"Babu Wurin Zaman Ƴan Ta'adda a Kebbi": Gwamnati Ta Fadi yadda aka Kai Hari Makaranta
- Gwamnatin Kebbi ta ce tana aiki kafada da kafada da jami’an tsaro domin tabbatar da an ceto daliban Maga
- Mashawarcin gwamna Nasir Idris me ya bayar da tabbacin ga Legit, inda ya ce gwamna na cikin takaici matuƙa
- Gwamnatin ta bayyana harin da kuma kwashe ɗaliban a matsayin ƙaddara, la'akari da ƙoƙarin da gwamnati ke yi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kebbi –Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa ana samun kyakkyawan haɗin kai a tsakaninta da jami'an tsaro da gwamnatin Tarayya domin ceto daliban Maga da ’yan bindiga suka sace.
Mashawarcin Shugaban Kasa na musamman kan yaɗa labaran Kebbi, Yahaya Sarki ne ya tabbatar wa Legit haka a safiyar Asabar.

Source: Facebook
Channels TV ta wallafa cewa a ranar Litinin da ta gabata ne wasu ’yan bindiga suka kutsa makarantar ’yan matan Maga, inda suka sace dalibai kusan 25.
Yadda Kebbi ta tsinci kanta a matsalar tsaro
A kalamansa, Yahaya Sarki ya ce matsalar tsaron Kebbi na faruwa ne saboda shigowar ’yan ta’adda daga Zamfara da sauran jihohi.
Ya ce a duk faɗin jihar Kebbi, babu wani wuri da ’yan ta’adda suka kama ko suke zaune a can.
Yahaya Sarki ya ce:
"Matsalolin da muke samu na tsaro, ya biyo bayan irin yadda su ’yan ta’adda kan kawo hari daga jihohin da ke makwabtaka da mu, kamar su Zamfara da Neja da Sakkwato."
"Sai su shigo su yi ɓarna, su gudu su koma."
Hadimin gwamnan, Yahaya Sarki, ya ƙara da cewa:
"Sannan ina ba ka tabbacin ba mu da wani mazauni na ’yan ta’adda, ba mu da shi a nan jihar Kebbi saboda matakan da Mai girma gwamna ke ɗauka."
"Wannan abu dai ya zo kan ƙaddara duk da matakan da ake ɗauka."
"Kuma gaskiya Mai girma gwamna ya nuna bakin ciki ƙwarai da gaske saboda sakacin da sojoji suka yi, ganin cewa ɗan ƙalilan lokaci da suka bar wurin aikinsu aka samu afkuwar wannan hari a makarantar."

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai
Gwamnatin Kebbi ta yi magana game da tsaro
Yahaya Sarki ya bayyana cewa ta daɗe tana samar wa jami'an tsaro dukkan abubuwan da za su buƙata domin ceto yaran makarantar da aka sace.
Ya ce baya ga wannan, ta buƙaci jama'a su tashi tsaye, kuma a gudanar da addu’a a ƙasa baki ɗaya game da matsalar.

Source: Twitter
A kalamansa:
"Tun lokacin da ya (Nasir Idris) hau kujerar mulki shekara biyu da suka wuce, abu na ɗaya da ya fara ba fifiko shi ne harka ta tsaro."
"Jami'an tsaro sun sani, al’ummar jiha sun sani, irin taimakon da yake ba su, ma motoci. Kuma an ƙara jawo bijilanti a haɗa su da sojoji, ’yan sanda da DSS, su ma an same musu babura."
"Yanzu haka da nake magana, akwai ƙarin motoci da Mai girma gwamna ya saya domin ƙara raba wa jami'an tsaro su ji daɗin gudanar da ayyukansu."
Ya ce Gwamnan na bayar da alawus duk wata domin gyara motocin da sauran ababen hawa domin samun sauƙin aiki.

Kara karanta wannan
Ta ya haka ta kasance: Gwamnatin Kebbi ta gano matsalar da ta auku kafin sace dalibai
Gwamnatin Kebbi ta gode wa dukkanin masu ruwa da tsaki da suka haɗa da gwamnoni da ɗaiɗaikun jama'a da suka jajanta mata game da sace ɗaliban Maga.
Yahaya Sarki ya ce tun bayan faruwar lamarin, ƙungiyar ƙwadago ta NLC da gwamnonin APC suka kai mata ziyarar jaje.
Matawalle ya dura a Kebbi
A baya, mun wallafa cewa Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya sauka a Kebbi bisa umarnin Shugaba Tinubu domin jagorantar ceto ‘yan makarantar Maga da aka sace.
Bayan isarsa, Matawalle ya shiga taron sirri da manyan hafsoshin tsaro — sojoji, ‘yan sanda, DSS — domin tsara dabarun ceto yaran daga hannun ƴan ta'adda.
Gwamna Nasir Idris na Kebbi ya yaba wa matakin, inda ya bayyana goyon bayansa ga duk ayyukan tsaro don ganin an dawo da ‘ya’yan makarantar cikin aminci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
