Wasu Dalibai Mata da Aka Sace a Kebbi Sun Kubuta daga Hannun 'Yan Bindiga

Wasu Dalibai Mata da Aka Sace a Kebbi Sun Kubuta daga Hannun 'Yan Bindiga

  • Rahotanni na nuni da cewa wasu dalibai mata daga cikin waɗanda aka sace a Kebbi sun kuɓuta daga hannun 'yan bindiga
  • Rundunar ‘yan sanda ta yi karin haske bayan tabbatar da mutuwar mataimakin shugaban makarantar da wani mutum
  • Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta ba da umarnin gaggawa kan ceto sauran daliban da aka yi garkuwa da su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Dalibai mata biyu daga cikin daliban da aka sace daga GGSS Maga, a jihar Kebbi, sun kuɓuta daga hannun ‘yan bindiga bayan harin da aka kai makarantar a safiyar Litinin.

Lamarin dai ya janyo fargaba da ɗar-ɗar a yankin Danko Wasagu, inda ake ci gaba da neman sauran dalibai da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Kebbi: Abin da ya faru kafin ƴan bindiga su kashe mataimakin shugaban makaranta

Motar makarantar Maga da aka sace dalibai
Motar GGSS Maga da 'yan bindiga suka sace dalibai. Hoto: Amnesty International|Zagazola Makama
Source: Facebook

Rahoton BBC ya yi karin haske kan yadda daliban suka kubuta bayan sace su daga aka yi daga makaranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda wasu daliban makarantar Kebbi suka kubuta

Rahotani sun nuna cewa daliban sun tsere ne lokacin da ‘yan bindigar ke tursasa su shiga cikin dazuzzuka, inda suka yi ta gudu har zuwa gonaki a kusa da yankin.

Hukumomi sun tabbatar da cewa an karɓe su kuma suna karkashin kulawa, duk da cewa ɗaya daga cikinsu ta samu rauni a ƙafarta yayin gudun tsira.

Hussaini Aliyu daga ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ya bayyana cewa daliban da suka kuɓuta sun dawo kuma suna cikin koshin lafiya.

Sai dai ya ce ɗaya daga cikinsu na bukatar kulawar likita saboda raunuka da ta samu yayin tserewa daga hannun 'yan ta'addan.

Harin ya kuma yi sanadin mutuwar mataimakin shugaban makarantar, Hassan Makuku, sannan Ali Shehu, mai gadin makarantar, wanda ya jikkata, ya rasu daga baya a asibiti.

Kara karanta wannan

Gwamna Kefas ya dakatar da shirin shiga jam'iyyar APC, ya fadi dalili

Harin da ya jawo sace daliban makaranta 25

A cewar rahotanni daga yankin, ‘yan bindiga sun kai wa makarantar hari ne a safiyar Litinin inda suka yi awon gaba da dalibai mata 25.

Rahoton The Cable ya tabbatar da cewa bayan tserewar biyun nan, sauran daliban har yanzu suna hannun waɗanda suka sace su.

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris
Gwamnan jihar Kebbi yana addu'a a wani taro. Hoto: Kebbi State Government
Source: Facebook

An ce harin ya sake tada muhawara kan tsaron makarantu da ba da kariya ga ɗalibai a Najeriya, musamman a yankunan Arewa maso Yamma da ke fama da 'yan bindiga.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Kebbi, Bello Muhammad Sani, ya ce an tura ƙarin rundunonin ‘yan sanda masu dabarun musamman tare da sojoji da kungiyoyin fararen hula domin ceto daliban.

Gwamnati ta bada umarnin gaggawa

A wani rahoton, kun ji cewa Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da harin tare da bada umarnin gudanar da aikin ceto cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi ajalin ƙanin kwamishina ana tsaka da zaman makoki

Ya ce shugaban kasar ya nuna cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kare rayuwar ‘yan Najeriya, musamman ɗaliban makarantu.

Ministan ya jaddada cewa gwamnatin Najeriya za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an ceto rayuwar daliban da masu garkuwa suka sace.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng