Me Ke Faruwa? Fusatattun Matasa Sun Rufe Babban Titi a Arewa, Sun Hana Kowa Wucewa
- Wasu fusatattun matasa jihar Kwara sun toshe hanyar Ilorin–Kabba saboda harin da 'yan bindiga suka kai wani coci
- ’Yan bindiga sun yi kaca-kaca da cocin CAC Oke-Isegun, inda suka kashe mutane tare da yin awon gaba da masu ibada
- Yayin zanga-zangar matasan, jami’an ’yan sanda, DSS da sojoji sun isa yankin, sun tura karin jami’ai da motar APC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Tashin hankali ya ƙara kamari a Eruku, cikin karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara, ranar Laraba, bayan matasa sun rufe hanyar Ilorin–Kabba.
Matasan sun rufe babbar hanyar domin nuna bacin ransu kan harin da ’yan bindiga suka kai garinsu.

Source: Twitter
Harin 'yan bindiga ya fusata matasan Kwara
Wannan rufe hanyar ya haddasa cunkoson manyan motoci da ke kan hanyarsu ta zuwa Kogi, in ji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Al’amuran sun kai makura ne bayan ’yan bindiga sun kai hari cocin Christ Apostolic Church, Oke-Isegun, da yammacin ranar Talata.
A yayin wannan mummunan harin, mun rahoto cewa 'yan ta'addan sun kashe mutane uku sannan suka yi awon gaba da akalla mutum 10 cikin masu ibada.
A cewar mazauna yankin, 'yan ta'addar sun shafe akalla awa guda suna cin karensu ba babbaka ba tare da zuwan jami'an tsaro ba.
Fusatattun matasa sun tare hanyar Ilorin-Kabba
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, bayan sun tare hanyar Ilorin-Kabba, Timothy Joshua, ya nuna matukar fushinsa kan wannan hari.
An rahoto cewa akwai matar Timothy Joshua da jikarsa a cikin masu ibadar da 'yan ta'addan suka sace, lamarin da ya ce akwai sakacin jami'an tsaro a ciki.
Haka nan shugaban matasa, Peter Adesiyan, ya ce suna ba da gudunmawa ga tsaron yankin amma abin da ya faru ya karya musu zuciya.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kashe malamin addini, sun sace masu ibada a Kwara
Wasu mazauna garin sun ce suna rayuwa cikin fargaba saboda hare-haren da ke yawan faruwa a yankunan da ke kan iyaka da Kogi da Ekiti.

Source: Original
’Yan sanda, DSS da sojoji sun isa Eruku
Kwamishinan ’yan sanda na jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya isa Eruku tare da daraktan DSS na jihar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
CP Adekimi Oyo ya bai wa mazauna garin tabbacin karin jami’ai da tura motar daukar jami'ai ta sulke (APC) domin ƙarfafa tsaro a yankin.
Sarkin yankin, Oba Busari Arinde Oyediran Olanrewaju, ya roki matasa su kwantar da hankalinsu su bar jami’an tsaro su gudanar da bincike.
A halin yanzu, sojoji sun karɓi ragamar tsaron yankin, bayan wani bidiyo da ya nuna ’yan bindiga suna harbi a cikin cocin yayin da mutane ke gudun tsira.
'Yan bindiga sun mamaye garuruwan Kwara?
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kwara ta warware rudanin da aka samu game da cewa 'yan bindiga sun mamaye wasu kananan hukumomi a jihar.
Kwamishinar yaɗa labarai ta jihar, Mrs. Bolanle Olukoju, ta bayyana cewa babu wani yankin jihar da ke karkashin ikon ‘yan bindiga.
Gwamnatin ta kuma nuna yatsa ga Peter Obi kan yada abubuwan da ba haka suke ba dangane da rashin tsaron jihar a shafukan sada zumunta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

