A Karshe, Kotu Ta Kama Nnamdi Kanu da Laifin Ta'addanci, Ta Yanke Masa Hukunci
- Babbar kotun tarayya ta samu Nnamdi Kanu da laifi a tuhumar farko cikin tuhume-tuhumen da ake yi masa na aikata ta’addanci
- Mai shari'a James Omotosho ya ce masu shigar da kara sun gabar da hujjojin da suka gamsar da kotu cewa Kanu ya aikata laifi
- Yanzu haka dai kotun ta na ci gaba da zartar da hukunci kan tuhume-tuhume bakwai na ta'addanci da aka shigar kan Nnamdi Kanu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An samu babban sauyi a shari’ar da ake yi wa shugaban ƙungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, bayan kotu ta same shi da laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayyana cewa ta samu Nnamdi Kanu da laifin aikata ta'addanci a karar da gwamnatin tarayya ta shigar a kansa.

Source: Twitter
Kotu ta kama Nnamdi Kanu da laifin ta'addanci
Mai shari'a James Omotosho, wanda ke jagorantar shari’ar, ya bayyana cewa kotun ta gamsu da sahihancin hujjojin da masu shigar da ƙara suka gabatar, in ji rahoton Vanguard.
A cewar kotun, ta gamsu cewa Kanu ya yi jerin jawabai da dama a kafafen watsa labarai, inda jawabansa suka hura wutar tashin hankali, kashe-kashe da haifar da rikice-rikice a sassan Kudu maso Gabas.
Kotun ta yi nuni da cewa waɗannan jawabai sun taimaka wajen ƙarfafa masu goyon bayan kafa kasar Biafra yin tashe-tashen hankula, wanda hakan ya sabawa dokokin ƙasa.
Mai shari'a James Omotosho ya ce ya yanke hukunci ne bayan masu karar sun gabatar da kwararan hujjoji da wanda ake kara ya gaza jayayya a kansu.
'Kanu ya gaza kare kansa a kotu' - Alkali
Alkalin ya yi nuni da cewa Kanu bai dauki zabin da aka basa na fara kare kansa ba, yana mai cewa, "Ya gaza kare kansa, kuma ya ki ba da wasu gamsassun dalilai kan hakan."

Kara karanta wannan
Ba fashi: Alkali zai yankewa Nnamdi Kanu hukunci bayan fitar da shi daga harabar kotu
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa alkalin ya kuma ce Nnamdi Kanu ya ki ya gabatar da wasu kwararan hujjoji da za su kare kansa a tuhume tuhumen da aka shigar kansa.

Source: Facebook
Yanzu haka dai kotun ta na ci gaba da zartar da hukunci kan tuhume-tuhume bakwai na ta'addanci da aka shigar kan Nnamdi Kanu.
Wannan na zuwa ne bayan Kanu ya tayar da rigima a cikin kotu, wanda har ya tilasta wa Mai shari'a Omotosho ya ba da umarnin a fitar da shi daga kotun.
Kanu ya dage cewa ba za a iya karanta hukuncin ba illa sai idan kotu ta nuna masa dokar da ta haramtawa wanda ake tuhuma damar gabatar da rubutaccen jawabi.
Kanu: 'Yan majalisa sun aika sako ga Tinubu
Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan majalisar wakilai 44 sun fara kokarin lallaba Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya saki shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.
'Yan majalisar sun hada kai, sun rubuta wasika kai tsaye zuwa ga Shugaba Tinubu kan shari'ar da ake yi da jagoran masu fafutukar ballewa daga Najeriya.
Wasikar ta bayyana cewa ci gaba da tsare Nnamdi Kanu na kara dagula harkar tsaro a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, kuma sakinsa zai daidaita lamura.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

