Faston da Ya Fara Maganar Kisan Kiristoci Ya Sake Bayyana a gaban Majalisar Amurka

Faston da Ya Fara Maganar Kisan Kiristoci Ya Sake Bayyana a gaban Majalisar Amurka

  • Fasto Wilfred Anagbe ya sake bayyana a gaban Majalisar Dokokin Amurka kan batun zargin kisan Kiristoci a Najeriya
  • Malamin addinin daga Benue ya ce Najeriya na fuskantar 'kashe-kashe masu kama da kisan kare dangi' kan Kiristoci
  • Ya yi magana kan kisan mutane 178 a Yelewata, kashe Fasto, garkuwa da malaman addini, tare da kai farmaki kan kauyuka da makarantu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Babban malamin addinin Kirista da ya fara kai korafi kan zargin kisan Kiristoci ya sake bayyana a gaban majalisar Amurka.

Fasto Wilfred Anagbe na Cocin Katolika ta Makurdi da jihar Benue, ya bayyana gaban Majalisar tare da jaddada ikirarinsa.

Fasto ya sake tona asiri a gaban majalisar Amurka
Fasto Wilfred Anagbe wanda ya bayyana a majalisar Amurka kna kisan Kiristoci. Hoto: @RealCharlesOgbu /@darth_kabowei.
Source: Facebook

Fasto ya tabbatar da kisan Kiristoci Najeriya

Rahoton Leadership ya ruwaito Faston na cewa Najeriya na fuskantar kisan kare dangi kan al’ummar Kirista, yana roƙon duniya ta shiga cikin lamarin da gaggawa.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: An kai karar Najeriya ga Majalisar Dinkin Duniya kan 'kisan Kiristoci'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin zaman binciken da aka shirya kan zargin tsananta wa Kiristoci, Fasto Anagbe ya ce halin da ake ciki ya lalace fiye da yadda ya bayyana a baya.

Ya ce hare-hare kan ƙauyukan Kiristoci sun ƙaru a Arewa ta Tsakiya da ma wasu sassan kasar.

Ya tuna cewa a 13 ga Maris 2025 ya bayyana irin hatsarin da ke tunkarar al’umma, amma cikin watanni shida kacal lamarin ya ta’azzara.

Ya ce kauyensa na Gwer ta Yamma an kai hari a ranar 22 ga Mayu 2025, an kashe ’yan uwansa, aka raba mata da iyalansu a cocin yankin.

Limamin cocin ya kuma ce a 24 ga Mayu 2025, an harbe wani Fasto, Solomon Atongo wanda aka bar shi jina-jina.

Fasto ya koka kan kashe-kashe a Benue
Taswirar jihar Benue da ke fama da matsalar tsaro a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda ake ci gaba da kashe-kashe a Benue

A Ranar 'Palm Sunday', 6 ga Afrilu 2025, ya ce yan ta'addan Fulani sun kai farmaki a Benue cikin jerin hare-haren da aka yi inda Kiristoci ke shirin bukukuwan addini.

Kara karanta wannan

Muhawara ta raba 'yan majalisar Amurka 2 kan zargin kashe Kiristoci a Najeriya

Ya kara da cewar a Yelwata, an kashe sama da mutane 178 maza, mata da yara cikin mugun yanayi.

Ya zargi gwamnati da ƙoƙarin rage adadin mutanen da aka kashe, kuma ta kasa ba wa wadanda suka tsira kulawar da ta dace.

A 17 ga Nuwamba 2025 kuma, ya ce an sace wani Fasto daga Kaduna, aka kashe ɗan uwansa, sannan aka kai hari wata makaranta a Kendi.

Fasto Anagbe ya ce rahotanni sun nuna har janar din sojoji da wasu jami’ai sun shiga hannun ’yan ta’adda, alamar yadda rikicin ke bazuwa.

Ya zargi gwamnati da rashin nuna kulawa, inda ya ce shiru da kin daukar mataki ya kara sa mutane jin an bar su cikin haɗari, cewar rahoton Daily Post.

An kai karar Najeriya gaban Majalisar Dinkin Duniya

Kun ji cewa Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Michael Waltz, ya kai karar Najeriya kan zargin kisan Kristoci wanda ya jawo maganganu.

Waltz ya kai korafin ne ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya domin daukar matakain da ya dace tun da wuri.

Kara karanta wannan

Trump: Wasu 'yan majalisar Amurka sun yi matsaya kan kai hari Najeriya

Ambassadan ya yi kira ga Najeriya ta dauki mataki kan sace ’yan mata 25 a Kebbi, yana mai cewa gwamnati dole ta kara tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.