Bulama Bukarti Ya Fadi Hanyoyi 5 da Tinubu Zai Bi Ya Kawo Karshen Rashin Tsaro
- Audu Bulama Bukarti ya yi gargadi cewa harin da ake kai wa makarantu da coci na faruwa ne saboda karancin daukar matakan gaggawa
- Ya danganta matsalar da ƙarancin jami’ai, jinkirin kai dauki, da sauransu duk da ana samun bayanan sirri kafin hare-hare a kasar nan
- Bukarti ya lissafo shawarwari biyar da ya ce gwamnatin Tinubu za ta iya bi domin tsayar da rikicin tsaron da ya daɗe yana addabar Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Masanin tsaro kuma lauya, Audu Bulama Bukarti, ya yi magana kan hare-haren da ake kaiwa a sassa daban-daban na Najeriya.
Ya bayyana cewa har yanzu hare-haren na faruwa ne saboda rashin tsari da kin saurin martani daga jami’an tsaro duk da cewa akan samu bayanai kafin a kai hari.

Source: Facebook
Ya bayyana haka ne a tattaunawa kai tsaye daga London a shirin Channels Television, inda ya lissafa hanyoyi biyar da za a iya magance rikicin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masanin ya ce harin da aka kai wa coci a jihar Kwara da kuma sace dalibai a Manga, Kebbi, na nuna cewa har yanzu matsalar tsaro babba ce.
Daliln karuwar rashin tsaro a Najeriya
Bukarti ya ce matsalar tsaro na karuwa ne ba saboda rashin samun bayanan sirri ba, sai dai rashin iya amfani da bayanan da gaggawa.
Ya ce jami'an tsaro sun yi kadan, ba su da motoci ko kayan aiki wadatattu, kuma ana samun jinkiri wajen kawo dauki.
Bulama ya ce hakan yana bai wa ‘yan ta’adda damar yin kutse wajen kai hari su tsere ba tare da samun damar kama su ba.
A hirarsa da tashar BBC, masanin ya nuna irin kalubalen da jami'an Najeriya ke fuskanta tun daga iyakokin kasar da suke a wangale.
Hanyoyi 5 na magance rashin tsaro
A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, Audu Bulama Bukarti ya jero matakai biyar da ya ce za su iya kawo karshen matsalar rashin tsaro a Najeriya.
1. Ya shawarci gwamnatin tarayya ta mayar da dukkan hafsoshin tsaro jihohi masu hadari har sai an ga canji. Ya ce bai kamata su kasance a Abuja ba muddin ana kai hare-hare.
2. Bukarti ya ce a kafa kwamiti ƙarƙashin mataimakin shugaban kasa ko sakataren gwamnatin tarayya domin rika ba ‘yan ƙasa bayani a kai a kai game da matakan tsaro da cigaban da ake samu.
3. Bisa bayaninsa, ya ce dole ne a haɗa gwamnoni, hafsoshin tsaro da sarakunan gargajiya domin aiwatar da manufofin tsaro cikin tsari guda.
4. Ya ce ya zama dole gwamnati ta ayyana dokar ta baci a iyakokin Najeriya domin dakatar da shigowar makamai da miyagun kwayoyi da ke ƙara ingiza ta’addanci.
5. A karshe Bulama ya ce ya kamata a tura dukkan manyan dakaru yankunan da ake fama da rikice-rikice, kada a bar ko daya a bariki.

Source: Facebook
Abba ya ba sojoji motoci a Kano
A wan labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Kano ta fara daukar matakan inganta tsaro, musamman a yankuna masu fama da barazana.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ba dakarun da ke aiki karkashin rundunar hadin gwiwa ta JTF motoci 10 da babura 50.
Rahotanni sun bayyana cewa za a yi amfani da abubuwan hawan ne a yankunan da suka fara fuskantar barazanar 'yan bindiga a Kano.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


