Tashin Hankali: Sojojin da Suka Je Ceto Ɗaliban Kebbi Sun Faɗa Tarkon Ƴan Bindiga
- Dakarun Najeriya sun jikkata bayan ’yan ta’adda sun yi masu kwanton-bauna a Kebbi yayin aikin ceto daliban GGCSS Maga
- Laftanal Janar Waidi Shaibu ne ya umurci sojojin su yi fitar kwari zuwa dazuzzuka domin ceto 'yan makarantar da aka sace
- Wannan na zuwa ne yayin da UNICEF ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ɗauki matakan tsaro masu ƙarfi a makarantu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kebbi - Sojoji da dama sun samu raunuka bayan wasu ’yan ta’adda sun yi masu kwanton-bauna a cikin dajin Danko Wasagu da ke jihar Kebbi.
Dakarun sojojin sun fada komar 'yan bindigar ne a lokacin da suka fita aikin ceto daliban makarantar GGCSS Maga, karamar hukumar Danko/Wasagu.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun farmaki sojoji a Kebbi
Harin ya zo ne kwanaki bayan sace daliban, inda dakarun suka shiga cikin dazuzzuka da dama domin kubutar da daliban da kuma kama 'yan ta'addar, in ji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani bidiyo da aka samu ya nuna dakarun sojojin suna kwance cikin jin raɗaɗin raunukan da suka samu, yayin da wasu sojoji ke kokarin taimaka musu.
Faifan bidiyon ya kuma nuna motar rundunar dauke da ramukan harsashi, alamar tsananin harbin da suka sha daga ’yan ta’addan.
A cikin faifan, wani sojan ya ce harsashi ya samu abokinsa Musa a ƙafa, kuma yanayinsa ya kara ta’azzara.
An tura dakarun sojoji ceto daliban Kebbi
Sojojin sun yi ta kira ga jami’an jinya domin a zo a taimaka musu cikin gaggawa saboda tsananin ciwo da jinin da suke zubarwa.
Kafin harin, hafsan sojojin kasa, COAS, Laftanal Janar Waidi Shaibu ya gana da shugabannin al'umma domin karfafa aikin ceto yaran cikin tsari mai inganci.
A yayin ziyarar, Shaibu ya umurci dakarun Operation Fasan Yamma da su yi fitar dango, su ceto daliban, yana nanata cewa hukumar soji ba za ta yarda da gazawa ba.
Laftanal Janar Shaibu ya ce dole ne a gaggauta yin aiki kan duk wani bayanan sirri da aka samu da zai taimaka wajen kubutar da yaran, a cewar wani rahoton Daily Trust.
Hafsun sojoji ya gargadi dakarun Fansan Yamma
Hafsun sojoji ya ziyarci Hakimin Danko da shugabar makarantar, inda ya alkawarin cewa gwamnati za ta ceto daliban cikin kankanin lokaci.
Ya ce sojoji, ’yan sa kai, da mafarauta za su yi aiki tare domin tabbatar da cewa daliban sun dawo gida cikin koshin lafiya.
Hafsun ya kuma nanata cewa “nasara ba zaɓi ba ce ga sojoji,” inda ya yi gargadi ga dakarun da su yi aiki cikin ladabi da tsari sosai.

Source: Original
UNICEF ta yi kira da tsaurara tsaron makarantu
Wannan na zuwa ne yayin da hukumar UNICEF ta bayyana takaici kan harin, tana mai cewa dole a tsaurara tsaron makarantu domin kare dalibai a yankunan da rikici ya dabaibaye.
Hukumar ta tuna cewa Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Safe Schools domin tabbatar da tsaron makarantu da dalibai.
UNICEF ta bukaci hukumomi su aiwatar da tsauraran matakai domin hana maimaita irin waɗannan hare-hare a nan gaba.
'Na sanar da hukumomi kan harin Kebbi' - Getso
A wani labarin, mun ruwaito cewa, masanin tsaro Yahuza Getso ya zargi hukumomin Najeriya da sakaci bayan ya ba da rahoto kan harin da aka kai Kebbi.
Kebbi Getso ya ce ya sanar da hukumomin tsaro tun da wuri cewa 'yan bindiga za su kai hari, kuma da an ji maganarsa, da ba a sace daliban makarantar Maga ba.
'Yan bindiga dai sun kashe mataimakin shugaban makarantar kwana ta mata da ke Maga, inda suka yi awon gaba da dalibai 26 a safiyar ranar Litinin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


