tawagar lauyoyinsa, iyalinsa, da magoya bayansa.
Ejimakor ya yi kira ga ’yan kabilar Igbo da su kwantar da hankalinsu, ka da su yi kokarin aikata abin da ya karya doka.
An jibge jami'an tsaro a gidan yari
Sai dai jami’an gidan gyaran hali na Sokoto sun ƙi tabbatar da zuwansa, amma rahotanni sun nuna an ga dakarun tsaro fiye da kowane lokaci a wajen, tsaro ya yi tsauri fiye da da.
Bincike ya nuna cewa an girke jami’an tsaro dauke da makamai a muhimman wurare a ciki da wajen gidan yari.
Babbar motar dakon sojoji ta shiga harabar gidan gyaran halin, abin da ba kasafai yake faruwa ba.

Source: Twitter
Mutanen Sakkwato sun yi mamaki
Wani mazaunin yankin ya ce:
“Mun ga sojoji sun shigo da manyan motocinsu a yammacin yau, ba mu taba ganin irin wannan tsaro ba.”
Mai magana da yawun Hukumar Gyaran Hali ta Kasa, Jane Osuji, ta tabbatar cewa Kanu yana hannunsu, amma ta ƙi bayyana ainihin wurin da ake tsare da shi saboda “yanayin da lamarin ya kunsa.”
'Yan Majalisa 44 sun roki a saki Kanu
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan Majalisar Wakilai 44 sun fara kokarin lallaba Bola Ahmed Tinubu domin ya saki shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Rahoto ya nuna cewa yan Majalisar sun aika wasika ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, suna rokon ya ba da umarnin sakin Nnamdi Kanu nan take.
Sun kuma shawarci shugaban kasa da ya fara tattaunawar siyasa mai faɗi domin warware matsalolin tsaro da siyasar Kudu maso Gabas.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


