Sace Dalibai: Atiku da Kwankwaso Sun Fadawa Tinubu Matakan da Ya Kamata Ya Dauka
- Atiku Abubakar ya yi tsokaci kan sace daliban Neja da 'yan bindiga suka yi, inda ya bukaci gwamnati ta ayyana dokar ta-ɓaci
- Shi ma Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi tir da harin, tare da yin gargadi cewa hare-hare kan makarantu za su gurgunta ci gaban kasa
- Sace dalibai a Neja da Kebbi a kwanakin nan ya jefa tsoro a cikin al'ummar Arewa, inda aka fara rufe makarantu a wasu jihohi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi tir da sace wasu dalibai da malamai na makarantar Katolika ta St. Mary da ke jihar Neja.
Atiku ya bayyana harin a matsayin abu “mai matuƙar raɗaɗi”, inda yake tambayar adadin rayukan ake jira su salwanta kafin gwamnati ta ɗauki cikakken mataki kan matsalar tsaro.

Source: Facebook
Atiku ya bukaci Tinubu ya ayyana dokar ta-baci
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a, Atiku ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro domin magance barazanar da ta yi wa ƙasar katutu shekaru da dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan takarar shugaban kasar ya ce tsaro a makarantu ba abin wasa ba ne, domin hare-haren baya-bayan nan sun sake nuna raunin da ake fama da shi a Arewa.
Sanarwar Atiku ta ce:
"Lallai wannan abin takaici ne matuka. Rayuka nawa ne za su salwanta kafin a dauki kwakkwaran mataki?
"Lokaci bai kurewa gwamnati na ayyana dokar ta baci kan matsalar tsaro ba, ta kuma tunkari wannan barazana da dukkan karfinta."
Kwankwaso: “A gaggauta kubutar da yaran”
Tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar NNPP a zaben shugaban kasa na 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shi ma ya yi tsokaci kan faruwar lamarin.
Ya bayyana sace daliban Papiri a matsayin sabon al’amari cikin jerin hare-haren da suka dade suna addabar Arewa, musamman yankunan karkara.
Kwankwaso ya ce sace dalibai ya zama abin damuwa sosai, yana mai kira da a dauki matakin gaggawa domin kubutar da yaran cikin aminci.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Kwankwaso ya ce:
"Ba iya ceto daliban ba, dole ne kasar nan ta ba tsaron makarantu mafi kololuwar fifiko, domin makarantun ne dabdalar cigaban al'umma, kuma idan suka kasance cikin hatsari, makomar kasa na cikin hadari."

Source: Original
Takaitaccen bayani kan sace daliban Neja
Rahotan jaridar Punch ya nuna cewa maharan sun kutsa makarantar ne da tsakar dare, inda suka yi awon gaba da dalibai da ma’aikata zuwa wani wurin da ba a sani ba.
Jami’an cocin Katolika da ke jihar sun tabbatar da harin, amma ba su tabbatar da adadin wadanda aka sace ba, saboda har yanzu ana tattara bayanai.
Gwamnatin jihar Neja ta yi ikirarin cewa makarantar ta na gudanar da ayyuka ne ba bisa ka'ida ba, domin tuni aka ba da umarnin a rufe ta saboda barazanar tsaro.
A cewar gwamnatin jihar, wannan rashin bin ka’ida ne ya jefa daliban makarantar cikin hatsari a lokacin da 'yan bindigar suka farmake su, kamar yadda muka ruwaito.
Gwamna ya ba da umarnin rufe makarantu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kwara ta bada umarnin rufe dukkanin makarantu kananan hukumomi hudu saboda karuwar rashin tsaro.
Sanarwar da NUT ta karanta ta ce za a rufe makarantu a kananan hukumomi hudu ciki har da Irepodun, Ifelodun da Ekiti, kuma za a rufe su nan take.
Gwamna AbdulRahman Abdulrazaq ya bukaci a kafa sansanin soji a yanin Eruku, garin da 'yan bindiga suka kai hari, har ma suka sace masu ibada.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


