Darasin Lissafi: Gwamna Abba Ya Fara Share Hawayen Daliban Makarantun Kano

Darasin Lissafi: Gwamna Abba Ya Fara Share Hawayen Daliban Makarantun Kano

  • Gwamma Abba Kabir Yusuf ya bai wa sababbin malaman darasin lissafi 400 takardun daukar aiki a jihar Kano
  • Ya ce malaman za su taimaka wajen cike gibin karancin masu koyar da darasin lissafi da ake da shi a makarantun sakandire
  • Wani malamin lissafi, Sanusi Isiyaku ya yaba wa gwamnan bisa wannan mataki, yana mai cewa malami na wahala a makarantu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnan Kano, Alhaki Abba Abba Kabir Yusuf na ci gaba da daukar matakai domin inganta makarantun sakandire a fadin jihar.

Sakamakon karancin malamai da ake fama da shi, Gwamna Abba ya dauki sababbin malamai da za su koyar da darasin lissafi a makarantun gwamnati.

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Hoton gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnati Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Majalisa na so Tinubu ya dauki sojoji 100,000 su gwabza da 'yan ta'adda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya dauki malamai 400 aiki

Tuni dai gwamnatin Kano ta bai wa wadannan malamai 400 takardun aiki na dindindin domin su fara koyarwa a makarantun sakandire na jihar.

Gwamnan ya ce daukar malaman na da nasaba kai tsaye da kokarin magance gibin darussa da ke shafar karatun dalibai da shirin su na shiga fannin sana’o’i a nan gaba.

Abba ya ce lissafi shi ne ginshiƙin kimiyya, fasaha, injiniyanci da kirkire-kirkire, don haka Kano na bukatar gina tubali mai karfi a wannan fanni domin ta iya yin gogayya a duniya.

Dalilin daukar malaman lissafi a Kano

Gwamna Abba ya ce matsalar karancin malamai, musamman a lissafi, ta kasance babbar tangarda ga ci gaban daliban da ke son kwarewa a fannonin Kimiyya, Fasaha, Injiniya da Lissafi (STEM).

Ya kara da cewa sababbin malaman za su taimaka matuka wajen inganta koyarwa, nasarar dalibai a jarabawa, tare da habaka hanyoyin shiga fannonin fasaha watau STEM.

Kara karanta wannan

Bayan sace ɗalibai 25 a Kebbi, Abba ya dauki mataki a makarantun Kano

Gwamnan ya yaba wa Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Kula da Makarantun Sakandare ta Jihar Kano (KSSSSMB) bisa gudanar da tsarin daukar aiki cikin gaskiya, tsari da adalci, in ji rahoton Daily Trust.

Ya kuma shawarci sababbin malaman da su yi aiki da himma, sadaukarwa da cikakkiyar kwarewa, yana mai jaddada cewa dole su tabbatar sun cancanci amincewar da aka nuna a gare su.

Gwamna Abba Kabur Yusuf.
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf ya na duba wasu takardu a fadar gwamnatin Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

An fara yaba wa Gwamna Abba

Sanusi Isiyaku, wani malamin lissafi a Kano, wanda ya yi karatu a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote, Wudil ya shaida wa Legit Hausa cewa gwamna ya yi abin a yaba.

A cewarsa, darasin lissafi na da matukar muhimmanci a kowane bangare kuma ya cancanci a bai wa harkar koyar da shi muhimmanci tun daga matakin farko.

Malam Sanusi ya ce:

"Na ji dadin wannan mataki saboda malaman lissafi na shan wahala a makarantun sakandire, za ka iya samun mutum daya ke koyar da darasin a makaranta guda, taya zai iya?
"Saboda haka, sababbin malaman za su taimaka matuka wajen ganin daliban Kano sun samu ilimin da ake bukata a fannin lissafi tun a matakin farko."

Kara karanta wannan

Gwamna Kefas ya dakatar da shirin shiga jam'iyyar APC, ya fadi dalili

An dauki masu gadin makarantu a Kano

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya amince da daukar masu tsaron makarantu domin aika su zuwa makarantun sakandare daban-daban a jihar Kano.

Gwamnan Abba ya ce samar da tsaro a makarantu na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ke mayar da hankali a kai.

Ya bayyana cewa ba za a samu ingantaccen ilimi ba har sai an tabbatar da tsaron dalibai da malamansu a duk inda suke karatu a Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262