'An Kashe Mutum 2': Halin da Ake ciki a Garin da Aka Sace Dalibai Mata a Kebbi
- Ana ci gaba da zaman dari-dari a garin Maga da ke karamar hukumar Danko/Wasagu, jihar Kebbi, inda aka sace dalibai mata
- Wasu daga cikin iyayen daliban da aka sace, sun ce ba za su koma gida ba, har sai 'ya'yansu sun dawo garesu cikin aminci
- Amina Hassan, matar Yakubu Makuku, da 'yan bindiga suka kashe a harin, ta fadi yadda maharan suka kashe mutane biyu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kebbi - Iyayen dalibai mata 'yan makarantar kwana ta GCGSS, Maga, karamar hukumar Danko/Wasagu, jihar Kebbi sun bayyana halin da suke ciki bayan sace 'ya'yansu.
Bayan awa 24 da sace dalibai matan, iyayen sun taru a harabar makarantar, cike da zullumi da kuma fatan 'ya'yansu za su dawo gare su cikin aminci.

Source: Twitter
'Ban zan koma gida ba' - Hajiya Rani

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kashe malamin addini, sun sace masu ibada a Kwara
Rahoton jaridar Daily Trust ya ce Hajiya Rani Maga, mahaifiyar wata daliba da aka sace, ta ce ba za ta bar makarantar ba har sai yarinyarta ta dawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hajiya Rani, wacce take ta faman kuka, ta ce har zuwa lokacin ta kasa yarda cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da 'yarta da sauran dalibai
Ta ce:
"Ba zan koma gida ba tare da 'yata ba, ba zan iya cin abinci ba. Kowane sakan daya zuciyata na tunaninta. Ban san a wane hali take ciki ko inda aka kai ta ba, ina cike da fargaba, saboda tana hannun miyagun mutane.
"Na san gwamnati ta dauki mataki kuma an ba mu tabbacin za a kubutar da 'ya'yanmu, amma har sai yaushe? Gwargwadon zamansu a can, gwargwadon tashin hankalinmu."
'Ni dai a dawo mun da 'yata' - Fatima
Hakazalika, wata mahaifiyar daya daga cikin yaran, Fatima Ibrahim, ta ce:
"Ni kawai fata na yarinta ta dawo gareni, ban damu da komai daga nan ba. Don Allah ku dawo mun da yarinyata cikin aminci."
Aminu Usman Lawal, mahaifin Hauwa, daya daga cikin daliban da aka sace, ya ce yana shirin zuwa gona a safiyar Litinin aka sanar da shi abin da ya faru.
Ya ce:
"Na dade ina sake-saken dalilin faruwar hakan a kai na, amma na san Allah zai tsare yarinta da sauran daliban tun da abin nan ya faru, jama'ar yankin ke cikin firgici.
"Ya kamata gwamnati ta taimake mu ta turo mana karin jami'an tsaro ta yadda al'umma za su samu nutsuwa, domin an fara kin zuwa gonaki da kasuwa."

Source: Original
'An kashe mijina da mai gadi' - Amina Hassan
Amina Hassa, wacce mata ce ga shugaban jami'an tsaron makarantar, Yakubu Makuku, wanda aka kashe a harin, ta ce har yanzu tana firgice da kisan mijinta a gabanta, in ji rahoton Channels TV.
Ta ce:
"Wajen karfe 4:00 na Asubar Litinin ne 'yan bindigar suka balle kofar dakinmu, suka shigo wajenmu, muna kwance a gado ni da mijina.
"Suka bukaci ya kai su bangaren da dalibai suke, ya ki amince wa. A gabana suka harbe shi, suka ture ni. Ban san ya aka yi suka karasa dakin kwanan daliban ba."

Kara karanta wannan
Annobar garkuwa da mutane ta sake kunno kai, an kwashe kusan mutum 150 a 'yan kwanaki
Ta kara da cewa 'yan ta'addar, sun kashe wani mai gadin kofar shiga makarantar, Ali Shehu, bayan sun harbe shi lokacin harin.
Tinubu ya tura Shettima zuwa Kebbi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashi game da harin da wasu yan bindiga suka kai a jihar Kebbi.
Tinubu ya umarci mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da ya tafi Kebbi domin jajanta wa gwamnati da iyalan ɗalibai mata da ’yan bindiga suka sace.
Shugaban kasar ya nuna matuƙar bakin ciki game da sace daliban da kisan Birgediya-janar M. Uba, yana mai cewa ya samu cikakken bayani daga hukumomin tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
