Birnin Shehu Ya Yi Baƙo, DSS Ta Maida Nnamdi Kanu Sokoto, Zai Zagaye Najeriya

Birnin Shehu Ya Yi Baƙo, DSS Ta Maida Nnamdi Kanu Sokoto, Zai Zagaye Najeriya

  • Hukumar DSS ta tura Nnamdi Kanu zuwa gidan gyaran hali na Sokoto bayan kotun tarayya ta Abuja ta yanke masa hukuncin laifin ta’addanci
  • Lauyansa Aloy Ejimakor ya tabbatar da matakin, yana cewa tura shi Sokoto ya nisanta shi da lauyoyinsa, iyalansa da kuma masoyansa
  • Alkalin kotun ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai yayin da lauyar gwamnati ta nemi hukuncin kisa da katse na’urorin kafafen sadarwarsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ta dauke shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB daga birnin Abuja.

Hukumar DSS ta mayar da Mazi Nnamdi Kanu, zuwa gidan gyaran hali da ke jihar Sokoto a Arewacin Najeriya.

An dauke Kanu daga Abuja zuwa gidan yarin Sokoto
Mazi Nnamdi Kanu yayin zama a kotu. Hoto: Getty Images.
Source: Twitter

Hukuncin da aka yankewa Nnamdi Kanu

Wannan na zuwa ne bayan kotun tarayya a Abuja ta yanke masa hukunci bayan samunsa da laifin ta’addanci, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Daurin rai da rai': Cikakken hukuncin da kotu ta yanke wa Kanu, shugaban IPOB

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin kotun ya yanke hukuncin ga jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu, hukunci kan laifin ta'addanci wanda ya jawo magana.

Kotun da ke zama a birnin Abuja ya yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai bayan sukar alkalin kotun da rashin sanin doka da kuma son rai.

Rokon lauyan gwamnati game da Nnamdi Kanu

Lauyan gwamnati, Adegboyega Awomolo, ya nemi kotu ta zartar da hukuncin kisa kan wasu tuhume-tuhumen da doka ta ware hukuncin dole.

Ya kuma roƙi kotun ta goge ko katse duk na’urorin Kanu na kafafen sadarwa da asusun intanet din da yake amfani da su.

Haka kuma ya nemi kotu ta umurci a tsare Kanu a wurin da ya fi tsaro domin kare shi daga abokan gaba ko makiya da kan iya kai hari.

An tura Nnamdi Kanu zuwa gidan yarin Sokoto
Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a cikin kotu. Hoto: Favour Michael Kanu.
Source: Facebook

Musabbabin dauke Nnamdi Kanu zuwa Sokoto

Kotun ta yi hukunci ne tare da bayyana cewa ana iya tura shi kowane gidan yari a kasar domin nesanta shi da yan uwansa da kuma sanin fadin kasar.

Kara karanta wannan

‘A duba tsufansa’: 'Dan majalisa ya roki alkali ya sassauta hukuncin Nnamdi Kanu

A ranar Juma’a, lauyansa Aloy Ejimakor, ya tabbatar da cewa an ɗauke Kanu daga Abuja zuwa Sokoto, lamarin da ya jawo da ce-ce-ku-ce, cewar Vanguard.

Ya ce nisan wurin zai hana Kanu damar samun ganawar lauyoyi, iyalai da masoyansa, kuma hakan ya haifar da damuwa ga mutanen yankinsa.

Wata majiya daga hukumomi ta tabbatar da sauya wurin, tana cewa abin da za ta iya faɗa a halin yanzu.

Kotun ya amince da ikirarin DSS cewa Kanu ya yi amfani da ta’addanci wajen neman balle yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.

'Dan majalisa ya rokawa Nnamdi Kanu alfarma

Kun ji cewa dan majalisar tarayya ya roki alkalin kotun tarayya alfarma wajen yanke hukunci kan shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Hon. Obi Aguocha ya roƙi a tausaya wa Nnamdi Kanu a kotun tarayya mai zama a Abuja, bayan an same shi da laifin ta’addanci.

Ya bayyana kansa a matsayin wakilin Kanu, yana roƙon alkali ya tausaya masa, tare da gode wa kotu kan damar da ta ba shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.