Tinubu Ya Tura Shettima zuwa Kebbi bayan Sace Dalibai, Ya Tabo Sakacin da Aka Yi
- Shugaba Bola Tinubu ya nuna damuwa game da harin yan bindiga a jihar Kebbi wanda ya yi sanadin sace dalibai
- Tinubu ya umarci mataimakinsa Kashim Shettima da ya ziyarci Kebbi domin jajantawa da kuma tabbatar da ceto ɗaliban
- Bola Tinubu ya bayyana bakin ciki kan kisan sojoji da suka haɗa da Birgediya Janar Musa Uba a Borno
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashi game da harin da wasu yan bindiga suka kai a jihar Kebbi.
Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da ya tafi Jihar Kebbi domin jajanta wa gwamnati da iyalan ɗalibai mata da ’yan bindiga suka sace.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da Babban Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kebbi: Tinubu ya fusata da aka sace dalibai
Shugaban ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya na kan aikin ceto su ba tare da ɓata lokaci ba.
Tinubu ya nuna matuƙar bakin ciki game da sace daliban da kisan birgediya-janar Uba, yana mai cewa ya samu cikakken bayani daga hukumomin tsaro.
Ya ce:
“A matsayina na babban mai kula da tsaron kasa, na ji baƙin cikin mutuwar sojojinmu da jami’anmu yayin aiki.
"Allah ya ba iyalan Brigadier-janar Musa Uba da sauran jaruman da suka rasu haƙuri da juriya.”

Source: Facebook
Tinubu ya damu da sakacin da aka samu
Shugaban kasa ya kuma nuna damuwa game da sace ɗaliban makarantar sakandare a Maga, musamman ganin cewa jami’an tsaro sun samu bayanan leƙen asiri tun kafin harin.
Ya yabawa Gwamna Mohammed Nasir Idris bisa ƙoƙarin da ya yi domin kauce wa wannan hari, duk da cewa ya kira faruwar lamarin “mummunan kuskuren tsaro”.
Tinubu ya bayyana hare-haren a matsayin kutse cikin haƙƙin yara a Najeriya na samun ilimi, inda ya tabbatar da cewa an rigaya an tura jami’an tsaro domin ganin an dawo da ’yan matan cikin koshin lafiya.
Ya yi kira ga al’umma musamman a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro da su ƙara ba da haɗin kai da jami’an tsaro ta hanyar ba su sahihin bayani.
Ya ce:
“Na ji matuƙar takaici ganin ’yan ta’adda marasa tausayi sun lalata karatun waɗannan yara, na umarci hukumomin tsaro da su gaggauta aiki don dawo da ’yan matan.
“Jami’an tsaro ba za su yi nasara ba idan jama’a ba su bayar da haɗin kai da bayanai masu amfani ba.”
Ana sa ran mataimakin shugaban kasa Shettima zai gana da jami’an gwamnati, kwamandojin tsaro, sarakunan gargajiya, iyayen yara da al’ummomin da abin ya shafa.
Gwamnan Kebbi ya sha alwashin ceto dalibai
A wani labarin, Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kai ziyarar gani da ido zuwa makarantar da aka sace dalibai domin ganewa idonsa halin da ake ciki.
Nasir Idris wanda ya gana da iyayen yaran da aka sace, ya ba su tabbacin cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin 'ya'yansu sun kubuta.
Hakan ya biyo bayan harin 'yan bindiga da suka yi awon gaba da wasu dalibai mata na wata makarantar sakandire a jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


