Matawalle Ya Dura Kebbi, Ya Dauki Matakin Farko Na Ceto Dalibai 25 da Aka Sace
- Ministan tsaro Bello Matawalle ya isa Kebbi bisa umarnin Bola Tinubu domin aikin ceto daliban makarantar Maga da aka sace
- An rahoto cewa Matawalle ya shiga taron sirri da manyan hafsoshin tsaro domin daukar tsauraran matakai na ceto yaran
- Gwamna Nasir Idris ya yaba da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka, yayin da iyaye ke cigaba da addu’o’in kubutar yaransu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kebbi — A ranar Juma'ar nan ne karamin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya isa Birnin Kebbi bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu.
Legit Hausa ta rahoto cewa Shugaba Tinubu ya ba Matawalle umarnin gaggawa na komawa Kebbi domin jagorantar ceto daliban GGCSS Maga da aka sace.

Source: Twitter
Matawalle ya shiga ganawa da hafsoshin tsaro
Bayan saukarsa, Ministan bai yi wata-wata ba, ya shiga taron sirri da manyan hafsoshin tsaro, da suka shafi sojoji, ’yan sanda, DSS da sauransu, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar jami’an tsaro da suka san abin da aka tattauna, taron ya mayar da hankali kan inganta dabarun aiki, sabunta bayanan leƙen asiri, da cike gibin tsaro da aka gano bayan harin.
Wani babban jami’in tsaro ya bayyana cewa isar ministan wata babbar alama ce da ke nuna cewa aikin ceto 'yan makarantar ya shiga sabon mataki.
Jami'in da ya nemi a sakaya sunan sa ya ce:
“Umarni da aka bayar daga Abuja daya ne — a dawo da daliban cikin koshin lafiya. An gudanar da wannan taron don haɗa kai, kawar da duk wani kalubale da tabbatar da ingantaccen shiri.”
Gwamnatin Kebbi ta yi godiya ga Tinubu
A halin yanzu ana ci gaba da tura karin dakaru, tare da jiragen leken asiri da jami'an sintirin ƙasa a kan manyan hanyoyin da suka hada Kebbi da Zamfara da Neja.
Tuni dai Gwamna Nasir Idris ya fitar da sanarwa ta bakin mai magana da yawunsa, inda ya jinjinawa Shugaba Tinubu bisa daukin gaggawar da ya kai Kebbi.
A cikin sanarwar, gwamnan ya ce jihar za ta ba da duk wata gudunmawa da ake bukata don ganin an ceto daliban makarantar da aka sace.
“Abin da ya faru a Maga abin bakin ciki ne. Muna godiya ga gwamnatin tarayya. Za mu bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata domin ganin an dawo da ’ya’yanmu lafiya.”
- Gwamna Nasir Idris.

Source: Twitter
Wanne umarni Tinubu ya ba Matawalle?
Bayan samun rahoton faruwar wannan mummunan lamari, The Nation ta rahoto cewa Shugaba Tinubu ya umurci karamin ministan tsaro ya koma Kebbi nan take domin:
- Haɗa rundunonin tsaro a suka hada da sojoji, 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro,
- Inganta dabarun ceto yaran,
- Tabbatar da komai na gudana cikin tsari.
A kauyen Maga, iyaye da dattawa sun ci gaba da gudanar da tarukan addu’o'i, inda suke rokon Allah ya dawo masu da 'ya'yan cikin aminci.
Matawalle ya yi martani kan harin Kebbi
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Dr. Bello Matawalle, ya fito ya yi magana kan harin da 'yan bindiga suka kai a Kebbi, inda suka sace dalibai mata.
Matawalle ya yi Allah wadai da harin da 'yan bindigan suka kai wanda ya jawo hallaka mataimakin shugaban makarantar da ke Danko/Wasagu.
Karamin ministan ya bayyana umarnin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba hukumomin tsaro kan sace daliban mata da 'yan bindigan suka yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


