Magana Ta Fito, An Ji Abin da Ya Hana Shugaba Tinubu zuwa Amurka Ya Gana da Trump

Magana Ta Fito, An Ji Abin da Ya Hana Shugaba Tinubu zuwa Amurka Ya Gana da Trump

  • Najeriya na ci gaba da tattaunawar diflomasiyya da Amurka domin warware sabanin da aka samu kan zargin kisan kiristoci
  • Tun bayan barazanar da Trump ya yi na kawo farmaki Najeriya, fadar shugaban kasa ta ce Bola Tinubu zai je ya gana da shugaban Amurka
  • Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ya ce Bola Tinubu zai je Amurka a lokacin da ya dace

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan shirin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na kai ziyara Amurka domin gana wa da Shugaba Donald Trump.

Kara karanta wannan

Bayan fasa zuwa kasashen waje, ADC ta gayawa Tinubu abin da ya kamata ya yi

A baya, fadar shugaban kasa ta sanar da cewa Bola Tinubu zai gana da Trump ne kan zargin da ya yi cewa ana yi wa kiristoci kisan kare dangi da kuma barazanar kawo hari Najeriya.

Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris.
Hoton Ministan Yada Labarai da Wayar da kan Jama'a, Mohammed Idris Hoto: Mohammed Idris
Source: Twitter

Me ya hana Tinubu zuwa Amurka?

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya fadi abin da ya hana Tinubu zuwa Amurka yayin da ya bayyana a shirin Politics Today na tashar Channels a ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Shugaba Tinubu zai kai ziyara Amurka kuma ya gana da Donald Trump ne a lokaci da kuma yanayin da ya dace da hakan.

Mohammed Idris ya ce:

“Mun yi imani cewa zai je (Amurka) idan lokacin ya dace a gare shi. Ba wannan ne karon farko da ya taba zuwa Amurka ba, na kasance tare da shi a Majalisar Ɗinkin Duniya lokacin da ya hau mulki.”

Sabanin Najeriya da kasar Amurka

Tun farko dai an samu sabani ne lokacin da Trump ya ayyana cewa ana “kisan Kiristoci” a Najeriya, sannan daga baya ya yi barazanar kai farmakin soji, idan gwamnati ba ta dakatar da tashin hankalin ba.

Kara karanta wannan

Muhawara ta raba 'yan majalisar Amurka 2 kan zargin kashe Kiristoci a Najeriya

Maganganun Trump sun ja hankalin duniya, sai dai gwamnatin Najeriya ta ƙaryata zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci ta fuskar addini.

Shugaba Tinubu ya ce:

“Najeriya ƙasa ce da kundin tsarin mulkinta ke ba da kariya ga kowane ɗan ƙasa ba tare da bambancin addini ba.”

Tawagar Najeriya na tattaunawa da Amurka

A halin yanzu, gwamnatin Najeriya na tattaunawa da gwamnatin Amurka ta hanyar wata tawaga mai ƙarfi, ciki har da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaron Ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu.

Tawagar na ci gaba da tattaunawa da wakilan Amurka domin warware sabanin da aka samu da kuma yayyafa wa wutar zarge-zargen kisan kiristoci ruwan sanyi.

Ministan yada labarai, Idris ya kara cewa duk da cewa Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro, gwamnatin tarayya na yin aiki tuƙuru domin magance su.

Shugaba Tinubu da Donald Trump.
Hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da na Shugaba Donald Trump Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ribadu ya gana da ministan tsaron Amurka

A wani labarin, kun ji cewa Nuhu Ribadu ya gana da Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, da Shugaban Hafsoshin Tsaron Amurka, Janar Dan Caine.

Hakan na cikin tattaunawar da mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, ke yi da shugabannin tsaron Amurka kan barazanar kawo farmaki Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fasa tafiya zuwa kasashen waje bayan abubuwa sun rikice a Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta maida hankali kan barazanar Shugaba Donald Trump cewa zai tura sojojin Amurka zuwa Najeriya domin yakar abin da ya kira cin zarafin Kiristoci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262