Bidiyon Yadda Aka Wulakanta ’Yan Kwallon Najeriya a Jirgi, an Kira Su ’Yan Ta’adda

Bidiyon Yadda Aka Wulakanta ’Yan Kwallon Najeriya a Jirgi, an Kira Su ’Yan Ta’adda

  • Wani mutum ya tayar da rigima cikin jirgin ƙasa inda ya jefi matasan ƙwallon Najeriya na mata da ke wakiltar kasar da munanan kalamai
  • A bidiyon da ya yadu, mutumin ya ci gaba da zagi, yana cewa ya kamata matasan su ji kunya, yayin wasu Turawa ke ƙoƙarin hana shi
  • Ya bayyana wahalar da matasa yan Najeriya ke sha a ƙasashen waje, yana cewa gwamnati ta gaza, bai dace ƴan wasa su wakilci gwamnati ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bern, Switzerland - Wani mutum ya tayar da rigima yayin da matasan yan kwallon Super Falcons na Najeriya ke tafiya a cikin jirgin kasa.

Mutumin ya nuna bacin ransa game da matasan da ke wakiltar abin da ya kira kasar yan ta'adda ko gwamnatin yan ta'adda.

An samu hayaniya bayan kiran yan kwallon Najeriya yan ta'adda
Kungiyar Super Falcons yayin murnar zuwa kwallo. Hoto: @NGSuper_Falcons.
Source: Twitter

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Victor OG ya wallafa a Facebook wanda ya jawo maganganu kuma ya yadu a kafofin sadarwa.

Kara karanta wannan

'Yadda mutuwar Gaddafi a Libya ke ci gaba da zama barazana ga Najeriya'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musabbabin wulakanta 'yan kwallon Najeriya mata

A cikin bidiyon, an ji muryar mutumin yana kiran matasan wawaye duba da cewa ya kamata su waye game da abin da ke faruwa.

Wasu a cikin har da Turawa a gefe sun yi kokarin hana shi amma ya yi barazanar kiran yan sanda ga duk wanda ya taba shi.

Ya ce:

'Ina rayuwa a nan fiye da shekaru, sannan ku wadannan mutane kuna wakiltar kungiya ko gwamnatin yan ta'adda.
"Ku wadannan matasan ya kamata ku ji kunya kan abin da kuke yi, dukan daya daga cikinku ya kamata ya ji kunyar abin da yake yi.
"Hakan ba zai taba faruwa ba a kasashen Turai, a ce wasu na wakiltar gwamnatin da ta ke daurewa yan ta'adda gindi."
An yi ta jifan yan kwallon Najeriya mata da yan ta'adda
Wasu yan wasan kwallon kafar mata a Najeriya. Hoto: @NGSuper_Falcons.
Source: Twitter

Mutumin ya fadi wahalar da matasa ke sha

Mutumin ya bayyana irin wahala da matasa ke sha wanda kasar ta bari kara zube a kasashen waje suna gararamba.

Kara karanta wannan

Kebbi: Abin da ya faru kafin ƴan bindiga su kashe mataimakin shugaban makaranta

Ya ce abin takaici ne matasan da ya kamata su gane gaskiya amma su ne ke ci gaba da wakiltar gwamnatin da ke marawa yan ta'adda baya.

"Matasa suna shan wahala a Najeriya, fiye da matasa miliyan 10 suna gararamba a kasashen waje, kungiyar kwallon kafa bai kamata tana wakiltar yan ta'adda ba, kuma ku da ya kamata ku game amma kuna wakiltar gwamnatin yan ta'adda.
"Ka da kowa ya taba ni, duk wanda ya taba ni, zan kira yan sanda, nan ba Najeriya ba ne, mahaukata kuna wakiltar gwamnatin yan ta'adda.
"Ina kira gare ku matasa wawaye, ku guji wakiltar gwamnatin yan ta'adda, wannan abin kunya ne musamman ga kwallaon kafa."

- Cewar matashin a bidiyo

Tinubu ya raba daloli ga Super Falcons

Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya karrama ‘yan wasan Super Falcons da kyautar $100,000 da gidaje bayan sun lashe kofin WAFCON na 2025.

Shugaban kasar ya kuma ba 'yan wasan lambar girmamawa ta OON a liyafar da aka shirya masu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya karyata dan majalisar Amurka kan sace daliban Kebbi a 'yankin Kiristoci'

Najeriya ta doke Morocco da ci 3-2 inda Esther, Folashade da Echegini suka zura kwallo uku bayan Morocco ta fara jan ragamar wasan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.