Gwamnatin Tarayya, Katsina da Wasu Jihohi da Suka Rufe Makarantu bayan An Shiga Dauke Dalibai

Gwamnatin Tarayya, Katsina da Wasu Jihohi da Suka Rufe Makarantu bayan An Shiga Dauke Dalibai

A makon nan da ake bankwana da shi, matsalar tsaro ta sake farfaɗowa a fadin Najeriya, musamman a makarantun gwamnati inda ’yan bindiga suka koma yin garkuwa da dalibai ba kakkautawa.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Nigeria – A jihar Kebbi, an sace fiye da 'yan mata 200, bayan ƴan bindigan sun harbe mataimakin shugaban makarantar yayin da yake kokarin hana su sace ɗaliban.

Gwamnonin jihohin Arewa sun fara daukar matakan kare rayukan ɗalibai
Gwamnan Katsina Dikko Radda, Caleb Muftwang na jihar Filato, Agbu Kefas na Taraba Hoto: Dr. Umaru Dikko Radda/Caleb Muftwang/Agbu Kefas
Source: Facebook

A jiya Juma’a, Vanguard ta ruwaito cewa a Jihar Neja, wasu ’yan bindiga sun shiga makarantar St. Mary, suka yi awon gaba da dalibai, lamarin da ya rikita al’umma.

Wadannan hare-hare sun sa gwamnatocin jihohi masu fama da matsalar ’yan bindiga suka rufe makarantunsu har sai baba ta gani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wannan rahoto, Legit ta tattaro jihohin da suka dauki matakin rufe makarantun gwamnati saboda tsoron sace dalibai.

Kara karanta wannan

Matawalle ya yi bayani bayan gano wurin da aka boye 'daliban da aka sace a Kebbi

1. Gwamnatin Tarayya

ThisDay ta ruwaito cewa gwamnati ta kasa ta rufe makarantun Unity 41 saboda yawaitar sace dalibai a sassa daban-daban na Najeriya.

Wannan umarni na kunshe a cikin wata takarda da Daraktar Ilimin Sakandare, Hajiya Binta Abdulkadir, ta fitar, inda tace Ministan Ilimi ya amince da rufe makarantar domin kaucewa wata barazanar tsaro.

A cewar takardar:

“Saboda tsananin matsalar tsaro a wasu yankuna na kasar, Ministan Ilimi ya amince da a yi gaggawar rufe wadannan makarantun gwamnatin e. An umarci shugabannin makarantu su bi umarnin nan take.”

Makarantun da aka rufe sun hada da: FGGC Minjibir; FGA Suleja; FTC Ganduje; FGGC Zaria; FTC Kafancha da FGGC Bakori.

Gwamnatin tarayya ta rufe makarantun unity
Dr. Tunji Alausa, Ministan ilimi a Najeriya Hoto: Hon Tunji Alausa
Source: Twitter

Sai kuma FTC Dayi; FGC Daura; FGGC Tambuwal; FSC Sokoto; FTC Wurno; FGC Gusau da FGC Anka.

Haka kuma akwai FGGC Gwandu; FGC Birnin Yauri; FTC Zuru; FGGC Kazaure; FGC Kiyawa da FTC Hadejia.

Sauran sun haɗa da FGGC Bida; FGC New Bussa; FTC Kuta-Shiroro; FGC Ilorin; FGGC Omu-Aran; FTC Gwanara da FGC Ugwolawo.

Kara karanta wannan

"Babu wurin zaman ƴan ta'adda a Kebbi": Gwamnati ta fadi yadda aka kai hari makaranta

Sai kuma FGGC Kabba; FTC Ogugu; FGGC Bwari; FGC Rubochi; FGGC Abaji; FGGC Potiskum da FGC Buni Yadi.

Akwai kuma FTC Gashau; FTC Michika; FGC Ganye; FGC Azare; FTC Misau; FGGC Bajoga; FGC Billiri da FTC Zambuk.

2. Jihar Katsina

Jaridar Punch ta wallafa cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta bada umarnin rufe dukkanin makarantun gwamnati nan take saboda batun tsaro.

Gwamnatin Katsina ta rufe makarantu saboda matsalar tsaro
Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Twitter

Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta bukaci iyaye, malamai da al’umma su yi biyayya domin kare rayukan dalibai.

Gwamnatin ta ce rufe makarantun ya zama dole ne domin kaucewa duk wata barazana ga rayuka.

An ce za a sanar da karin matakai idan an bukata.

3. Jihar Kwara

Channels TV ta ruwaito cewa Gwamnatin Jihar Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi hudu saboda tsananin tashin-tsaro a yankunan Kwara ta Kudu.

Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a wasu kananan hukumomi
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq Hoto: @RealAARahman
Source: Twitter

A wata takarda da NUT reshen jihar ta fitar, shugaban kungiyar, Yusuf Agboola, ya ce an rufe makarantun da ke Isin, Irepodun, Ifelodun da Ekiti.

Kungiyar ta ce tana bin umarnin Ma’aikatar Ilimi bayan gwamnatin jihar ta nuna damuwa kan barazanar tsaro.

Kara karanta wannan

Ta ya haka ta kasance: Gwamnatin Kebbi ta gano matsalar da ta auku kafin sace dalibai

4. Jihar Filato

Daily Post ta ruwaito cewa hukumar ilimin bai ɗaya ta Filato, SUBEB ta bada umarnin rufe duka makarantu na firamare da sakandaren farko a jihar saboda sabuwar matsalar tsaro.

Gwamnatin Filato ta sanar da rufe makarantu
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang Hoto: Caleb Muftwang
Source: Twitter

A cewar sanarwar da kakakin hukumar, Richard Jonah ya fitar, an ji cewa an dauki matakin ne domin kare rayukan dalibai da malamai.

Hukumar ta jaddada cewa ana bukatar matakin gaggawa kuma ta bukaci malamai da iyaye su bayar da hadin kai don kare rayuka.

5. Jihar Taraba

TVC News ta wallafa cewa Gwamnan Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya bada umarni cewa a rufe duk makarantun kwana — na gwamnati da masu zaman kansu.

Kwamishinar Ilimi, Dr. Augustina Godwin ta ce karuwar hare-haren da ake yi a fadin kasa ya jefa daliban makarantun kwana cikin hatsari, musamman bayan sace dalibai a Kebbi da Neja.

Gwamnan jihar Taraba ya yi umarnin a rufe makarantun kwana
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba Hoto: Agbu Kefas
Source: Twitter

Gwamna Kefas ya umarci makarantun sakandaren kwana da su koma makarantar jeka-ka-dawo har sai a sake fitar da sabon umarni.

Kara karanta wannan

CAN: Dalibai da malamai 227 'yan bindiga suka yi awon gaba da su a Jihar Neja

An bukaci shugabannin makarantu su aiwatar da umarnin nan take, domin hakan rigakafi ne na kare rayukan yara

An sace dalibai a jihar Neja

A baya, kun ji cewa wasu ’yan bindiga sun kai farmaki makarantar St. Mary’s da ke Papiri, karamar hukumar Agwara a Jihar Neja, inda suka sace dalibai da ma’aikata.

Wasu majiyoyi sun ce maharan sun zo da babura da yawa, suka kutsa cikin makarantun firamare da sakandare na St. Mary’s, Sannan suka kaɗa zuwa dazuka.

A wata sanarwa da katolika ta fitar a jihar, ta ce ana aiki kafada da kafada da jami’an tsaro, shugabannin al’umma da gwamnatoci domin ganin an ceto daliban lafiya lau.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng