Kwankwaso Ya Yi Magana kan Sace Daliban Kebbi da Rashin Tsaro a Kano
- Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakan gaggawa don magance karuwar rashin tsaro
- Sanata Kwankwaso Ya nuna damuwa kan sace dalibai 25 a Kebbi, kisan Janar M. Uba a Borno da kuma yin garkuwa da mutane da yawa a Zamfara
- Ya kuma koka a kan yadda aka samu 'yan ta'adda suna kutsa wa wasu kananan hukumomi da ke gefe da garuruwan da ke fama da rashin tsaro
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya zafafa magana kan tsanantar matsalar tsaro a ƙasar nan.
Ya bayyana cewa lamarin ya kai wani matsayi da dole gwamnati ta mayar da hankali kai tsaye don magance matsalar ba tare da bata lokaci ba.

Source: Facebook
Rabiu Kwankwaso ya bayyana haka ne a wani sako da ya fitar a shafinsa na Facebook awanni kadan bayan sace dalibai a jihar Kebbi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso ya magantu kan sace daliban Kebbi
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana tsananin damuwarsa kan sace dalibai mata sama da 20 a jihar Kebbi.
Ya bayyana cewa wannan ya tuno da irin mummunan salon satar dalibai da aka sha gani a wasu shekarun baya.
Kwankwaso ya kuma yi yi tir da sacewa tare da kisan Birgediya Janar M. Uba a jihar Borno, yana mai kiran lamarin mummunan koma baya a yaki da ta’addanci.

Source: Facebook
Tsohon Ministan tsaron ya ce irin wannan kuskuren abu ne da ke bukatar gwamnati ta yi gaggawar gudanar da bincike domin dakile matsalar.
Haka zalika, jagoran na NNPP ya nuna bakin ciki kan garkuwa da mutane da yawa a Zamfara, yana mai kira ga hukumomi da su hanzarta kubutar da su.
Kwankwaso ya fusata da shigar 'yan ta'adda Kano
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya koka kan yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a Shanono da Ghari a jihar Kano, inda ya ce dole ne gwamnati ta tashi tsaye domin kare rayuwar jama’a.
Kwankwaso ya yaba wa gwamnatin Kano kan daukar matakin gaggawa, daga ciki har da bada motocin aiki ga jami’an tsaro.
Ya ce wadannan hare-hare babban koma baya ne a yaki da matsalar tsaro a Najeriya da ke bukatar a dauki matakin dakile su.
Tsohon gwamnan ya yi kira ga gwamnati da ta farfado da rundunonin soji da ‘yan sanda ta hanyar ba su kayan aiki na zamani da karfi, domin su kare al’umma yadda ya kamata.
Rabiu Kwankwaso ya burge gwamnatin tarayya
A baya, kun ji cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana jin dadinta da yadda tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa a NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso.
Hadimin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga ya ce martanin da Kwankwaso ya yi ya nuna cikakken kishin ƙasa, jarumta da jajircewa wajen kare martabar Najeriya a idon duniya.
Onanuga ya bayyana cewa wannan shi ne irin lokacin da ake bukatar hazikan shugabanni su tsaya tare a matsayin murya guda domin kare ikon Najeriya daga duk wata barazana.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


