Sace Dalibai: An Taso Tinubu a gaba, Malami Ya Buƙace Shi don Allah Ya Yi Murabus

Sace Dalibai: An Taso Tinubu a gaba, Malami Ya Buƙace Shi don Allah Ya Yi Murabus

  • Malamin addini a Najeriya ya fusata game da yawan sace al'umma da ake yi inda ya roki Shugaba Bola Tinubu ya sauka
  • Fasto Elijah Ayodele ya soki Tinubu saboda karuwar sace-sace da kashe-kashe inda ya bukaci ya magance matsalolin
  • Malamin ya ce kashe-kashen da aka danganta bai da alaka Kiristoci kaɗai, ya hada da Musulmi da sauran ‘yan Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Babban malamin addini a Najeriya, Fasto Babatunde Elijah Ayodele ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kawo karshen ta'addanci.

Fasto Ayodele ya bukaci shugaban da ya sauka daga mukaminsa, bayan sace dalibai a jihohin Kebbi da Niger da kuma kisan Birgediya Janar Musa Uba a Borno.

Fasto Ayodele ya gargadi Tinubu kan rashin tsaro
Fasto Elijah Ayodele da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Wannan bukata na cikin wani faifan bidiyo da Ayodele ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Juma'a 21 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

Shugaban DSS ya fadi halin tsaron da kasa ke ciki yayin ganawa da Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasto ya bukaci Tinubu ya yi murabus

Ayodele ya ce Tinubu ya yi duk mai yiwuwa wajen kare ‘yan Najeriya kuma ya dinga sauraron shawarwari.

Malamin ya bayyana halin da ake ciki a Najeriya a matsayin abin kunya, musamman ganin cewa wasu jami’an gwamnati sun tafi Amurka domin ganawa kan batun tsaro da barazanar Trump.

Ya ce hakkin shugaban kasa ne ya tabbatar da tsaron kowa, kuma idan Tinubu ya kasa hakan, “ya fi dacewa ya sauka daga kujera ya bari wanda ya fi iya wannan aiki ya karɓa.”

“Abin kunya ne mu kai rahoto Amurka; mu faɗi gaskiya, wannan kisan kiyashin ba addini guda yake shafa ba.
Ba Kiristoci kaɗai ake kashewa ba, Musulmi ma na cikin matsala. Kisan ya zama ruwan dare, kuma abin takaici ne sosai, Tinubu yana da alhakin kare kowane ɗan Najeriya ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, amma abin da muka gani zuwa yanzu bai nuna cewa shugaban zai iya ba.

Kara karanta wannan

Bayan fasa zuwa kasashen waje, ADC ta gayawa Tinubu abin da ya kamata ya yi

"Abin bakin ciki, ’yan kasa suna rasa kwarin gwiwa a kan shugaban nasu, Idan shugaban kasa ya kasa magance matsalar tsaro, ya kamata ya yi murabus, ya ba wanda zai iya yin aikin dama.”
Fasto ya bukaci Tinubu ya yi murabus
Shugaba Bola Tinubu da Fasto Elijah Ayodele. Hoto: Bayo Onanuga, Primate Babatunde Elijah Ayodele.
Source: Facebook

Ayodele ya musanta kisan Kiristoci kadai

Ayodele ya kara da cewa kashe-kashe da ake kira “kisan kiyashi” ba wai ya shafi Kiristoci kaɗai ba ne, Musulmi da sauran jama’a duk suna cikin bala’in.

A cikin sanarwar, Ayodele ya soki mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, yana zarginsa da rashin sauraron gargadi da shawarwarin da za su kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ya ce Ribadu bai yi aikin da ya dace da kujerarsa ba, kuma hakan na janyo wa gwamnatin Tinubu matsala.

Fasto ya ba Tinubu mafita kan Shettima

Kun ji cewa malamin coci, Fasto Elijiah Ayodele ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya jure wa duk wata matsin lamba, ka da ya canza Shettima a 2027.

Ayodele ya yi hasashen cewa nan gaba za a haɗa Tinubu da Shettima faɗa amma ka da hakan ya sa shugaban kasa ya sauya abokin takara.

Kara karanta wannan

Faston da ya fara maganar kisan Kiristoci ya sake bayyana a gaban majalisar Amurka

Malamin ya ce tazarcen shugaba Tinubu zai raba kawunan Arewa, yana mai cewa akwai bukatar Tinubu ya shirya fuskantar yaƙi mai tsanani.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.