'Hukumomi Sun San Za a Kai Hari Makarantar Kebbi, Suka Ƙi Ɗaukar Mataki,' In Ji Getso

'Hukumomi Sun San Za a Kai Hari Makarantar Kebbi, Suka Ƙi Ɗaukar Mataki,' In Ji Getso

  • Masanin tsaro Yahuza Getso ya zargi hukumomin Najeriya da sakaci bayan ya ba da rahoto, wanda ya kai ga sace daliban Kebbi
  • Getso ya ce ya sanar da hukumomin tsaro tun da wuri cewa 'yan bindiga za su kai hari, amma babu wanda ya dauki mataki
  • 'Yan bindiga dai sun kashe mataimakin shugaban makarantar kwana ta mata da ke Maga, inda suka yi awon gaba da dalibai 26

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wani masanin tsaro, Yahuza Getso ya dora laifin sace dalibai mata a makarantar GCGSS Maga, jihar Kebbi kan hukumomin Najeriya.

Yahuza Getso ya bayyana cewa, sai da ya sanar da hukumomin gwamnati da na tsaro cewa 'yan bindiga suna shirin kai hari, amma ba a dauki mataki ba.

Masanin tsaro ya ce sai da ya yi gargadi game da harin Kebbi amma ba a dauki mataki ba.
Hoton Yahuza Getso, masanin tsaro da na makarantar Kebbi da aka sace dalibai. Hoto: @YahuzaGetso
Source: Twitter

A zantawarsa da Channels TV a ranar Laraba, masanin ya ce kin daukar mataki bayan ya ba da rahoton harin ne ya jawo aka sace dalibai mata 26.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Sanatan Amurka ya taso gwamnati a gaba kan sace dalibai a Kebbi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Na fadawa hukumomi batun harin Kebbi' - Getso

A cewar Yahuza Getso, abin da ya faru a Kebbi ya nuna tsantsar zagon kasa da ake yi wa Najeriya, musamman ta fuskar tsaro.

"Wannan tsantsar sakaci ne. Tsantsar zagon kasa ne ga jihar saboda, ni da nake magana yanzu, na ba da bayanai na harin da 'yan bindiga ke shirin kai wa wasu kananan hukumomi.
"Na tura bayanan ga mafi kololuwar hukumar gwamnati, da hukumar fikirar tsaro, da mafi kololuwar tawagar tsaro da ke a Kebbi da ma Neja, da Abuja, da duk wadanda suka dace.
"Kuma bayan awanni uku, na sake kiransu, na fada masu: 'wadannan mutanen suna kan shirin kai hari. Suna wuri kaza yanzu.'
"Kuma fa, wannan tabbataccen bayanin sirri ne: ko a lokacin akwai jami'an sojoji ko dai wasu jami'an tsaro a makarantar amma suka bar wajen. Bayan sun tafi, cikin kankanin lokaci 'yan bindigar suka kai harin."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan sace daliban Kebbi da rashin tsaro a Kano

- Yahuza Getso.

Getso ya kira jami'an sojoji kan harin Kebbi

Getso ya yi ikirarin cewa ya kira wayoyin wasu manyan jami'an sojoji a lokacin da ake kai harin ba tare da ya samu amsa ba.

"Ko a lokacin da ake kan harin, na kikkira manyan jami'an tsaro. Idan har jami'an suna kallo na, sun sani; sun san na kira wayoyinsu lokacin da 'yan bindigar ke kai harin.
"Amma babu wanda ya daga wayata har zuwa lokacin nan da nake maku magana, ko su kira su tambaya me ya sa na kira, babu wanda ya kira, musamman kira a irin wannan lokaci.
"Ai sun san duk lokacin da na kira su a irin wannan lokacin, cikin tsakiyar dare, to wani abu ne ya faru wanda dole ana bukatarsu."

- Yahuza Getso.

'Yan bindiga dai sun sace dalibai 26 a makarantar kwana ta mata da ke Kebbi.
Hoton babbar bas mallakin makarantar GGCSS, Maga, jihar Kebbi, inda aka sace dalibai 26. Hoto: @AmnestyNigeria
Source: Twitter

'Da gangan hukumomi suka ki daukar mataki' - Getso

Da aka tambaye shi ko rashin daukar matakin da hukumomi suka yi kan bayanan sirrin da ya bayar za a iya kiransa 'abun da aka yi da gangan,' Getso ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamna Kefas ya dakatar da shirin shiga jam'iyyar APC, ya fadi dalili

"A iya fahimtata, da gangan ne aka ki amfani da bayanan sirrin da na bayar. Ai a al'adance, akwai lambobin kiran gaggawa na DSS, 'yan sanda, sojoji da sauransu.
"Duk wanda ya kira wadannan lambobi ya ba da rahoton sirri game da tsaro, to idan ba a dauki matakin gaggawa ba, to ya zama ganganci ke nan, kuma zagon kasa ne wannan."

'Yan bindiga dai sun kashe mataimakin makarantar GCGSS Maga, Malam Hassan Makuku, sannan suka yi awon gaba da dalibai 26.

Adadin daliban da aka sace a Kebbi

Tun da fari, mun ruwaito cewa, adadin daliban da 'yan bindiga suka sace a makarantar sakandaren kwana ta mata da ke Kebbi ya haura 25.

Kwamishinar ilimin Firamare da Sakandare ta jihar, Dr. Halima Muhammad Bande ta bayyana cewa dalibai 26 ne 'yan bindiga suka sace.

Wani mazaunin garin kuma dan uwa ga mahaifin daya daga cikin daliban da aka sace, Abubakar Dabai ya bayyana cewa har yanzu suna cikin tashin hankali.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com