Sace Dalibai: Tinubu Ya Umarci Matawalle Ya Tattara Kayansa Ya Koma Kebbi

Sace Dalibai: Tinubu Ya Umarci Matawalle Ya Tattara Kayansa Ya Koma Kebbi

  • Shugaba Bola Tinubu ya nuna damuwa game da tabarbarewar tsaro musamman a yankin Arewacin Najeriya
  • Tinubu ya umarci karamin ministan tsaron kasa, Bello Matawalle ya koma Kebbi domin sa ido kan batun sace dalibai
  • Tinubu ya dage tafiyarsa zuwa Afrika ta Kudu da Angola, yana jiran rahotanni kan harin Kwara da sace ɗaliban Kebbi domin ɗaukar matakai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Ministan Tsaron Ƙasa, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi nan take.

An umarce shi da ya ci gaba da zama a jihar domin sa ido kan dukkan ayyukan tsaro da ake gudanarwa don ceto yaran da aka sace a makarantar GGCSS Maga.

Tinubu ya umarci Matawalle ya koma Kebbi
Shugaba Bola Tinubu da karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. Bayo Onanuga, Dr. Bello Matawalle.
Source: Twitter

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga shi ya tabbatar da a cikin wata sanarwa da ya rubuta a shafin X a yau Alhamis 20 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

Kiraye kiraye sun yawaita, ana son Tinubu ya yi murabus daga shugabancin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sace dalibai ya jawo hankalin duniya

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a garin Maga da misalin ƙarfe 4:00 na asuba a ranar Litinin 17 ga watan Nuwambar 2025 inda suka yi garkuwa da ɗalibai mata 25.

Sace daliban ya dauki hankulan al'umma har da wasu a kasashen waje duba da cewa yaran da aka sace mata ne masu kananan shekaru.

Lamarin ya sake tabbatar da yadda tsaro ke kara tabarbarewa musamman a yankunan Arewacin kasar da ke fama da fitintinu kala-kala.

Matakin fasa ziyarar Tinubu zuwa kasashen ketare

Dalilin haka, Shugaba Tinubu ya dage tafiye-tafiyensa zuwa Johannesburg da Luanda, domin jiran ƙarin bayanai kan sace daliban Kebbi.

Har ila yau, ya kuma nuna damuwarsa kan harin da ya rutsa da mabiya cocin CAC a Eruku da ke jihar Kwara wanda ya tayar da hankula sosai.

Wannan hari ya zo ne a daidai lokacin da ake zargin ana yawan kashe Kiristoci a kasar wanda gwamnatin tarayya ta musanta.

Kara karanta wannan

Ran maza ya baci: Tinubu ya umarci sojoji su ruguza 'yan ta'adda a Najeriya

Tinubu ya nuna damuwarsa kan sace dalibai a Kebbi
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Yaushe Matawalle zai wuce jihar Kebbi?

A cikin sanarwar, Onanuga ya bayyana cewa Matawalle zai isa Birnin Kebbi a ranar Jumma’a 21 ga watan Nuwambar 2025.

A cewar sanarwar, gwamnati ta ɗauki matakin ne saboda ƙwarewar Matawalle wajen fuskantar matsalar garkuwa da mutane, tun lokacin da yake gwamnan Zamfara tsakanin 2019 zuwa 2023.

A zamaninsa, an taba sace dalibai mata 279 a Jangebe daga hannun ‘yan bindiga, kafin daga baya a sako su.

Gwamnati ta ce ana ɗaukar duk matakan gaggawa domin tabbatar da tsaro da ceto rayuka.

Tinubu ya tura Shettima zuwa Kebbi

A baya, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nuna damuwa game da harin yan bindiga a jihar Kebbi wanda ya yi sanadin sace dalibai mata har guda 25 a makaranta.

Tinubu ya umarci mataimakinsa Kashim Shettima da ya ziyarci Kebbi domin jajantawa da kuma tabbatar da ceto ɗaliban inda ya nuna damuwa kan lamarin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan sace daliban Kebbi da rashin tsaro a Kano

Bola Tinubu ya bayyana bakin ciki kan kisan sojoji da suka haɗa da Birgediya Janar Musa Uba a Borno wanda ya ce hakan abin takaici ne da bai kamata ya afku ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.