Ba Fashi: Alkali zai Yankewa Nnamdi Kanu Hukunci bayan Fitar da Shi daga Harabar Kotu

Ba Fashi: Alkali zai Yankewa Nnamdi Kanu Hukunci bayan Fitar da Shi daga Harabar Kotu

  • Alkalin Babbar Kotun Tarayya Abuja, Mai Shari’a James Omotosho, ya ce za a yanke hukuncin shari’ar Nnamdi Kanu a wannan rana ta Laraba
  • Za a yanke hukuncin ne duk da an fitar da Kanu daga zauren kotu bayan ya zargi alkalin da son rai, tare da tayar da hayaniya ana tsaka da shari'a
  • Kafin a fitar da shi daga kotun, James Omotosho ya ce sababbin bukatun da ya gabatar a gabansa ba su cancanci a saurare su ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin Mai Shari’a James Omotosho, ta yi bayani a kan yanke hukuncin shari’ar shugaban ƙungiyar IPOB Nnamdi Kanu.

Alkalin ya bayyana cewa za a yanke hukuncin a wannan rana duk da cewa an fitar da Shugaban haramtacciyar kungiyar kamar yadda aka tsara da farko.

Kara karanta wannan

A karshe, kotu ta kama Nnamdi Kanu da laifin ta'addanci, ta yanke masa hukunci

Kotu ta yi magana kan shari'ar Nnamdi Kanu
Shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB Hoto: Omoleye Sowore
Source: Twitter

Channels TV ta wallafa cewa wannan sanarwa ta biyo halin Kanu da kotu ta bayyana a matsayin rashin ladabi da zubar da mutunci yayin cigaba da shari’ar a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ci gaba da shari'ar Nnamdi Kanu

Daily Post ta wallafa cewa kotun ta bayyana cewa tun da farko an riga an kai ƙarshen shari’ar, an kammala muhawara, kuma an ɗage zaman domin yanke hukunci.

Sai dai kafin yanke hukuncin da aka tsara yi ranar Alhamis, 20 ga Nuwamba 2025, Kanu ya dage cewa ba za a cigaba da zama ba saboda a cewarsa bai kammala shigar da jawabansa na karshe ba.

Za a yankewa Nnamdi Kanu hukunci a ranar Alhamis
Hoton Nnamdi Kanu a yayin zaman kotu Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

Wannan batu nasa ya tayar da kura a kotu, inda ya fara daga murya, yana zargin alkalin da nuna bambanci, tare da cewa Omotosho bai san doka ba.

Saboda haka, Mai Shari’a Omotosho ya umarci jami’an tsaro da su fitar da Kanu daga zauren kotu saboda ya hana cigaba da gudanar da zaman a cikin natsuwa.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu ya birkita kotu yayin da za a yanke masa hukunci kan ta'addanci

Kotu ta yi magana kan bayanan Nnamdi Kanu

A yayin zaman na ranar Alhamis, Mai Shari’a Omotosho ya kuma yi watsi da sababbin bukatun da lauyoyin Kanu suka gabatar.

Mai Shari'a Omotosho ya bayyana bukatu guda uku da aka shigar gabansa a matsayin wadanda ba su cancanta a saurare su ba .

Alkalin ya ce dukkannin bangarorin sun riga sun gabatar da hujjojin su, kuma babu wata hujja da zata sa a sauya wa shari’ar alkibla a wannan mataki.

Ya ce:

“Kotun ba za ta ci gaba da lamuntar jinkiri marar tushe ba.”

Bayan fitar da Kanu daga dakin shari’ar, kotu ta cigaba da shirin karanta hukuncin da aka yankewa Nnamdi Kanu a kan zargin ta'addanci.

Ana sa ran kotun za ta bayyana hukuncin ta a hukumance a kwanaki masu zuwa, a yayin da jama'a ke dakon bayanan da za a fitar.

Nnamdi Kanu ya rikita zaman kotu

A baya, mun ruwaito cewa an samu hayaniya a Babbar Kotun Tarayya Abuja yayin shari’ar Nnamdi Kanu, da ya nemi kotu ta nuna masa dokar da ta hana shi gabatar da rubutaccen jawabi.

Kara karanta wannan

Tinubu zai nada jakadu bayan DSS ta mika sunayen mutanen da ta tantance

Zaman ya rikide zuwa hayaniya ne bayan da Kanu ya dage cewa ba za a karanta hukunci ba sai kotu ta nuna masa takamaiman dokar da ta haramta masa gabatar da jawabin karshe a rubuce.

Kanu, wanda a halin yanzu yake tsare kan tuhumar ta’addanci, ya kara da jayayya cewa kotu na ƙoƙarin tauye masa haƙƙinsa na kare kansa a shari'ar da ake shafe shekaru ana yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng