Remi Tinubu Ta Fadi Halin Kunci da Ta Shiga bayan Sace Dalibai Mata a Kebbi

Remi Tinubu Ta Fadi Halin Kunci da Ta Shiga bayan Sace Dalibai Mata a Kebbi

  • Matar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana sace dalibai mata 25 a GGCSS Maga a matsayin hari ga darajar ilimi
  • Ta ce Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su tabbatar da ceto daliban cikin gaggawa tare da kamo masu laifi
  • Lamarin ya sake tunzura jama’a kan tashe-tashen hankula da garkuwa da yara da ke barazana a yankin Arewa maso Yamma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A ranar Litinin ne aka yi awon gaba da dalibai mata 25 daga makarantar GGCSS Maga, a karamar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi.

Lamari ya kara jefa al’umma cikin tashin hankali, musamman ganin yadda hare-haren ‘yan bindiga suka ci gaba da karuwa yankunan Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi sauyi a gwamnati, ya ba ɗanuwan marigayi Shehu Shagari muƙami

Matar shugaban kasa, Remi Tinubu
Matar shugaban Najeriya, Remi Tinubu a wani taro. Hoto: @SenRemiTinubu
Source: UGC

A sakon da ta wallafa a X, matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta nuna bakin ciki kan wannan danyen aikin da 'yan ta'adda suka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce shugaban kasa ya ba jami'an tsaro umarnin shugaban ceto daliban cikin lokaci da kuma tabbatar da kama masu hannu a wannan ta’asa domin fuskantar hukunci.

Maganar matar Tinubu kan sace dalibai

A cikin sanarwar ta, Remi Tinubu ta jaddada cewa abin da ya faru a Maga barazana ce ga makarantu, tsaro, ilimi da rayuwar yara.

Ta ce Shugaba Tinubu ya ba da umarni kai tsaye ga hukumomin tsaro su dauki mataki cikin gaggawa domin dawo da daliban cikin koshin lafiya.

Remi Tinubu ta kuma yi addu’ar Allah ya kara wa iyalan wadanda abin ya rutsa da su hakuri, tare da fatan Allah ya jikan mataimakin shugaban makarantar da aka harbe yayin kai harin.

Haka zalika daya daga cikin masu gadin makarantar ya rasu bayan an kai shi asibiti saboda raunin da aka masa yayin harin.

Kara karanta wannan

Majalisa na so Tinubu ya dauki sojoji 100,000 su gwabza da 'yan ta'adda

Hare-hare da aka kai Kebbi a baya

Premium Times ta rahoto cewa jihar Kebbi na daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da matsalar garkuwa da mutane ta yi kamari musamman tun bayan shekarar 2020.

A shekarar 2021 wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Dogo Gide, ya sace dalibai 11 na makarantar gwamnatin tarayya ta Yauri, wadanda daga bisani aka sako su bayan biyan kudin fansa.

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris
Gwamnan jihar Kebbi da aka sace dalibai a jiharsa. Hoto: Nasir Idris
Source: Facebook

Duk da cewa babu wata kungiya da ta dauki alhakin sabon harin Maga, alamu sun nuna cewa lamarin na da nasaba da irin hare-haren kungiyoyin da suka dade suna addabar yankin.

Yayin da wasu daga cikin daliban da aka sace suka kubuta, al'umma sun zuba ido ga gwamnati da jami'an tsaro domin ganin sun ceto daliban cikin koshin lafiya.

An bukaci karin sojoji 100,000 a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa majalisar dattawa ta yi muhawara game da daliban da aka sace a makarantar GGCSS Maga a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Tinubu zai je Afrika ta Kudu taron G20 yayin da matsalar tsaro ta kara kamari

'Yan majalisar dattawa sun yi korafi kan makudan kudin da aka ware domin tsaron makarantu a shekarun baya amma duk da haka ana cigaba a sace dalibai.

A zaman da suka yi, Sanatoci sun yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya kara yawan sojoji har 100,000 domin kara wa rundunar tsaro karfi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng