Gwamna Bago Ya Fitar da Bayanai bayan Sace Daliban Makaranta cikin Dare a Neja

Gwamna Bago Ya Fitar da Bayanai bayan Sace Daliban Makaranta cikin Dare a Neja

  • Gwamnatin Neja ta ce ta samu rahoton sace ɗaliban makaratar St. Mary’s da ke Agwara duk da ba a tabbatar da adadin wadanda aka dauke ba
  • Ta bayyana cewa an riga an samu bayanan sirri da suka nuna hatsaniya a yankin, lamarin da ya sa ta rufe makarantun kwana baki daya
  • Gwamnati ta ce makarantar ta ci gaba da karatu ba tare da neman izini ba, sannan jami’an tsaro sun fara bincike da aikin ceto daliban

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Neja - Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana bakin ciki tare da tsananin damuwa game da sace wasu ɗalibai a makarantar St. Mary’s da ke Papiri, a karamar hukumar Agwara.

Wannan lamari, in ji gwamnati, ya faru ne a wani lokaci da ake ci gaba da fuskantar ƙarin barazana a yankin Neja ta Arewa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake shiga makaranta sun sace dalibai da malamai a Neja

Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago
Gwamna Umaru Bago na jihar Neja yana bayani. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

Gwamnatin ta tabbatar sace daliban ne a wata sanarwa da ta fitar a shafin gwamna Umaru Bago na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bayyana cewa har yanzu ba a tabbatar adadin ɗaliban da aka sace ba, domin hukumomin tsaro na ci gaba da tantance bayanai da nazari kan halin da ake ciki.

Gwamnati ta ce lamarin ya faru duk da cewa tun da farko an samu sahihan bayanan sirri da suka nuna yiwuwar ƙaruwar barazanar tsaro a yankuna da dama na Neja ta Arewa.

Makarantar ta saba umarnin gwamnatin Neja

A cewar sanarwar, gwamnatin Jihar Neja ta riga ta fitar da umarni na dakatar da duk wasu ayyukan gine-gine da kuma rufe dukkan makarantun kwana a yankin da ake fuskantar matsalar tsaro.

Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne domin rage hadari ga ɗalibai da malamai a yankin da ke fama da barazanar.

Sanarwar ta ce:

“Wannan umarni ya fito ne sakamakon samun bayanan sirri da suka nuna yiwuwar karin barazana a wasu sassan Neja ta Arewa.”

Kara karanta wannan

Asiri ya bankadu: An kama magidanci yana neman sulalewa da gawar matarsa a babur

Gwamnati ta bayyana takaici cewa, duk da wannan umarni, makarantar St. Mary’s ta bude ba tare da sanarwa ko neman izini daga hukumomin jiha ba.

Ta ce:

“Makarantar ta cigaba da karatu ba tare da wani izini daga gwamnatin jiha ba, abin da ya jefa ɗalibai da ma’aikata cikin hadarin da za a iya kauce masa.”

Jami’an tsaro sun fara bincike da aikin ceto

A cewar gwamnatin jihar, hukumomin tsaro sun kaddamar da cikakken bincike da aikin ceto domin gano inda aka kai ɗaliban da mayar da su gida cikin aminci.

Gwamnati ta ce tana tuntubar hukumomin tsaro kai tsaye domin samun sahihan bayanai yayin da abubuwa ke ci gaba da bayyana.

Sanarwar ta yi karin bayani cewa za a rika fitar da sababbin bayanai ga jama’a a hankali, da zarar an samu wata nasara.

Makarantar da aka sace dalibai a Neja
Hoton makarantar Katolika da aka sace dalibai a Neja. Hoto: Legit
Source: Original

Gwamnatin ta kuma bukaci al’ummar yankin da sauran mazauna jihar su kasance cikin kwanciyar hankali tare da taimakawa jami’an tsaro da bayanai da za su iya amfani da su.

Gwamnatin jiha ta bukaci shugabannin makarantu, masu ruwa da tsaki na al’umma, da sauran jama’a su tabbatar da bin dukkan shawarwarin tsaro domin kare rayuka, musamman na yara.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Tinubu ya umarci Matawalle ya tattara kayansa ya koma Kebbi

An bukaci Tinubu ya tare a Kebbi

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu ya kara kaimi wajen magance matsalar tsaro.

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa fasa tafiya kasashen waje da shugaban ya yi ba zai wadatar ba wajen magance matsalar.

Ta ce gwamnatin APC ta gaza daukar matakan da ya kamata wajen tabbatar da tsaro a Najeriya a halin yanzu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng