Bayan Sace Ɗalibai 25 a Kebbi, Abba Ya Dauki Mataki a Makarantun Kano

Bayan Sace Ɗalibai 25 a Kebbi, Abba Ya Dauki Mataki a Makarantun Kano

  • Abba Kabir Yusuf ya amince da daukar masu tsaron makarantu domin aika su zuwa makarantun sakandare daban-daban a jihar Kano
  • Gwamnan ya ce matakin na daga cikin dabarun dawo da tsaro, da kwanciyar hankali a makarantun gwamnati domin inganta ilimi a jihar
  • Ya umarci ma’aikatan tsaron da su yi aiki yadda ya kamata wajen kula da tsaron ɗalibai da makarantu a dukkannin bangarorin Kano

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince tare da kaddamar da rabon takardun aiki ga sababbin ma’aikatan tsaro 1,600.

An dauke su aiki domin aika su ga makarantun sakandare a fadin jihar domin tabbatar da tsaron daliban da ke zuwa karatu.

Kara karanta wannan

Majalisa na so Tinubu ya dauki sojoji 100,000 su gwabza da 'yan ta'adda

Gwamnatin Kano ta dauki masu gadi a makarantu
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya dauki ma'aikatan tsaro a Kano

Sanarwar ta kara da bayyana cewa daukar ma’aikatan tsaron zai taimaka matuka wajen farfaɗo da tsaro da da’a a makarantun gwamnati.

A cewarta, gwamnan Abba Gida Gida ya ce samar da tsaro a makarantu na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ke mayar da hankali a kai.

Ya bayyana cewa ba za a samu ingantaccen ilimi ba har sai an tabbatar da tsaron dalibai da malamansu a duk inda suke karatu a Kano.

Abba ya jaddada cewa ɗalibai, malamai da dukkannin ginin makarantu na bukatar kariya ta musamman, duba da matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar.

Gwamna Abba ya zaburar da jami'an tsaro

Gwamna Abba ya bayyana cewa wadannan ma’aikatan tsaro za su taka muhimmiyar rawa wajen tsare filayen makarantu.

Kara karanta wannan

Gwamna Kefas ya dakatar da shirin shiga jam'iyyar APC, ya fadi dalili

Ya ce an horar da su ne musamman don tabbatar da tsaro da kare duk wata matsala da ka iya kawo cikas ga harkar ilmantarwa.

Gwamnan Kano ya shawarci ma'aikatan da aka dauka
Hoton gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ya yabawa Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Kula da Makarantun Sakandare ta KSSSSMB saboda bin umarnin gwamnati da himmatuwa wajen tabbatar da cewa tsare-tsaren gwamnati kan ilimi.

Gwamnan ya ce sauye-sauyen da ake aiwatarwa a bangaren ilimi na da burin gina makarantun da ke da tsari, tsaro da yanayin da ya dace da koyon zamani.

Abba ya gargade su da cewa an dauke su ne domin kare rayuka da dukiyoyin gwamnati, don haka ya zama wajibi su rike amana.

An sace daliban sakandare a Kebbi

A baya, mun wallafa cewa mazauna masarautar Zuru sun shiga tashin hankali bayan wani mummunan farmaki da ‘yan bindiga suka kai makarantar kwana ta mata a Maga.

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan, dauke da mugayen makamai, sun shiga makarantar cikin daren Lahadi, inda suka yi ta harbe-harbe na tsawon lokaci ba tare da samun cikas ba.

A yayin harin, ‘yan bindigar sun kashe mataimakin shugaban makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, bayan sun ci karo da shi yayin da yake ƙoƙarin hana su daukar yaran.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng