Abba Ya Miƙawa Majalisa Kasafin 2026, a Karon Farko Kano Za Ta Kashe N1.3tr
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya kai Naira tiriliyan 1.36 ga Majalisar dokokin jihar Kano
- Gwamnati ta ware kashi 68 cikin 100 na kasafin don manyan ayyukan ci gaba, wanda shi ne mafi girma a tarihin jihar Kano
- Ilimi, gine-gine da lafiya sun samu kaso mafi yawa a kasafin, wanda hakan ke nuna bangaren da gwamnan ya fi ba wa muhimmanci
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da sabon kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai adadin N1,368,127,929,271 ga Majalisar dokokin jiha.
Gwamnan ya kara jaddada kudirin gwamnatinsa na kammala manyan ayyukan da aka fara da kuma zurfafa ci gaba da ya shafi kowa.

Source: Facebook
Wannan na kunshe a cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, kuma ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya mika kasafi ga majalisar Kano
Kasafin kudin ya ƙunshi kashi 68 cikin 100 na kuɗin manyan ayyuka, wanda ya kai N934.6bn, yayinda kudin gudanar da gwamnati ya tsaya a N433.4bn, wato 32%.
Wannan dai na daga cikin mafi girman rabon kasafin kudi manyan ayyuka da gwamnatin jihar ta taba warewa a shekarun baya-bayan nan.
Gwamnan ya ce rabon kasafi ya nuna sahihiyar manufar gwamnatinsa na mayar da hankali kan fannonin da za su ginaal'ummaɗorewa, musamman ta fuskar ilimi.
Gwamna Abba ya fayyace cewa bangaren Ilimi ne ya samu kaso mafi tsoka da N405.3bn (30%), wanda ke nuna jajircewarsa na tallafa wa ci gaban ɗalibai da inganta makarantun jihar.
Yadda Abba ya raba kasafin kudin Kano
Bangaren gine-gine da ababen more rayuwa ya samu N346.2bn (25%) a kasafin kudin, inda bangaren lafiya ya samu N212.2bn (16%).
Gwamna Abba ya ce:
“Wadannan rabe-raben kasafi suna nuna kokarin gwamnati na zuba jari a cigaban ɗan adam, inganta rayuwar jama’a, da kuma shimfiɗa tubalin ci gaba mai ɗorewa.”
Gwamnan ya kuma bayyana cewa an kuma ba wa bangaren tattalin arziki muhimmanaci a kasafin kudi na shekarar 2026.

Source: Facebook
Ya ce an tanadi kudi mai tsoka ga noman zamani, tsaro, kasuwanci, ruwa, muhalli, yawon bude ido, ci gaban mata da matasa, da kuma mutane masu bukata ta musamman.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da daidaita ayyukanta bisa bukatun jama’ar Kano, inda ya kira kasafin taswirar ci gaba da za ta taimaka wajen gina Kano.
Ya bukaci ‘yan majalisar su gaggauta duba kasafin ta fuskar da za ta taimaka wa mutanen Kano tare da amincewa da ita cikin gaggawa.
Tsohon gwamnan Kano ya magantu kan tsaro
A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya bukaci Bola Tinubu ya sake waiwayar matsalar tsaro da idon basira.
Ya ce matsalar tsaro ke ta’azzara a Najeriya, yana mai cewa lamarin ya kai wani mataki da dole gwamnatin tarayya ta tashi da gaggawa domin shawo kan shi ba tare da bata lokaci ba.
Kwankwaso ya fitar da wannan sako ne jim kadan bayan labarin sace dalibai mata sama da 20 a jihar Kebbi, abin da ya bayyana a matsayin abin tayar da hankali da tsoratarwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


