Bayan Dikko Radda, Wani Gwamna Ya ba da Umarni a Rufe Dukkan Makarantu a Jiharsa
- Gwamnatin Filato ta ba da umarnin a rufe dukkan makarantu saboda barazanar tsaro bayan hare-hare a Kebbi da Neja
- Rufe makarantun Filato ya zo bayan Katsina ma ta rufe makarantun gwamnati domin kare dalibai daga duk barazanar tsaro
- Gwamnatin Caleb Mutfwang ta bayyana cewa za a rufe makarantun firamare da sakandare daga 24 ga Nuwamba, 2025
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Filato (PSUBEB) ta bada umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare a fadin jihar.
A cikin sanarwar da PSUBEB ta fitar a Jos, hukumar ta ce za a rufe dukkanin kananun makarantun gwamnati na GJMSSs daga ranar 22 ga Nuwamba, 2025.

Source: Facebook
An rufe dukkan makarantu a jihar Filato
Sannan, sanarwar ta bayyana cewa, za a rufe makarantun firamare da sakandaren jihar ne daga ranar Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025, in ji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin jihar Filato ta ce ta dauki matakin rufe makarantu ne a matsayin rigakafi domin kare rayukan ɗalibai daga duk wata yiwuwar barazanar tsaro.
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan mataki ya biyo bayan hare-haren da aka kai wa makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda aka yi garkuwa da dalibai da dama.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, wacce jami’in hulɗa da jama’a, Rechard John Samanja, ya tabbatar, an bayyana cewa rufe makarantun na ɗan lokaci ne.
Abin da gwamnatin Filato ta fadawa dalibai
Sanarwar ta ce:
“Gwamnatin jihar Filato, ta hannun hukumar PSUBEB, ta bada umarnin rufe dukkan makarantu a jihar nan take.
"Za a rufe makarantun GJMSSs daga ranar Asabar, 22 ga Nuwamba, 2025, yayin da za a rufe makarantun firamare da na sakandaren jeka-ka-dawo daga Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025.
"Hukumar na tabbatar wa iyaye, malamai da daukacin al’umma cewa matakin rufe makarantun na ɗan lokaci ne, domin dakile duk wata barazana ga tsaron ɗalibai.”
Hukumar ta kuma bukaci kananan hukumomi, shugabannin makarantu da shugabannin al’umma su bi umarnin rufe makarantun tare da sanya idanu kan harkokin tsaro.

Source: Original
Katsina ma ta rufe dukkan makarantun gwamnati
A daidai wannan lokaci, gwamnatin jihar Katsina ta bada umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati, sakamakon karuwar barazanar tsaro da kai hare-hare a wasu yankuna na jihar.
Kwamishinan ilimi, Yusuf Sulaiman Jibia, ya tabbatar da hakan a Juma’ar nan yayin ganawa da manema labarai a Katsina, kamar yadda muka ruwaito.
Ya ce matakin ya zama dole saboda tsaron rayukan ɗalibai da malamai ya fi komai muhimmanci, duk da cewa dalibai na ci gaba da rubuta jarabawa.
Rahoton The Nation ya nuna cewa wannan mataki ya biyo bayan sace daliban sakandare a jihohin Kebbi da Neja, lamarin da ya tayar da hankalin iyaye da hukumomi a jihohin Arewa maso Yamma.
Gwamna ya rufe makarantu a jihar Kwara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, matsalar tsaro a yankunan Kwara ta Kudu ya sa gwamnatin jihar ta rufe makarantu a kananan hukumomi hudu.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ba da umarnin a rufe dukkanin makarantu a kananan hukumomin Isin, Irepodun, Ifelodun da Ekiti.
Rufe makarantun ya biyo bayan mummunan harin da ya 'yan bindiga suka kai kauyen Eruku da ke cikin karamar hukumar Ekiti LGA a jihar ta Kwara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


