Tinubu Ya Fadi yadda Jonathan Ya Ceto Siyasar Najeriya da Taimakonsa da Ya Yi
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana gudunmawa da tsohon shugaban kasa a Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya bayar
- Tinubu ya taya tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, murnar zagayowar ranar haihuwarsa, ya cika shekara 68
- Tinubu ya jaddada sadaukarwa da sauƙin hali da Jonathan ya nuna musamman a zaben 2015, wanda ya ƙarfafa dimokaradiyya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana game da tasirin siyasar tsohon shugaban kasa a Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan.
Tinubu ya tura sako na musamman tare da taya tsohon shugaban kasa, Jonathan, murnar cika shekaru 68 da haihuwa a makon nan.

Source: UGC
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Dada Olusegun, ya fitar a shafin X a jiya Alhamis 20 ga watan Nuwambar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya taya Goodluck Jonathan murna
Shugaban kasar ya taya iyalan Jonathan da abokai da ’yan siyasa murnar wannan rana ta musamman a gare su.
Ya yabawa dattijon saboda gudummawar da ya bai wa ƙasar nan tun daga lokacin yana kan mulki har zuwa yau, wanda ya kara darajar Najeriya da dimukaradiyyarta a idon duniya.
Shugaba Tinubu ya ce sauƙin hali da natsuwa sun kasance ginshikin jagorancin Jonathan, musamman yadda ya nuna salon kishin kasa a zaben 2015, lamarin da ya ƙarfafa dimokuraɗiyya kuma ya ba Najeriya girma a idon duniya.

Source: Getty Images
Tinubu ya tuna alakar siyasarsa da Jonathan
Tinubu ya kuma tuna tarurrukan da ya yi da Jonathan a lokacin da suke siyasa, da yadda goyon baya da shawarwarin da Jonathan ya samu suka taimaka wajen samun mukaminsa a 2010 da kuma zabensa na 2011.
Sanarwar ta ce:
"Shugaba Tinubu ya ce sauƙin hali da tawali’u su ne suka bambanta salon jagorancin Dr. Jonathan, musamman yadda ya nuna ƙwarin guiwar jagoranci a zaben 2015, abin da ya ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya ya kuma ba ƙasar ɗaukaka a idon duniya.
Shugaban ya kuma tuna tattaunawarsa da tsohon shugaban kasar a lokuta daban-daban, tare da goyon baya da shawarwarin da suka taimaka wajen hawan Dr. Jonathan kan karagar mulki, musamman a shekarar 2010 da kuma zaben shugaban kasa na 2011."
Shugaba Tinubu ya ce nagartar Jonathan har yanzu tana ƙara zuga shugabanni a Afrika, musamman yadda yake daukar nauyin aikace-aikacen diflomasiyya da nufin yaɗa dimokuraɗiyya a nahiyar.
Daga karshe, shugaban kasar ya yi addu’a Allah ya ci gaba da ba Jonathan lafiya, ya albarkaci matarsa Patience Jonathan, da iyalansa baki ɗaya.
Lokacin da Tinubu ya soki Jonathan saboda kashe-kashe
Mun ba ku labarin cewa zargin yi wa al'ummar Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a muhawara mai zafi a sassa daban-daban.
Wannan ya kara kamari ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump ya sanya Najeriya cikin kasashe masu matsala ta musamman kan batun cin zarafin Kiristoci.
A shekarar 2014, Shugaba Bola Tinubu ya taba sukar Goodluck Jonathan bayan an farmaki wasu al'ummomin Kiristoci a Arewacin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

