"Su Nemi Taimako": Amaechi Ya Ga Gazawar Gwamnati wajen Yaki da Ta'addanci
- Tsohon Ministan sufuri a gwamnatin Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi ya soki gwamnatin tarayya kan karuwar ta'addanci a Najeriya
- Ya bayyana cewa yawaitar kashe-kashe da garkuwa da mutane a cikin mako guda ya nuna cewa gwamnati ba ta da niyyar magance matsalar
- Amaechi ya jaddada cewa za su iya taimakawa gwamnati ta hanyar koya mata yadda ya kawo karshen rashin tsaro a jihar Ribas
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri, Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi, ya caccaki gwamnatin tarayya saboda karuwar matsalolin tsaro.
Ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da cewa ba ta da niyyar dakile ta’addanci da hare-haren da suka addabi Najeriya, musamman saboda yadda suke karuwa a 'yan kwanakin nan.

Source: Twitter
Amaechi, wanda ya wallafa takaicinsa a shafinsa na X, ya ce gwamnati ta kasa sauke babban nauyin da doka ta dora mata na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
Amaechi ya dura kan gwamnatin Tinubu
A cewar Rotimi Amaechi, samun karuwar hare-hare a Najeriya ya samo asali ne daga gazawar gwamnati na yin tsayin-daka a kan rashin tsaro da dakile 'yan ta'adda.
Ya ce:
“Gwamnati ta nuna gazawa wajen kare rayukan jama'a, musamman ganin cewa hare-haren ta’addanci da garkuwa da mutane sun karu a wasu yankunan ƙasar. Wannan rashin tsayin daka ya kara ƙarfafa gwiwar 'yan ta'adda.”

Source: Twitter
Tsohon ministan ya yi nuni da jerin munanan hare-haren da suka faru cikin mako guda, wadanda suka hada da kashe-kashe a Filato da sace dalibai mata a Kebbi.
Amaechi ya kuma bayyana takaicin kwanton bauna da aka yiwa sojoji a Borno da ya yi sanadiyyar sacewa da kisan Birgediya Janar M. Uba da hari kan coci a Kwara.
Ya kuma ce abin a yi tir ne yadda 'yan ta'adda suka sace limamin Katolika, Rabarran Fr. Bobbo Paschal, a Kaduna.
Shawarar Amaechi ga gwamnatin Najeriya
Amaechi ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sake fasalin yadda take yaki da ta’addanci, tare da daukar sababbin dabaru da inganta bayanan sirri na soji da sauran jami’an tsaro.
Ya ce lokaci ya yi da shugaban kasa zai daina fifita taruka da tafiye-tafiye a yayin da al’umma ke kuka saboda azabar da suke sha a hannun 'yan ta'adda.
A kalamansa:
“Babban aikin Shugaban Kasa shi ne kare rayuka da dukiyoyi."
Ya kara da cewa Najeriya na bukatar jagoranci nagari, cikakken hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, da tabbatar da masu laifi sun fuskanci hukunci.
Amaechi ya shaida cewa irin nasarar da aka samu a jihar Ribas a gwamnatinsa na nuni da cewa ana iya samun sauyi a matakin kasa baki daya.
Ya ce:
“Mun yi hakan a Jihar Ribas; za a iya yi a Najeriya. A shirye mu ke mu ba da gudummawa idan an bukata.”
Tsaro: Manyan Najeriya sun isa Amurka
A baya, mun wallafa cewa tawagar gwamnatin tarayya ta isa Amurka domin bayyana ainihin matsayar Najeriya game da zarge-zargen da ake yaɗawa na cewa ana cin zarafin Kirista a ƙasar.
Wannan batu ya sake tasowa ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya mayar da Najeriya cikin jerin kasashen da ake sa ido a kansu saboda batutuwan ‘yancin addini.
Gwamnatin Najeriya ta dade tana kokarin bayyana cewa rikice-rikicen da ake fama da su a yankuna daban-daban ba rikicin addini ba ne, illa rikicin ƙabilanci da na makiyaya da manoma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


