Gwamnatin Tinubu Ta Bada Umarnin Rufe Makarantu 47 a fadin Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta ba da umarnin kulle makarantu 47 yayin da sha'anin tsaro ke kara tabarbarewa a wasu sassan Najeriya
- Wannan mataki ne kunshe ne a wata sanarwa da ma'aikatar ilimi ta tarayya ta fitar yau Juma'a, 21 ga watan Nuwamba, 2025
- A cikin wannan makon ne 'yan bindiga suka kai farmaki makarantu biyu a jihohin Neja da Kebbi, inda suka yi garkuwa da dalibai da malamai
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya na ci gaba da daukar matakan kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya yayin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a kasa.
Wannan na zuwa ne bayan wasu jerin hare-hare da 'yan bindiga suka kai kan dalibai da masu ibada a jihohin Kwara, Neja da kuma Kebbi.

Source: Facebook
Gwamnatin Tarayya ta rufe makarantu 47
The Cable ta rahoto cewa a kokarin kare rayukan dalibai, Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin rufe makarantu 47 daga cikin wadanda ke karkashinta na ƙasar nan cikin gaggawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin na zuwa ne biyo bayan abin da ke faruwa a wasu sassan ƙasar da kuma bukatar tabbatar da cewa ba a samu wata matsalar tsaro da za ta iya jefa rayuwar ɗalibai cikin hadari ba.
A cewar wata takardar sanarwa da ma'aikatar ilimi ta fitar a ranar Juma’a, 21 ga watan Nuwamba, 2025, Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya ba da umarnin rufe makarantun.
Sanarwar na dauke da sa hannun Binta Abdulkadir, Daraktar Sashen Makarantu na Sakandare na tarayya a madadin ministan.
Sunayen makarantun da aka rufe
Ta umurci dukkan shugabannin makarantu da abin ya shafa da su bi umarnin nan take ba tare da wani jinkiri ba, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Makarantun da gwamnatin ta umarci a rufe su nan take sun hada da:
1. FGGC Minjibir
2. FTC Ganduje
3. FGGC Zaria
4. FTC Kafanchan
5. FGGC Bakori
6. FTC Dayi
7. FGC Daura

Kara karanta wannan
Mutane sun ga abin da ba su taba gani ba bayan maida Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato
8. FGGC Tambuwal
9. FSC Sakkwato
10. FTC Wurno
11. FGC Gusau
12. FGC Anka
13. FGGC Gwandu
14. FGC Birnin Yauri
15. FTC Zuru
16. FGGC Kazaure
17. FGC Kiyawa
18. FTC Hadeja
19. FGGC Bida
20. FGC New Bussa
21. FTC Kuta–Shiroro
22. FGA Suleja
23. FGC Ilorin
24. FGGC Omu-Aran
25. FTC Gwanara
26. FGC Ugwolawo
27. FGGC Kabba
28. FTC Ogugu
29. FGGC Bwari
30. FGC Rubochi
31. FGC Abaji
32. FGGC Kazaure
33. FGC Kiyawa
34. FTC Hadejia
35. FGGC Potiskum
36. FGC Buni Yadi
37. FTC Gashua
38. FTC Michika
39. FGC Ganye
40. FGC Azare
41. FTC Misau
42. FGGC Bajoga
43. FGC Billiri
44. FTC Zambuk
45. FTC Ikare-Akoko
46. FTC Ijebu-Imusin
47. FTC Ushi-Ekiti.

Source: Twitter
An rufe makarantun gwamnati a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Dikko Umaru Radda ta umarci a rufe dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati da ke fadin jihar Katsina.

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka, Trump ya kara daukar zafi, ya kira Najeriya da kalma mara dadin ji
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da ma'aikatar kula da harkokin ilimin firamare da sakandire ta jihar Katsina ta fitar ranar Juma'a.
Ma’aikatar ta ja hankalin iyaye, malamai da al’umma gaba ɗaya da su bi wannan umarnin nan take, yayin da ake ci gaba da bibiyar yanayin tsaron jihar baki ɗaya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
