Pantami Ya Yi Allah Wadai da Hare Hare, Ya Samo Mafita ga Gwamnati

Pantami Ya Yi Allah Wadai da Hare Hare, Ya Samo Mafita ga Gwamnati

  • Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi magana kan hare-haren da ake fama da su a kasar nan
  • Majidadin na Daular Usmaniyya ya yi Allah wadai kan yadda hare-haren suka jawo asarar rayuka da sace mutane
  • Hakazalika, ya ba hukumomin tsaro shawarar hanyar da ya kamata su bi domin cafke mutanen da ke aikata irin wadannan laifuffuka

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana takaicinsa kan karuwar tashin hankali a fadin Najeriya.

Tashe-tashen hankulan dai sun haifar da munanan hare-hare da garkuwa da mutane da dama a jihohin Kebbi da Zamfara.

Pantami ya yi Allah wadai kan hare-hare
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami Hoto: @ProfIsaPantami
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa tsohon ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, ya yi kira ga hukumomin gwamnati da su gaggauta ɗaukar sababbin dabaru na zamani da ke amfani da fasaha domin yaƙar ta’addanci da kuma kare rayukan ’yan kasa.

Kara karanta wannan

Ran maza ya baci: Tinubu ya umarci sojoji su ruguza 'yan ta'adda a Najeriya

Farfesa Isa Pantami ya lissafo hare-hare

Pantami ya yi Allah-wadai da jerin mummunan al’amura da suka faru cikin ’yan kwanakin nan, shafin @pipfoundation ya sanya sanarwar a X.

A ranar 16 ga Nuwamba, ’yan ta’adda sun yi garkuwa da shugaban kungiyar dalibai Musulmai na kasa (MSSN) a Kebbi, Alqasim Uthman Ibrahim, daga bisani kuma suka kashe shi.

A ranar 17 ga Nuwamba, an sace ’yan mata 25 daga makarantar GGCSS, Maga, a jihar Kebbi, sannan suka kashe mataimakin shugaban makarantar, Hassan Yakubu Makuku, yayin kare daliban tare da raunata wani mai gadi.

Jihar Zamfara ma ta fuskanci tashin hankali a ranar 18 ga Nuwamba, lokacin da ’yan bindiga suka kutsa garin Fegin Baza suka kashe mutane uku, ciki har da Umaru Moriki, Sarkin Fadan Moriki.

An yi garkuwa da akalla mutum 64, mafi yawansu mata da yara, inda aka kwantar da mutanen da suka ji rauni a asibitin Tsafe.

Mummunar tashin hankalin ya bazu har zuwa jihar Kwara inda aka kai hari cocin Christ Apostolic Church a Eruku, da kuma jihar Borno.

Kara karanta wannan

An 'gano' jihohi 8 da 'yan ta'adda za su iya kai mummunan hari a Najeriya

Daga cikin wadanda suka rasu akwai Birgediya Janar Musa Uba, wanda ya mutu a kusa da Damboa. Fararen hula da jami’an tsaro da dama sun rasa rayukansu ko suka jikkata.

Wace shawara Pantami ya bada?

Pantami ya bayyana cewa amfani da dabarun tsaro na zamani da fasaha zai taimaka wajen kama miyagun da suka aikata laifuffuka, kare jama’a, da dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Ya roki ’yan Najeriya da su hada kai da hukumomin tsaro ta hanyar ba su muhimman bayanai don magance ta’addanci da laifuffukan da ke da nasaba da shi.

Pantami ya ba gwamnati mafita
Majidadin Daular Usmaniyya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami Hoto: @ProfIsaPantami
Source: Twitter

Sheikh Pantami ya aika da ta'aziyya

Tsohon ministan, wanda ke rike da sarautar Majidadin Daular Usmaniyya, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu, tare da yin Allah wadai da hare-haren wadanda ke nuna yadda matsalar tsaro ke karuwa a kasa.

Ya yi addu’ar Allah Ya ba iyalan mamatan hakuri, Ya kare wadanda aka yi garkuwa da su, Ya warkar da wadanda suka jikkata, Ya kuma karfafa jami’an tsaro wajen ci gaba da aikin dawo da zaman lafiya.

Shettima ya dauki alkawari da aka sace dalibai

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya karyata dan majalisar Amurka kan sace daliban Kebbi a 'yankin Kiristoci'

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima, ya je jihar Kebbi domin jaje kan dalibai mata da 'yan bindiga suka sace.

Kashim Shettima ya daukarwa iyayen daliban alkawarin cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin kubutar da su.

Hakazalika, ya yi alkawarin cewa za a tura dukkan kayan aikin tsaro da ke hannun gwamnati domin tabbatar da cewa an dawo da yaran ba tare da wata cutarwa ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng