CBN Ya 'Haramta' Amfani da Wani Banki Mai Rassa a Abuja, Kano da Wasu Jihohi 2

CBN Ya 'Haramta' Amfani da Wani Banki Mai Rassa a Abuja, Kano da Wasu Jihohi 2

  • Bankin CBN ya samu labarin yadda wani kamfani ke yada cewa yana da lasisin gudanar da harkokin banki a Najeriya
  • Bankin mai suna Zuldal Microfinance yana da rassa a jihohin Kano, Kaduna, Legas da kuma babban birnin tarayya Abuja
  • A wata sanarwa da CBN ya fitar yau Alhamis, ya gargadi 'yan Najeriya su guji mu'amala da wannan banki domin bai da lasisi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya nesanta kansa daga duk wani aiki da ya shafi bankin Zuldal Microfinance Bank.

CBN ya kuma gargadi 'yan Najeriya su kauce wa amfani da wannan banki saboda har yanzu ba shi da lasisin gudanar da aiki a Najeriya.

Gwamnan CBN, Yemi Cardoso.
Hoton gwamnan babban bankin Najeriya, Yemi Cardoso Hoto: @Centbank
Source: Getty Images

Hakan na kunshe ne a a wata sanarwa da Mai Rikon Mukamin Daraktan Hulɗa da Jama’a na CBN, Hakama Sidi Ali, ta fitar ranar Alhamis, kamar yadda Channels tv ta kawo.

Kara karanta wannan

Pantami ya yi Allah wadai da hare hare, ya samo mafita ga gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sharadin da dole banki ya cika a Najeriya

Babban bankin Najeriya ya ce babu wani banki da ke da ikon gudanar da ayyukansa har dai ya samu lasisi daga CBN kuma kamfaninsa ya yi rijista bisa tsarin dokar kasa.

CBN ya ce dokar gudanar da harkokin bankuna ta BOFIA 2020, sashe na 2(1), ya fayyace cewa:

“Ba wanda zai gudanar da harkokin banki a Najeriya sai idan kamfani ne da aka yi masa rijista a Najeriya kuma yana da lasisin banki daga CBN.”

Shin bankin Zuldal na da lasisi?

CBN ya ce ya samu rahotanni cewa bankin, wanda yake ikirarin yana da rassan aiki a Lagos, Abuja, Kaduna da Kano, yana ayyana kansa a matsayin Microfinance Bank da aka ba lasisi.

Bankin ya bayyana a sarari cewa:

“Zuldal Microfinance Bank Limited ba bankin Microfinance ba ne da aka bai wa lasisi, kuma babu wani izini daga CBN da ya amince masa ya gudanar da harkokin banki ko kudi a Najeriya.”

Kara karanta wannan

'Yadda mutuwar Gaddafi a Libya ke ci gaba da zama barazana ga Najeriya'

Bankin CBN ya ƙara da cewa duk wani ikirari da kamfanin yake yi na cewa an ba shi lasisi ƙarya ce kuma a yi watsi da shi.

Bankin CBN.
Hoton babban ofishin CBN da ke Abuja Hoto: @centbank
Source: Twitter

CBN ya ja kunnen 'yan Najeriya

A ƙarshe, babban bankin kasa, CBN, ya gargadi ‘yan Najeriya da su guji yin mu’amala ko wata hulɗa ta kuɗi da bankin, yana mai jaddada cewa:

“Duk wanda ya shiga mu’amala da Zuldal Microfinance Bank Limited yana yin hakan ne bisa ra'ayin kansa kuma duk matsalar da ta biyo baya kar ya zargi kowa ya zargi kansa.”

CBN ta shawarci jama’a da su tabbatar da sahihancin kowace cibiyar kuɗi kafin yin hulɗa da ita don kare kansu daga zamba da asarar kuɗi, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

An nemi CBN ya kawo takardun N10,000

A wani rahoton, kun ji cewa masana tattalin arziki daga Quartus Economics sun bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya fitar da sababbin takardun kuɗi.

Rahoton da suka fitar ya nemi a samar da takardun N10,000 da N20,000 domin rage wahalar hada-hadar kuɗi da inganta sauƙin amfani da Naira.

Kara karanta wannan

Ran APC ya baci, ta dura kan PDP bayan saboda taimakon Trump a Najeriya

Masanan Quartus Economics sun ce idan aka kwatanta da shekarar 2005, lokacin da aka samar da N1,000 a karon farko, darajarta ta kai kusan Dala 7, amma yau ba ta kai Dala daya ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262