Ribadu da Manyan Najeriya Sun Isa Amurka, Sun Tattauna Batun Rashin Tsaro
- Tawagar da Nuhu Ribadu ya jagoranta ta gana da dan majalisar Amurka, Riley Moore kan zargin wariyar addini a Najeriya
- Gwamnatin Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin kasashe masu matsala ta musamman saboda zargin cin zarafin Kirista
- Hon. Moore ya ce tattaunawarsu ta kasance a fili, inda ya bukaci matakan da za su tabbatar an kare mabiya addinin Kirista
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka - Tawaga mai ƙarfi daga gwamnatin tarayya ta isa Amurka domin bayyana matsayar Najeriya kan zarge-zargen da ake yadawa na cewa ana cin zarafin Kirista a kasar.
Wannan zargi dai ya kara yin karfi ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake kula da su saboda matsalolin addini.

Source: Facebook
A cikin wani rubutu da dan majalisar Amurka, Riley Moore, ya wallafa a X ya tabbatar da ganawarsa da tawagar Najeriya, yana mai cewa tattaunawar ta kasance mai amfani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Najeriya ta sha kokarin yin karin bayani kan cewa rikice-rikicen da ake fama da su a kasar ba na addini ba ne.
Duk da haka, gwamnatin Amurka ta ci gaba da jaddada cewa akwai alamun wariyar addini da ke bukatar kulawa ta musamman.
Tattaunawar tawagar Najeriya da Amurka
Tawagar Najeriya karkashin jagorancin Nuhu Ribadu ta hadu da Moore domin yin bayanin matsalolin tsaro da tasirin da rikice-rikicen suka yi wa al’umma.
Moore ya ce:
“A yau, na yi tattaunawa da manyan jami’an gwamnatin Najeriya kan tashin hankalin da Kiristoci ke fuskanta da kuma barazanar da ta’addanci ke yi a fadin Najeriya.
"Na fayyace cewa dole Amurka ta ga matakai na zahiri da za su tabbatar cewa ba a bar Kiristoci cikin tashin hankali, tsangwama, ko kisa saboda addininsu ba.”
Ya ci gaba da cewa:
“Mun shirya aiki tare da Najeriya domin yaki da Boko Haram, ISWAP da kuma wasu kungiyoyi da ake zargi da kai hare-hare musamman a Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.
"Gwamnatin Najeriya tana da damar karfafa alakar ta da Amurka. Shugaba Trump da majalisa suna da niyyar kawo karshen tashin hankali da keta hakkin mabiya Kirista a Najeriya.”

Source: Getty Images
Manyan Najeriya da suka je Amurka
Tawagar ta ƙunshi mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, wanda shi ne shugaban tafiyar; ministar harkokin wajen waje, Bianca Ojukwu; sufeton ’yan sanda, Kayode Egbetokun.
Daga cikin tawagar akwai Antoni Janar na tarayya, Lateef Olasunkami Fagbemi; hafsun tsaro, Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede da Laftanar Janar EAP Undiendeye na rundunar leken asiri.
Daily Trust ta rahoto cewa mai ba Ribadu shawara ta musamman, Idayat Hassan; daraktan hulda da ƙasashen wajensa, Ibrahim Babani na cikin tawagar.
Saura sun hada da mukaddashin shugaban ofishin jakadancin Najeriya, Ambasada Nuru Biu da jami’in sashen siyasa da tattalin arziki na ofishin jakadancin Najeriya, Paul Alabi.
Abin da Najeriya ke nema a tattaunawar
Najeriya ta bayyana cewa matsalolin tsaro da take fama da su sun samo asali ne daga ta’addanci, satar mutane, rikicin makiyaya da manoma da kuma karancin kayan yaki.
Gwamnatin ta nemi Amurka ta kara tallafa wa rundunonin tsaro, musamman wajen kayan aiki, bayanan sirri da horo.
An nemi Tinubu ya dauki sojoji 100,000
A wani labarin, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta yi muhawara game da sace dalibai mata da aka yi a Kebbi.
A tattaunawar da ta yi, majalisar ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki dakarun soja 100,000.
Ta ce karancin jami'ai a rundunar sojin Najeriya na daga cikin abin da ke kara ruruta matsalar tsaro a fadin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

